Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Manzon Allah Rahamatan lil Alamina ne

Mai karatu wannan shi ne wani bangare na jawabin Sayyid Zakzaky (H) a ranar rufe muzaharar maulud ta ran 19 ga Rabi'ul Awwal 1432. Matsalolin da muke samu ne a sashen Kwamfutarmu suka hana mu kawo muku daya daga cikin jawaban Maulud da Sayyid din ya halarta a cikin Zariya da kewaye. Amma insha Allah a mako mai zuwa za a ji sabon bayani. Wannan din ma in ka karanta za ka ji kamar yau aka yi shi saboda fa'idojin da ke ciki.

IN ZA KA YI GYARA, TO KA BI SUNNAR ANNABI

Na'am an kore shi, na'am an yi masa a-ture, na'am an yi masa wulakanci, an yi masa jina-jina, amma mene addu'arsa, addu'a mai tsawo? Cikin jumlar abin da Manzon Allah yake cewa "Ya Rabbi ina kawo maka kukan kaskantuwata da kaskancin matsayina (wadannan mutane ba su san darajata ba)." A cikin addu'arsa yake cewa, "ga wa za ka wakilta ni, ga makiyin da ka mallaka masa al'amarina, wanda bai san darajata ba.." Sannan karshe Manzon Allah ya ce, "in dai ba ka yi fushi da ni ba, to ban damu ba." Duk halin da na shiga in dai ba kai ne ka yi fushi da ni ba, to shi kenan. Don mutane su yi fushi da ni, wannan na yarda. Wannan addu'ar Manzo kenan. Ba addu'a ya yi a kan mutanen nan ba, bai kuma yarda aka halaka su ba. Kuma cikin ikon Allah, sai aka samu daga cikin wadanda suka zo suna masa eho da a-ture din nan, wasu sun yi imani da "La ilaha illallah Muhammadur Rasulullah," sun kyautata Musuluncinsu.

To, kuma Manzon Allah ya zauna da mutane iri-iri. Ya zauna da mutanen da ya san zukatansu, amma ya yi mu'amala da su da zahirinsu. Bai yi mu'amala da su da abin da ya sani wanda suka boye ba, duk da Allah ya yi masa iddila'i a kai. Allah ma ya sanar da shi wani abin da za su yi a bayan ransa, amma bai yi mu'amala da su a kan ya san nan gaba za su yi kaza ba. Sai ya yi mu'amala da su da zahiri. Wannan Manzon Rahama kenan. In ka ce addininsa kake bi, to yaya zai zama kai ka dauki wata hanya ta daban?

Wani ka ga yana da nau'i na fandara, mene ya kamata ka yi? Ai gyara za ka yi ko? Gyaran nan yaya za ka yi? Sunnar Manzon Allah za ka bi, ba jafa'i da tsinuwa ba, ballantana kuma har da dauko makami da ta da bama-bamai da harbe-harbe. Ba da shi Annabi ya kawo gyara ba. Wadanda suka kori Annabi bayan sun cutar da shi a Makka, shekara 13 suna cutar da shi, suka kore shi, suka bi shi da yaki, bayan sun yi shelar a kawo shi da rai ko ba rai, Allah ya tsamar da shi ya kai shi Madina, suka bi shi da yaki, suka bi shi da Badar, Allah ya taimake shi. Suka bi shi da Uhud da nufin su gama da shi, Allah ya taimake shi. Suka bi shi da Khandak, amma da Allah ya ba wannan Manzo nasara ya bude Makka.

Yayin da wadannan mutane suka zo, sun dauka zai fille musu wuya ne, don dama ka'idar kenan, zaunannen abu ne cewa idan kuka yaki mutane kuka yi nasara a kansu, to sai yadda kuka so yi da su. Sun zama bayinku ko kuma ku fille wanda kuka ga damar fille masa wuya, ku bautar da wadanda kuka ga damar bautarwa. Wannan ita ce ka'idar da aka sani a da, kuma haka suke tsammanin za a yi musu. Amma Manzon Allah (SAWA) ya ce, "me kuke tsammanin zan yi da ku?" Sun sunkuyar da kawukansu, sun bar hannuwansu a keyoyinsu, suna tsammanin fillan wuya ne, suka sunkuyar da kai suka yi shiru. "Me kuke tsammanin zan yi da ku?" Wasu suka yi dan karfin hali suka ce, "to ai kai dan zumunci ne." Sai Manzo ya ce, "ku tafi, ku sakakku ne (an sake ku)!"

Wannan ya sa wasu suka ce lalle wannan mutumin ba domin duniya yake abinsa ba, ba domin kansa yake abin nan ba, yana yi don Allah ne. Wasu wannan ya sa suka shiga Musulunci, wasu kuma suka kyautata Musuluncinsu.

To, in har a wannan al'umma a yau muka ga fandara, to hanyar gyara ita ce hanyar da Manzon Allah ya bi. In har a wannan al'umma muka ga lalacewa, hanyar gyara ita ce hanyar da wannan Manzo ya bi. In har wannan al'umma ta koma ba ta da martaba, ba ta da izza, ta sami kaskanci da wulakanci, hanyar Manzon Allah ne zai dawo mata da martabarta.

DABARAR RABA-KA-MALLAKA AKE WA MUSULMI

Amma ra'ayin mutane na cewa su gutsuttsura addini, kowanne ya dauki wani bangare, "kullu hizbin bi ma ladaihim farihun," wannan ba zai kai mu ko'ina ba. Wannan ajandar makiya ne. Wanda har makiyanmu sun gano su hada mu fada, mu yi musu fadan, su su huta. Idan kana fada da wadansu abokan gaba a bangare guda, ku ga ku a nan, abokan gabanku ga su a daya bangaren. Sai abokan gabanku suka koma suna fada da juna; yaya ku a gare ku? Ai tsaf, kun huta. Ka ga maimakon su hada karfi su yi fada da ku, su fi karfinku, Allah ya hada su fada, ya hutasshe ku fadan, sai su mangare kansu, ku kuma sai ku dira a kansu.

Wannan dabara da ake kira raba-ka-mallaka (Divide and rule), shi Bature ya zo da shi kasar musulmi. Ko'ina ya je sai ya yi nazari na abin da ke tsakanin mutane, ya jefa rarraba. Kafin nan ma sai da ya sa musamman a yi masa nazarin musulmi, a gano masa nukudodin karfinsu da nukudodin rauninsu, don ya yi amfani da wadannan ya raba su. To, ya iya yin wannan. A haka nan ya mamayi duniya. Wannan al'umma, wadda da ita ke da izza, ta mamayi duniya, ta koyar da duniya komai, sai ta dawo, Bature wadda ta koya masa karatu, shi ya zo ya salladu a kanta. Kuma ya bar ta da rigimar raba-ka-mallaka. Ya bar ta da rigingimun akidodi, ya bar mu da rigingimu a hukunce-hukunce. Ya bar mu muna ta faman tattaunawa.

Wani Mai hikima da Larabci yake cewa ana rigimar me za a yi wa kafa a alwala, wankewa za a yi ko za a shafa ne? To, da aka tsaya ana wannan rigima, sai aka wayi gari ba mu da 'maudu'il kadam'. Muna neman me za mu yi wa 'kadam' dinmu, za mu wanke ne ko za mu shafa ne? Wannan ya ce shafa za a yi, wancan ya ce wankewa za a yi. Wallahi in ka wanke sai mu yi rigima. In ka shafa ba zan bi ka salla ba. To, ana cikin haka nan sai muka wayi gari ba mu da 'maudu'il kadam' din. Su sun riga sun mallake kasar, sun bar mu da rigima.

Ahkam ba muhallin rigima bane. Na'am ga hujjar wannan, ga hujjar wancan. Abu ne na hujja, da me muka dogara? Addinin nan ya zo mana ne daga Manzon Allah. Daga ina aka samu wannan ruwayar? A tantance su gaba daya mana, duk a zube su mana. Sai aka sa mana katangu na karfe wadanda babu su. Ba katangar karfe wadda ake gani ba. Yanzu in aka sa katangar karfe aka raba mutane biyu, ina na nan za su iya zuwa can bangaren? Ai ba za su iya ba ko? Saboda ba za su iya busa katangar karfe ba ko? Sai ya zama ba katangar, amma an sa ta, an sawwala ta a kwakwalwa. Muna ganin akwai katanga din, har ma ba ma iya zuwa daya bangaren, sai dai a kawo mana labarin daya bangaren. Wai ba su yarda da kaza ba, ko su suna yin kaza ne, sannan sai mu tashi a wa'azozinmu mu yi ta jafa'i a kan sauran. Wadancan ai fandararru ne, wadannan ba su gane ba, suna da kaza, kaza. Wannan ba shi ne alheri ba.

Ana nan, ana nan sai aka wayi gari sun sa shamakai da babu su zahiran, hissiyyan, amma kuma sun shiga kwakwalenmu sun raba. Sai ya zama karfinsu ya fi katangar zahiri. Domin katangar zahiri kana iya balle shi, amma ka ga katangar kwakwalwa in ya sami zama a kwakwalwa, to yaye shi yana da wahala. Ta haka nan sai al'ummar musulmi suka zama dan kaza da dan kaza. Su kuwa Turawa suka samu salladuwa a kan wannan al'umma. Ya zama duniyar nan a yau tana tinkaho da dukiyar da ke kasar musulmi ne, amma musulmi matalauta ne. An raba su zuwa ga dauloli wajen 55, kowacce tana tinkaho da daularta, ita daban take.

TARONMU ALAMI NE NA DAGOWAR ADDININ NAN

Abin da Allah ya so, ba abin da suka so ba. Allah yanzu ya ga daman addini ya rayu, ya ga daman a gano sakon da Annabinsa ya zo da shi. Ya ga daman mutane su gane sahihi, su bar hululu wanda makiya suka kawo musu. Wannan taro namu daya ne daga cikin alamomin wannan na abin da Allah ya so.

Wannan taro namu, mun taru ne a kan son Manzon Allah (SAWA). A nan kun ga 'yan uwa sun zo sun yi mana wani dan 'show', wanda yake alami ne kawai, an dai kamanta ne. Na ji ana ba wasu hakuri cewa an shirya su ma za su zagaya, su yi hakuri sai wata shekarar. Mun ga Ibo da Yoroba da Fulani, wannan ta janibin kabilu kenan. Mun kuma ga ra'ayoyi daban-daban. Mun ga Salafiyya. A wannan muhalli bara waccan nake cewa na ga 'yan Salafiyya sun wuce da yawan gaske, muka ce ba mu da mishkila dangane da magogi ko gajeren wando. In dai har ka ce Salafus salih za ka bi, wallahi ba mu da matsala da kai. Domin kuwa lallai bin Salafus salih mafita ne. Amma a kawo littattafan Salafus salih din a gani. Me ke cikin littattafan Salafus salih din? Salafus salih a kan me suka rayu? Salafus salih ba su kafirta juna ba, ba su yaki juna ba.

Salafus salih in ka dauko littattafansu ka duba na Ahlus Sunna Wal Jama'a, abu biyu za ka gani. Sai dai ya zama ba ka so. Za ka ga darikun sufaye, za ka kuma ga mazhabobin nan guda hudu, intaha. Saboda haka in Salafus salih ne ba mu da wata matsala. Amma mun san akwai jama'a wadanda mun san makiyanmu suka kirkiro, suka sa mata wannan sunan, suka dauki wannan sunan suka kakaba wa kansu. Suka kira kansu Salafiyya da kuma Ahlus Sunna Wal jama'a, alhali tsakaninsu da Salafus salih sun yi masu bara'a, kuma sun yi wa Ahlus Sunna Wal Jama'a bara'a, amma sun fake da sunan Salafiyya da Ahlus Sunna wal jama'a suna farraka tsakanin musulmi. Saboda haka in da gaske ne Ahlus Sunna Wal Jama'a kake da bukata, sai mu ce masha Allah. Da gaske ne Salafus salih kake bi? Masha Allah. A dauko koyarwar Ahlus Sunna Wal jama'a, a dauko koyarwar Salafus salih. Ba mu da rigima da kai. Amma a ajiye abin da makiyanmu suka kawo suka kawo suka cusa a cikinmu; wannan ba zai amfane mu ba.

Kamar yadda nake cewa mun ga masu ra'ayin Salafiyya, to har 'yan Gayu ma mun gani, da 'yan tauri. Wani lokaci a nan wurin, don bara ba mu iya yi a wannan kewayen ba saboda inda muka yi taron ya dan takura, cewa akwai mu ma da 'yan tauri, kuma taurin na gaske ne ba na 'show' bane. Har ma su 'yan tauri suna rigima, akwai Kurawa da Yadakwarawa, amma in sun fahimci addini, za su gane cewa ba rigima a kan wannan. Saboda haka ma ne wasu masu yi mana barazana da 'yan tauri, za su gayyato 'yan tauri su kawo mana hari, to ai da aka yi maulidin bara da bara waccan, ba karamin darga muka yi ba da 'yan taurin da suka ce za su dauki fansa. Muka ce a'a ba haka ake yi ba. Sunnar Annabi za a bi. Ba ramuwar gayya za a yi ba. In su sun kawo hari sun yi kisan kai, mu ba ramawa za mu yi mu kai musu hari ba. Amma aikinku shi ne in sun kawo harin, to ku ku kare, ba a kai hari ba, a kare kai.

Akwai wani Gwamna mai ci yanzu, tunda Gwamna ba sai ka ci zabe ba, haka nan za a dauko ka a maka ka a ce wai ka ci zabe, akwai Gwamna wanda ya taba yin abin kunya a kauyensu lokacin yana saurayi, ba zan fadi abin kunyar da ya yi ba, yanzu yana yayin biyan 'yan tauri su kai wa 'yan uwa hari. Har ma kwanakin baya ya biya wadansu a wata unguwa a Kaduna, ya ba su kudi miliyan 30 su gyara masallacinsu, ya ce kuma su kori Shi'a daga masallacin. Suka yi ta bambami, suka yi ta bambami, suka gayyato mutane suka yi sare-sare.

Da yake su ba su gane wa za su sara ba, an gayyato su ne su yi sara, sai ya zama duk wanda suka gani da doguwar riga sai su sare shi, sai suka sari wadanda suka gayyato su. Na'am sun ji wa 'yan uwa da dama ciwo, amma sun kashe mutum daya daga cikin mutanen da suka gayyato su. Nake cewa, to wannan dabbanci ne. Idan da da gaske ne addini kake so, ai hujja ne, ba sara da suka ba. Hankali za a sa ba hauka ba. Amma mun san ba su da hankalin, haukar kawai za su sa.

To, na sha fadin wannan maganar maganin haukar mahaukaci, haukar mai hankali. Idan mutum ya ce zai sa hauka ne, kar ya dauka zai ci riba ne, mu ma za mu sa hankali mu yi maganin haukan mahaukaci!

To, kuma mun ga janibobi daban-daban, har da 'yan kwallo, kar su ce ban ambace su ba. Da wasu bangarori daban-daban wadanda ba su shigo ba, har da Buzaye da 'yar butarsu ta shayi. Wannan wata alama ce ta haduwar al'umma duk da kuma bambance-bambancensu ta fuskacin kabilu, wanda a wurinmu halittar Allah ne.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan