Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Gasar Faretin Makarantun Islamiyya na Kaduna

Madrasatu ta Da'irar Mafara ta kayatar

Daga Tanimu Yahaya

A ranar Lahadi 13/1/2013 ne aka gabatar da gasar faretin daliban Fudiyyoyin yankin Da'irar Mafara da ke jihar Zamfara. Gasar dai ta samu halarta akalla makarantu goma sha biyu daga ciki da wajen Da'irar.

A jawabinsa a wurin taron, Wakilin 'yan uwa na Mafara, Malam Abubakar Nuhu ya ce, "wanan gasar faretin takenta shi ne, Faretin girmamawa ga Manzon Allah Muhamad (S), saboda murnar zagayowar watan da aka haife shi. Don haka muna jinjina wa dukkan daliban da suka samu halartar wannan gasar".

An dai fara gasar ne da bude taro da addu'a, sannan karatun Alkur'ani mai girma. Da aka shigo filin gasar, Madarasatu Fudiyya Mafara ce ta bude da faretin share fage, inda bayan ta kammala aka ci gaba da gabatar da sauran makaratun. Tabbas duk makarantar da ta taka, sai 'yan kallo sun jinjina mata. Haka dai aka ci gaba da gasar har zuwa karshe. A karshen gasar an fitar da zakaru daga na daya zuwa na uku.

Madarasatu Fudiyya Madaci ne ta zo ta uku, yayin da Madarasatul Fudiyya Gora ta zo ta biyu. A karshe kuma Madarasatul Fudiyya Maradun ta zo ta daya. Malam Adamu Sani, daya daga cikin Alkalan gasar ya bayana cewa,"dama kamar yadda muka saba, duk shekara muna shirya wannan gasar idan watan Mauludi ya kusa kamawa don tarbon watan, sai dai wani lokaci sai ma watan ya kama ne muke gabatar da gasar. Inda mu fatanmu ya kasance dalibai sun yi kumaji da kara dagewa da himmatuwa a kan wannan harka".

Malam Sanusi, daya daga cikin Malaman makarantar Fudiyya Mafara ya bayyana yadda gasar take, "to dama dai ita wannan gasar akan gayyaci dukkan makarantun Islamiyyoyi da Fudiyyoyin yankin Da'irar Mafara, ba wai sai Fudiyyoyi kawai ba. Shi ne ma dalilin da ya sa ka ga akwai makarantun Islamiyyoyi a nan".

Shi kuma wani dan kallo mai su Surajo cewa ya yi, "mu kam wallahi wannan gasar ta kayatar da mu, musamman irin yadda daliban kan yi faraiti, kai ka ce sojoji ne. Haka ma wani da ya bukaci a sakaya sunansa ya ce,"a hakikanin gaskiya wadannan yara da kake gani, ba za a samu kwatankwacin su ba a duk fadin makarantun da ke kasar nan. Ni da ma shi ne dalilin da ya sa zan cire dana daga makarantar gwamnati zan saka shi a daya daga cikin wadannan makarantu".

A karshe dai an ba da kyautuka ga wadanda suka sami nasara, kuma an fara taron lafiya, an kare lafiya.


Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan