Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Gasar Faretin Makarantun Islamiyya na Kaduna

Madrasatu Ahlul Baiti ta yi zarra

Ranar Asabar da ta gabata ne aka gudanar da bikin gasar faretin na makarantun Islamiyya da ke Kaduna karkashin Lajna Fudiyya don murna da zagayowar watan haihuwar Fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (S), inda kuma Madarasatu Ahlul Baiti ta yi zarra a cikin kason da aka gudanar da gasar a kai.

Wakilinmu da ya shaidi wannan biki, kuma ya shaida mana cewa akwai abubuwa guda uku da aka lura da su a lokacin gudanar da wannan gasa, kamar yadda Shugaban Alkalan, Malam Shu'áibu Malumfashi ya bayyana wa taron. Ya ce an kasa gasar ne kashi uku, Fareti, Tsafta da kuma Wake.

A wadannan rukunai, Madrasatu Ahlul Baiti ta zo ta daya a wake, ta kuma zo ta daya a Tsafta, sannan kuma ta zo ta biyu a fareti. Daga nan kuma sai madrasatu Ikamatud Dinul Islam ke bi mata, inda ta zo ta biyu a tsafta, sannan ta zo ta uku a fareti da wake. Sannan Fudiyya Badiko, kamar sauran shekaru ta zo ta daya a Fareti, ta kuma zo ta uku a tsafta. Madrasatu Muhammad Suraj Bn Sulaiman kuma ta zo ta biyu a wake.

Makarantu da dama ne suka shiga wannan gasa, wadanda suka hada da madrasatu Hubbu Rasul da ke Kurmin Mashi, Madrasatu Aliyu Ibn Umar da ke Dirkaniya, Madrasatu Shafa'atul Dinul Islam da ke Rigasa da dai sauransu.

Cikin jawabin da ya gabatar jim kadan bayan kammala wannan gasa, Wakilin 'yan uwa na Kaduna, Malam Muhammad Mukhtar Sahabi ya bayyana cewa wannan gasar fareti da aka yi, yana daya daga cikin bukukuwan Maulidin Manzon Allah (S).

Ya ci gaba da cewa gayyato makarantu da ake yi don shiga wannan taro domin su hadu da na Fudiyya, an yi ne don kara samun dankon zumunci da hadin kai tsakanin juna. Ya ce wannan ba karamar hanya ba ce da za ta kawo hadin hadin kai tsakaninn al'úmmar musulmi.

Daga nan sai ya yi albishir ga duk makarantun da suka samu shiga wannan gasa da cewa kowa ya ci, ko makaranta ta samu kyauta ko ba ta samu ba, ko ta zo ta daya ko ba zo ba, to duk dai an ci. Domin a cewarsa, duk an yi wannan abu ne domin Manzon Allah (S).

Bayan kammalawa ne kuma aka miki takardun shaida ga duk makarantun da suka shiga wannan gasa, sannan aka bayar da kyauta ga wadanda suka sami nasara daga na daya zuwa na uku daga kowane rukuni.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan