Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           A bara ne aka fi kashe 'yan jarida a duniya

Cibiyar 'yan jarida ta duniya da ke da cibiya a birnin Vienna ta fitar da rahoto a ranar Litinin dangane da yawan 'yan jaridar da aka kashe a shekarar 2012 da ta gabata.

Cibiyar ta bayyana shekarar 2012 da cewa ita ce mafi muni wajen kashe 'yan jarida tun daga kafuwarta a 1997. Shekara mafi muni ta kashe 'yan jarida da cibiyar ta fara tattara bayanai a kanta ita ce ta 2009 da aka kashe 'yan jarida 110, daga cikin akwai 32 a lokacin guda a kasar Philliphines.

A cikin shekarar 2011 kuwa an kashe 'yan jarida 102 a kasashe daban-daban a lokacin da suke gudanar da ayyukansu. A shekarar 2012 da ta zo karshe, an kashe 'yan jarida da adadinsu ya kai 132.

Shugaban cibiyar Elison Macenzy ya bayyana kasashen da suka fi zama hatsari ga 'yan jarida da suka hada "Pakistan da Somaliya da Philliphines da Honduras da Mexico da Brazil."

A cikin kasar Siriya kadai an kashe 'yan jarida 31 yayin da a kasar Somaliya aka kashe 'yan jarida 16. A kasar Pakistan an kashe 'yan jarida biyar sai Columbia da Hundoras 'yan jarida biyar-biyar. A cikin kasar Mexico kuwa adadin 'yan jaridar da aka kashe a shekarar da ta gabata sun kai bakwai.

A bisa rahoton na cibiyar 'yan jarida, an daure 'yan jaridu 70 a cikin kasar Turkiyya a 2012 wanda shi ne mafi muni.

A Nijeriya ma a ranar Asabar 12 ga Junairun nan, Editan mujallar Anambara News da ake bugawa wata-wata mai suna Ikechukwu Udendu ya zama dan jarida na bakwai da aka kashe a duk fadin duniyar nan a wannan sabuwar shekara ta 2013.

A yayin da yake yin tir da kisan, Gabriel Baglo, Daraktan kungiyar 'yan jarida da ake kira IFJ, a takaice ya ce, "Najeriya ta soma zama kasar da ake kai wa 'yan jarida hari da ma kashe su ba gaira ba sabat. A gaskiya wannan koma baya ne ga 'yancin 'yan jarida."

Muhammad Garba, Shugaban kungiyar 'yan jarida ta kasa, ya ce, "yanzu dai 'yan jarida suna zaune ne cikin zullumin ko dai jami'an tsaro su kama su su tsare, ko kuma wasu da ba a san ko su waye ba su kai musu harin kisa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba."
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan