Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da motoci ga jami'án tsaro

A kwanakin baya ne gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ta raba wasu motoci 40 ga jami'án tsaro na Operation Yaki domin ci gaba da da gudanar da ayyukansu na samar da tsaro a duk fadin jihar.

Cikin jawabin da ya gabatar, Gwamna Mukhtar Ramalan Yero ya soma ne da mika godiyarsa ga jami'an tsaron bisa irin namijin kokarin da suke yi don ganin al'úmmar jihar Kaduna sun samu tsaro a harkokinsu.

Gwamnan ya ci gaba da cewa bisa irin wannan kokari nasu ne ya sa gwamnatinsa ta ga cewa ya kamata ta taimaka masu da duk abin da za ta iya don kara masu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu.

Ya ce taron da ake yi a yau, shi ne na mika wadannan motoci ga Operation Yaki, domin maye gurbinsu da tsofaffin, wanda su kuma ya ce za a gyara su a bayar ga ofisoshin 'yan sandan da ke fadin jihar, wadanda kuma yawancinsu ba su da motoci.

Saboda haka sai Gwamnan ya nemi wadannan jami'án tsaro da su kula da wadannan motoci tamkar nasu, domin ta hanyar haka ne za a dade ana amfani da motocin ba tare da sun lalace ba.

Tun farko cikin nasa jawabin, jagoran hukumar Operation Yaki, Kanar Dangana Mamman, ya nuna maktukar godiyarsa ga Gwamnatin ne bisa irin hadin kan da suke ba su a duk lokacin da suka nemi hakan.

Daga nan ya tabbatar wa da gwamnatin cewa za su kula da wadannan motoci. Sannan kuma ya yi karin haske da cewa a wadannan motoci da aka bayar a ranar, kowace mota tana dauke da cikakkun kayan sadarwa, ta yadda kowace mota, kuma ko daga ina ne za ta iya tuntubar hedikwatar rundunar da ke Kaduna.

Kanar Dangana ya ci gaba da cewa, kuma dukkan motocin, an sanya musu alama ta yadda da zarar mutum ya gan ta zai iya gane jami'an tsaron da ke ciki, wato ko dai 'yan sanda ne, ko sojojin sama, ko na kasa, ko kuma 'yan sintiri. Ya ce sun yi haka ne domin jama'á su sami saukin gane ko wadanne irin jami'an tsaro suka zo masu.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan