AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Rahoto

HANTSI: Shahidi, Gwarzon Dan Jarida: Ibrahim Usman

Daga Danjuma Katsina


 Shema Ibrahim

Na dau lokaci ina son fitar da rubutu a kan Shahid Alhaji Ibrahim Usman, amma bisa wasu dalilai masu karfi sai in dakata. Mafi yawa abin da zan kawo a wannan rubutun yana cikin wani littafi da muka dade muna tattarawa da Ibrahim Usman.

Labarai ne wadanda wasu ba wanda ya taba jin su, kila kuma shi ya taba bayyana wa wadansu ba tare da sani na ba. Wasu bayanan sirri ne, sai yanzu na fito da su. Wanda a da mun yi niyyar ba za mu taba bayyana wasu daga cikin su ba a tsakanin mu.

A bayanan da zan kawo, wani lokaci zan rika bayyana sunaye. Duk inda na fadi sunan wani, sai da na samu amincewa daga wanda zan fadi sunan nasa, musamman idan wanda zan fadi sunan nasa ba dan Harka Islamiyya ba ne. Wasu bayanan zan bar su a kunshe, sai dai wata rana, ko kuma wani lokaci in yanayin da za a fade su ya kama. Wani yanayi nake ciki, wanda mutum biyu suke wani rubutu a kan daya ba zai fitar da bayanin ba sai da iznin daya. Dayan Allah ya yi masa baiwa da shahada, daya dole ya yi taka-tsantsan.

WAKI’AR ZARIYA ZAMANIN ABACHA 1996

Ina Katsina aka yi waki’ar Zariya, wanda aka bude wuta a kofar Doka lokacin Abacha. Lokacin iyalina suna zaune a Zariya, yayin da ni kuma nakan yawan zuwa Katsina, saboda nakan samo wa ALMIZAN talla. Labarin ya watsu kamar wutar daji, da maraice na hawo mota zuwa Zariya, da kyar na samu motar Mararrbar Kankara. Daga can na samu ta Funtuwa. Daga Funtuwa sai Zariya. Na iso Zariya tsakar dare na nufi gidana.

Duk abin da ya rika biyo baya ina Zariya, wasu gida na aka tare ana shirya su. Wannan ya sanya ’yan sanda daga baya suka matsa wa gidan da kai farmaki ba kakkautawa, kodayake kafin abu ya ta’azzara na sanya iyalina a mota na mai da su gida a Katsina, aka bar ni ni daya a gidan, sai wadanda sukan zo waje na.

A Zariya na lura matsalar babba ce, kuma tana da tsawo, na yanke shawarar garin Kano zan tare a matsayin inda zan yi gudun hijira. Na lissafa na ga Kano tana kusa da Katsina, da kuma Zariya da Kaduna. Kano babban gari ne kana iya wasan boyo da jami’an tsaro, kuma yana da wahalar gaske Abacha ya kuskura ya kawo yamutsi a Kano. Kuma a Kano ina da aminai masu kauna ta sosai tsakani da Allah. Kuma babbar cibiya ce ta kasuwa da makaranta ALMIZAN.

Na je Katsina na iske lokacin an yamutsa garin ana ta kama duk wani fitaccen dan uwan da aka sani. An je gidanmu wajen Mahaifina an tsorata shi. Gidana kuma ana ta zuwa har ta kai zuwan karshe a gidan, suna tsammanin ina ciki, suka kewaye shi da rana. Da ba su same ni ba, sai suka tafi da matata Rukayya Danladi da ’ya’yana Muhammad Sani yana goye, sai Hadiza ita kuma tana karama.

A wannan ranar na bar Katsina zuwa Kano, inda na fara sauka gidan Alhaji Hasan Baffa. Daga baya Yahaya Alhasan Kunya ya ba ni wajen da na zaune har waki’ar ta kwaranye bayan shekaru a cikin ta.

Kano ta taka rawar gaske wajen tabbatuwar ALMIZAN da dorewar ta a wannan yanayi mai tsanani, kuma jagororinta irin su Hasan Baffa, Umar Chiroma da Malam Ibrahim Musa sun taka rawar da ta kamata a yi rubutu a kai domin na baya su dau darussan da ke ciki.

Daga Kano muka rika tafiyar da duk harkokin gudanarwa na ALMIZAN. Ofis kuma gidan su Hasan Baffa. Ni a lokacin na samu damar yin rubuce-rubuce masu yawan gaske. Lokacin na samu yin nazari, wanda kullum ina dakin karatu na British Council. A nan ne na samu alaka da Rediyo Kudirat, wadanda suka rika caccakar gwamnatin Abacha, har suka ga bayan ta.

SHARI’AR MALAM ZAKZAKY A KADUNA

Duk lokacin da za a yi shara’ar Malam a Kaduna nakan baro Kano in zo Kaduna. Masaukin da nake sauka shi ne dakin Muhammad Sabo, wanda daga baya ya rika rubutu da sunan Mahfuz Mundadu. Na rika zama dangata a dakinsa duk lokacin da nake Kaduna. Wajen da muke haduwa da Edita da Umar Ciroma domin aikin ALMIZAN shi ne ofishin Dakta Shu’aibu Musa da ke wani Asibitin da yake aiki, kuma a nan na fara ganin sa. Daga nan nake shiga garin Kaduna domin tsara ya zan samu bayanin kai Malam kotu da abin da ya faru a kotun. Ba wanda ya san ya nake samun labarina, kuma babu mai tambaya ta zan fita, zan kuma in dawo da labarina, kuma ba a da shakkun me na kawo za a buga shi.

Yadda nakan yi a lokacin, na rika amfani da wasu ’yan jarida ne wadanda suke da cikakkiyar rijista da wata babbar jarida, kuma aikinsu dauko labaran da ke faruwa a kotu, sai in roke su, su za su je har cikin kotun. Shi ya sa a lokacin hatta irin kayan da Malam ya sanya na kan fada da yadda ya tsaya.

Wani lokaci kuma ’yan jaridar in sun ga ba a bincike sosai, sai su zo su sanya ni tsakiya mu shiga kotun tare, ba tare da an gane ni ba, sai a dauka dan jarida ne kawai. Idan ba a shiga da ni kotu ba, to zan tabbatar idan mutum daya ya ba ni labari, sai na kara tabbatar da shi daga wajen wasu kafin in rubuta shi.

A lokacin zan rubuta wa ALMIZAN, zan kuma shaida wa gidan rediyon Kudirat. Wannan ya sa a lokacin duk abin da ya samu ’yan uwa, rediyo Kudirat tana kawo shi garau. Wasu ’yan jaridan da suka rika taimaka mani suna aiki da gidan jaridun RANA da HOTLINE ta Sani Kontagora. Wasu na aiki da jaridar TODAY ta Marigayi Abidina Kumasi. Wasu a jaridar Kamfanin NEW NIGERIA, sai daya daga wata jaridar Kudu.

Dahiru Ibrahim Masariyya, muna kiran sa da wannan sunan saboda ya fara buga wata Mujalla mai suna MASARIYYA, wanda a lokacin ke aiki a jaridar A YAU da kuma TODAY. Yana cikin wadanda suka fi taimaka wa akwai wani Wakilin daga Jaridar Kudu. Wasu ba zan fadi sunayensu ba, saboda ban samu amincewaarsu ba. Wani lokaci in na samu damar yin wani rubutun na kawo.

A lokacin ofishin Malam Ibrahim Sheme nan ne wajen yada zangona, daga nan nake tafiyar da duk ayyukana na tattara bayanai. Ibrahim Sheme lokacin shi ne mataimakin Editan jaridar NEW NIGERIA da ke fitowa duk ranar Asabar, lokacin Mahmood Jega, babban Edita a jaridun DAILY TRUST a yanzu, yana Editan Saturday New Nigeria. Garba Dangida yana jami’in kasuwanci na kamfanin. Sai Nasiru Abdul, Shugaban gidan rediyon ABU FM a yanzu, shi ma yana cikin Editocin kamfanin. Don haka idan ina NEW NIGERIA ina da cikakkiyar kula da kuma tsaro. Daga nan kuma ina iya sanin duk abin da ke faruwa a kasar nan. A nan muke haduwa da ’yan jaridan da suka je kotu su bayyana mani me ya faru in rubuta, in kai wa Edita, Malam Ibrahim Musa.

Wata rana na raka Malam Ibrahim Sheme wajen wani mitin da aka kira shi, wanda ake son kafa jaridun WEEKLY TRUST. Mun je wajen muka dade suna ciki suna mitin ni kuma ina falo. An ce su hudu ne, Sheme, Kabiru Yusuf, Ishaq Ajibola, da wani. Muna dawowa sai Alhaji Garba Dangida ya shaida mani cewa wani ma’aikacin gidan rediyon Jihar Kaduna mai suna Ibrahim ya zo nema na. A ranar ba mu hadu ba, washegari na tafi Post Office aika wa rediyon Kudirat wani sako, ina zuwa sai na same shi a ofis din Sheme yana jira na. Ban san shi ba, bai san ni ba a fuska, amma yana ganin sunana da rubutu a jaridu, muka rungume juna. Ya gabatar da kansa a waje na. Wannan ita ce haduwarmu ta farko da shi.

Ganin na farko ya zauna mani a rai, na natsu da shi, na kuma yarda da shi, duk da ina da hali da tsarin ba na saurin yarda da mutane, har sai na samu tabbaci daban-daban. A ranar muka wuce gidansa na ci abincin dare, kuma a ranar na bayyana masa duk tsare-tsarena da yadda nake samun bayanai na kotu.

A ranar muka sake tsarin yadda za mu kara inganta bayanan da yadda yanzu shi da kansa zai rika zuwa kotun, da yadda za mu rika tabbatarwa cewa yanzu kowane zuwa kotu ba wai kawai ALMIZAN za ta yi amfani da rahoton ba, za mu rika ba wasu jaridun. A ranar muka tsara duk wani shirinmu zai zama a cikin sirri. Muka mai da kanmu wata runduna ta mutum biyu wadanda za su rika aiki daidai bukatar Harka da cigabanta. A kuma tsari irin namu a lokacin, muka ce Hadisi ya ce in mutane biyu za su yi tafiya su zabi Shugaba, na ce shi ne Shugaban tun da a shekaru ya girme ni a rayuwa.

Amma sai gardama ta sarke a tsakanin mu, sai aka ce a yi kuri’a, sai aka yi, kuma ya dauko shi ne Shugaba. Daga lokacin nake ba shi girma, yana mutunta ni har Allah ya sanya ya yi shahada. A ranar na fada masa cewa na samu alaka da ’yan Rediyo Kudirat ta hannun Tajudeen Abdurrahim. Wannan ya sa ake yawan kawo maganar Malam kullum a gidan rediyon.

NADECO DA REDIYO KUDIRAT

Lokacin Abacha na mulki ya sanya kafar wando da kasashe da kabilu da kungiyoyi daban-daban da mutane. Kasashen Turai sun yanke hulda da shi sakamakon kashe su Ken Saro-wiwa, aka kuma dakatar da kasar daga kungiyar kasashe renon Ingila.

Kasashen Amurka da kawayenta sun yanke hulda da kasar saboda kin ba Abiola mulki, da kuma wasu halayya na take hakkin bil’adama. An kafa kungiyoyin dawo da dimokradiyya daban-daban a ciki da wajen kasar. A cikin kasa yana tsare da su ’Yar Aduwa da Obasanjo, ya kuma dira a kan ’yan uwa Almajiran Malam Zakzaky. Wadda ta yi kaurin suna ita ce NADECO, wadda a cikin ta su Wole Soyinka suke da irin su Bola Ahmad Tinubu da mai buga jaridar Sahara Reporters, da dai mutane da yawan gaske. NADECO suna da gidan Rediyo wanda suke kira da Rediyo Kudirat, suna watsa labaransu da Hausa, Turancin Fijin da kuma Yarbanci.

Har yanzu ban san yadda aka yi ba, wata rana ina karatu a British Council Library da ke Kano, wani ya kawo mani wata takarda cikin ambulan, a cikinta da katin buga waya a NITEL, lokacin kana iya sayen katin waya, da ka je NITEL sai ka saka shi ka kira lambar da kake so in ka gama magana ka zare abinka. Da takarda da lambar waya an rubuta “ka kira lamban nan”. Ina amsa na yi maza na nufi NITEL na kira lambar. Sai wanda ya amsa ya ce sunansa Tajo da Hausa radau.

Ya ce; “Ina son duk abin da ke faruwa a kan kuntatawa mabiyan Zakzaky ka rika turo mana muna sa wa a gidan Rediyonmu. Da kuma wasu abubuwa da ke faruwa na cin zarafi da tauye hakki a nan arewacin Nijeriya”. Ya gargade ni da taka-tsantsan da kuma cewa in na yi kuskure na san sakamakon. A lokacin duk wanda aka sani na da alaka da Rediyo Kudirat kisa ne, babu wani zuwa kotu.

Yadda muka rika yi wannan kuma labari ne mai zaman kansa, amma kowa ya san a lokacin gidan Rediyon Kudirat kullum sai ya yi maganar Malam Zakzaky, duk wani motsi ko kokari ko wani taro na ’yan uwa, ko wani nau’in zalunci gare su, sai gidan Rediyon ya fada.

Wani gata da muka rika samu shi ne duk wata shela da kungiyoyin NADECO za su yi a ko’ina a duniya, sai sun fadi halin da Malam Zakzaky da kuma ’yan uwa suke ciki, haka kuma sun sanya duk jaridun Kudu suna ba halin da ’yan uwa suke ciki muhimmanci. Duk jaridun da za a dauko na waki’ar Abacha, za a ga cewa rahotanninsu masu tausayawa ne da tallata halin da ake a ciki. Ban taba maganar da kowa ba, saboda ina tsoron da wa zan yi ya fitar da ita, kuma a lokacin kisa ne kai tsaye.

Mutum farko da na yi maganar da shi a duniya shi ne Ibrahim Usman, inda na fara fada wa gidan Rediyon cewa zan shigo da wani wanda zai rika kawo bayanan Kaduna koyaushe, kuma yana aiki da gidan Rediyo ne, sun mani tambaya na yarda da shi? Na gargade shi? Ya san hatsarin da zai shiga? Duk na shaida masu, na’am. Suka amince, sannan na shaida masa. A ranar ma mun yi gardama daga baya ya amince. Muka zama mu biyu daga Arewa kamar Wakilai ne na gidan Rediyon muna bayyana masu me ke faruwa. Suna da wani sashen Turanci zalla, Ibrahim Usman ya rika aika wa har da sashen na Turanci zalla.

An rubuta littafai a kan wannan gwagwarmayar ta NADECO da Rediyo Kudirat, duk sunayenmu sun fito ni da sunan da na rika amfani da shi Dan Azumi, shi kuma Ibrahim Usman da sunan Ilolo. An yi wani Decumentry na TV, Ibrahim Usman ya yi magana a cikin sa a madadinmu. Lokacin ma sai da muka samu matsala. Ya ce bai yi, sai mun shaida wa Malam Zakaky ya amince. Na gamsar da shi da kyar. Saboda a lokacin mun tsara cewa wata rana za mu samu lokaci mu iske su Malam mu ba su labarin abin da muka yi, kafin kowa ya san labarin.

Ina tuna wani lokaci da saura kiris da an kama mu a NITEL na Kaduna. Tsarinmu in za mu aika da sako daya zai je, daya kuma ya koma gefe kamar yana jiran waya, ko yana waya, idan muka ba da Fax. Fax wata hanya ce a da can ta aikawa da takarda bisa tsarin fasaha ta waya, in muka biya kudin Fax lokacin da aka gama turawa, sai ka yi maza ka zare takardarka, ka bar wurin.

Tsarin da muke yi shi ne daya zai je kamar zai buga waya, dayan kuma ya aika da sako, in an samu matsala, daya zai gudu ya bar dayan ya fitar da kansa. A ranar an yi shari’ar su Malam Zakzaky, sai muka nufi NITEL don aika wa Rediyo Kudirat labari. Ni na je wajen aikawa da sakon FAX, Ibrahim ya je wajen buga waya, kamar yadda mukan tsara, ashe a ranar duk jami’an tsaron farin kaya na wajen suna sa ido, sai da na biya kudin aka fara turawa sai jikina ya ba ni, wani na lura da takardar da nake son turawa. Ashe Ibrahim ya lura yana yi mani alama, amma ban gane ba, sai kawai ya fita. Yana fita sai ya bar duk yankin wajen, ni ma ina lura cewa lallai ana kallo na, na daga kaina inda Ibrahim ke tsaye, na ga ban gan shi ba, sai na san dubu ta cika.

Sai na fito da taba sigari na kunna, na ciro wata takardar na ce wa mai aikin in ka gama wannan ga wannan. Na ciro kudi na aje masa, sai na laluba aljihuna, na yi irin zagin na ashar, na ce takarda ta ta fadi, na fara dube-dube kamar na ya da wata takarda. Na koma ina dubawa, ina tambayar masu shiga da fita, don Allah ko sun ga wata takarda. Da haka na fito waje. Na fito, cikin taimakon Allah, wani dan mashin na tsaye na yi daraf na haye na ce mu je kawai. Bayan mun dan yi yawo da shi na tabbatar da babu mai bin mu, na ce ya kai ni ofishin NEW NIGERIA, a nan na iske Ibrahim Usman gindin masallaci ya yi tagumi.

TSALLAKE RIJIYA NA BIYU

Rediyo Kudirat da NADECO sun dau Kano da muhimmaci, domin nan ne garin Shugaban Kasa kuma jalla ce babbar Hausa a Arewa, sukan yi taro sosai a garin, wani lokaci sukan hadu a wani wajen wasanni da ake kira ROXY, wanda yake hanyar zuwa filin wasa. Wajen kato ne, yana da kayan wasa kala-kala da wajen cin abinci da dakunan gudanar da taro. Akwai lokacin da suka zo Kano suka yi taro, na kira Ibrahim Usama ya zo daga Kaduna, domin ya hadu da Shugaban gidan Rediyon. A ranar muka yi taronmu na farko fuska da fuska mu uku, ni, Ibrahim Usman sai Tajo. Ibrahim ya zo da jaddada bukatarmu cewa, muna so a kara fadar halin da Malam (H) da almajiransa da ke tsare ke ciki.

Tajo ya tabbatar mana da cewa duk tsarinsu suna sanya almajaran Malam (H). Ya ce ganawarsu da shugabannin kasashe da kungiyoyi abin na tasiri. Ya ce Jakadan Birtaniya zai tura Wakili a zaman shari’ar da za a ci gaba, har ma ya nemi bukatar haka a rubuce ga gwamnatin Nijeriya. Kuma Wakilin ofishin jakadancin na Ingila ya halarci kotun na shara’ar su Malam.

Ranar muka san yadda aka yi kasashe suka nuna damuwarsu a halin da ’yan uwa suke a ciki zamanin waki’ar Abacha. Ubangiji cikin hikimarsa ya yi amfani da Rediyo Kudirat da NADECO.

Ya gargade mu kan kin amincewa da kowa. Ya ce, idan ka amince da wani, kai kuma ba ka san da wa ya amince mawa ba. Don haka babban makami, sirrinka yana cikinka, sai wanda ya zama dole.

Wannan taron ashe jami’an tsaro sun san da shi. Don haka suna sa ido, bayan gama taron kowa shi daya yake fitowa ya kama gabansa. Ibrahim ya tafi Kaduna, ni na tafi inda nake da zama. Tsarina zan fadi inda za a sauke ni a bayyane, amma zan sulale in sauka tare da wasu in sun zo sauka, ina da hanyoyin zuwa dakina sun fi 10, kuma in aka sauke ni, ina iya daukar awa ban kai dakina ba, ina yada zango da tsaye-tsaye, ba ni isa dakina sai na lura, ban kuma fitowa sai na sanya ido sosai.

Ina shiga mota sai na ce wa yaron motar Kurna Tudun Bojuwa, amma sai na sauka a shagon wani dan uwa Marigayi Malam Abubakar Batsari mai Bara’a Chemist. Ashe na shigo mota da wani jami’in tsaro, ga alama bai lura da inda na sauka ba. A shagon Bara’a na dade, daga nan na yi ta tafiya har zuwa dakina.

Da safe ’ya’yan Yahaya Kunya masu kawo mani abinci daga gidansa, Salahuddeen da Nusaiba, suka zo, lokacin su kadai ke zuwa waje na, suna kanana za su kawo man abinci kullum safiya, da na ji an taba kofa na san su ne. Bayan na bude sun shigo sun aje abincin kamar kullum na dan yi masu wasa.

Ran nan suna tafiya sai na lura wasu da ban aminta da su ba sun wuce ta gaban dakin. Kuma daya yana kallon fuskokin duk masu wucewa a tsanake. Na yi sa’a, daya ya tsaya gaban dakina. Na ga yadda a jikinsa kamar sakarai, amma yadda a tsanake yake kallon mutane na san lallai wata fuska yake son gani. Sai na kulle dakina. A ranar ban fita ba. Sai da dare, na fito na je wani wajen buga waya da ke wajen Airport na buga wa Ibrahim Sheme waya a ofis dinsa da ke NEW NIGERIA. Na san Editoci suna kai dare a ofis, sai sun tabbatar sun gama aiki. Na ce ya ga Ibrahim Usman? Ya ce eh ya zo tare suka yi Sallah, har ma ya ba shi wani aiki ya yi masa. Na yi ajiyar zuciya, na ce in ya zo ka ce masa na bugo, amma na wuce Katsina.

Dama tsarin da muka yi shi ne in komai lafiya ya je ofishin Sheme, ni kuma zan buga waya in ba da alamin komai lafiya. Daga wajen wayar na wuce shagon Yahaya Kunya na shaida masa cewa za ni Katsina cikin daren, akwai wani lamarin gaggawa. Ya ba ni kudi, kila zan iske wasu bukatun gida. Cikin daren na shiga Katsina na nufi gidan wani abokina mai suna Awwal NEPA, dan Jos ne, aiki ya kawo shi Katsina, yanzu yana Malumfashi da zama shi da iyalinsa. A lokacin waki’ar dakinsa nakan fake in ina cikin Katsina. Daga nan nake tafiyar da duk harkokina, sai na kwana uku, sannan in dawo Kano.

A lokacin waki’ar Abacha rayuwar Ibrahim Usman ta kasance ya duniya za ta san halin da Malam Zakzaky da sauran ’yan uwa suke ciki. Mun rubuta wasiku zuwa wurare daban-daban. Mun yada labarai ta hanyoyi daban-daban. Mun hada kai da wasu kungoyoyi don cimma manufar hakan, kana iya cewa hatta wannan dimokradiyyar da ake tinkaho ana cikin ta, mun taka rawa, domin mun yi aiki tare wadanda ke son da dimokradiyyar a bisa manufa daban-daban. Amma akwai abin da ya hada mu, su suna son kawar da soja, mu kuma sojan ya tafi don Malaminmu da ’yan uwanmu su fito, su kuma a kori soja. Lokacin babu duk kafofin intanet na Social Media. Allah ya yi amfani da Ibrahim Usman wajen gagarumin aikin.

Wata hira da Wole Soyinka ya taba da yi da BBC a 1998, lokacin yana gudun hijira, aka ce ya suke son cimma manufarsu? Ya ce; “Muna tare da mutane daban-daban a cikin Nijeriya wadanda manufarmu daban-daban ne, amma alkiblarmu daya ce, kuma muna tafiya a wata lema daya. Ya ce wasu daidaiku ne, wasu kuma kungiyoyi, kowa da dalilin da ya sanya yake tare da mu.”’

KUDIN AYYUKANMU

Duk abin da muka rika yi, ba wata Da’ira ko ta gari da aka rika ba mu wani tallafi. Ba wata kungiya da ta rika taimaka mana, babu wanda ya san me muke yi, tsoro muke a sani. Don mun san sakamakon da zai biyo baya daga gwamnati kisa ne babu shari’a. Ibrahim Usman yana aiki, yana da albashi, ciki koyaushe yake matsewa, mu hada a yi duk abin da za a yi. Matarsa ta taba yi mani koke, na zo garin ta kira ni gefe daya ta ce ka ji, ka ji, kullum in ya amso kudinsa, sai mu zo wajen lissafin yadda za a kashe su, sai ya fitar da wasu ya ce wadannan na wani aiki na musamman ne. Ta kalle ni ta ce wai wane aiki ne yake da wadannan kudaden? Ko aure yake nema? A ranar ta ba ni tausayi,. Sai na ce mata adashe yake zai sayi fili, ya gina gida, sai ta daka tsalle domin murna. Cikin zuciyata na ce Allah ka gafarta min. Ina nufin fili da gida, a gidan Aljanna. Daga ranar ba ta kara daga masa hankali ba a kan kudin da yakan ware in ya amso albashinsa.

Ni kuma yadda nake samun nawa abin da zan saka a wajen aikin, shi ne Edita Ibrahim Musa bai taba kiyawa ba, a duk lokacin da na ce a ba ni kudi zan wa iyalina hidima, da na fada masa, zai ce Hasan Baffa ya ba ka. Shi ma Hasan Baffa ban taba zo masa da bukata ta kudi ba ya ce a’a, zan amsa na yi ma iyalin nawa, sai mu hada ai wani aikin da su.

’Yan uwan Kano sun nuna mani karamci cewa wani da yake gudun hijira yana wani aiki na musamman, don haka duk lokacin da muka hadu, wasu masu halinsu ka ji sun ce ga wannan an kai wa iyali. ’Yan uwan suna da yawa, amma zan iya kawo su. Alhaji Yahaya Kunya shi ne mai masaukina. Alhaji Adamu Gobirawa, Alhaji Kabir Mai Fata. Alhaji Sule Bacirawa a matsayin misali, cikakken sunayensu na a wani rubutu na da na yi wanda zan mai da shi littafi Mai taken; JARIDAR AL MIZAN A WAKI’AR ABACHA.

Akwai wasu ’yan uwa kuma masu sana’ar fata, biyu ’yan Katsina ne, daya dan Kano, Mustafa da Umar da kuma Usman, su wadanda suke da ofis a Goron Dutse sun rika daukar nauyin duk wata hidima ta iyali in na fada masu za ni gida. Na rika rubuta littafai in sa ALMIZAN ta buga, ciki ina samun wani abu, wani lokacin an rika kaddamar da wasu daga littattafan don ALMIZAN ta sami kudin shiga.

Kafin a fara waki’a ina da harkokina masu ja a Katsina, duk sai da suka koma zero, kudinmu sun rika tafiya a sayen katin buga waya da biyan kudin FAX na aikawa da takardu. Wani lokaci kuma aikawa da takardun ta gidan waya, da buga takardun na rika yin tawassuli da aikin, kuma ina ganin sakamakon har yanzu.

HAWWA’U IBRAHIM USMAN MAI DAKINSA

Malama Hawwa’u, matarsa a lokacin, ta nuna wa Malam Ibrahim kula da soyayya. Ni ganau ne. Kullum kafin mu dawo ta shirya mana abinci ta gyara. Kullum tana hakuri da mu a kan koyaushe muna iya fita, kuma in mun dawo kus-kus-kus dinmu ya yi yawa. Za mu dade a waje ana magana, in kuma ya je raka ni sai ta gan shi. Kullum muna ’yan rubuce-rubucenmu, ba mu son ta san me muka rubuta, ko me muke a ciki, amma ba ta taba damuwa ba, ko a fuska ban taba ganin canji ba, a kan in na zo gari, mijinta ba ya da zama har na yi masa bankwana, ko kuma kawai ya ce mata zai tafi waje na a Kano.

HIRARM U DA MALAM ZAK ZAKY

Bayan fitowar su Malam (H) akwai wata tattaunawa wadda Edita ya sanya in je in yi da su Malam (H). A hirar ce muka yi wa Malam tambaya a kan rubuta littafin MISSION OF MAN ON EARTH nasa, inda ya yi bayanin hatta rubuta littafin tarihin kasar Zazzau. Da Edita ya ba ni aikin sai na fada wa Ibrahim Usman, tare muka je inda Malam ya karrama mu, muka sha shayi da wani biskit mai dadi. Daga nan muka shiga ofis din Malam muka tattauna. Ina jin kila a lokacin mu ne ’yan uwa na farko-farko da muka fara shiga wannan ofis don yana sabo.

A lokacin mun yi niyyar mu ba Malam labarin abin da muka yi, amma sai na roki Ibrahim Usman mu bari sai a wani lokaci, amma kafin hirar da bayan hirar ta jarida, mun tattauna da Malam sosai. Ibrahim Usman ya ji dadin wannan karamci da na yi masa, domin wannan shi ne karon farko da ya samu kebewa da Malam. Daga gidan Malam muka nufo gidan surukansa, a nan ya yi wani alkawari da shan alwashin cewa har ya mutu yana tare da yi wa Malam hidima. Ban mantawa ya ce; “Wani son sa ya shiga jikina da ban iya misaltawa”.

ZAMANSA A KANO.

Bayan waki’a, an dauke Ibrahim Usman aka kai shi aiki a wata sabuwar mujallar OUTLOOK da aka kafa a Kano, Sunusi S. Muhammad ne Edita. Ibrahim Sheme ya yi mani magana na yi masa, wanda har ya koma da iyalinsa Kano, wanda har nakan je gidansa. Ya yi watanni a nan, sai ya ga mujallar tana tangal-tangal, wanda yake son assassa ta bai tanadi kudade masu kwari ba. Sai muka yi shawara da shi, inda ya koma mujjalar RANA da HOTLINE ta Sani Kontagora. Shi ma duk lokacin da na shigo Kaduna muna tare.

Ibrahim Usman ya samu aiki a matsayin jami’in watsa labarai na matar Gwamnan Kaduna Asma’u Makarfi. Lokacin da yake wannan matsayin sau daya na taba zuwa ofis nasa. Sau daya na gan shi, lokacin da muka samu wata yankewa ta hulda na tsawon lokaci. Daidai lokacin hidima ta yi man yawa, shi ma hakan. Bayan ya sauka mun ci gaba.

Da aka sami wata matsala da Harka da gwamnatin Kaduna, na san rawar da Ibrahim Usman ya taka har lamarin ya kwanta. Har ma aka kai ga yin wata ganawa tsakanin wasu Wakilan ‘yan uwa da manyan jami’an gwamnatin na Kaduna. Ni ma na sa albarka. Don a lokacin Malam Ibrahim Potiskum ya yi mani magana na ce zan yi abin da zan iya, na buga wa Ibrahim Usman waya na tarar ya yi nisa a yin wani abin, na kara da nawa aka cimma nasara.

Har Allah ya dau ransa ina cikin aminansa na shawara, amma ban da shawara daya, wadda ba ya tambaya ta, ita ce abin da ya shafi harkar iyalinsa, don ya san ina da wata matsaya mai tsauri. Shi ya sanya ya kebe ni a kan maganar.

Gab da zai yi shahada, muna ta kokarin ya samu canjin wajen aiki, ya nema a wata Hukuma mai zaman kanta a Jigawa, wadda na kushe saboda muhimmacin zaman sa a Kaduna. Na sanya ya rubuta wa DAILY TRUST, dama lokacin sun ba da sanarwa za su dau ma’aikata, har na yi niyyar zuwa Abuja don kamun kafa ya samu. Ya rubuta wa PREMIUM TIMES, ya kuma rubuta a wata Hukumar kare hakkin bil’adama.

WAKI’AR ZARIYA 2015 DA SHAHADARSA

Ina Kano ranar da za a sanya tuta ban je Zariya ba, kuma a ranar ba ni da wata niyya ta zuwa Zariya. Na dawo da dare don haka na kwanta a gajiye, ban sani ba ashe da dare an yi ta min waya a fada min abin da ke faruwa. Da asuba na tashi Sallah a bisa al’adata naka bude intanet na mintuna kadan in ga me duniya ke ciki. Sai na rika ganin labarai kamar almara. Da safe ’ya’yana suka zo suna kara min haske a kan wasu da suka yi waya da su, har ma suna neman in amince masu su tafi Zariyan.

Sai na fara waya da wasu majiyoyi da nake da su a jami’an tsaro, ai duk inda na tuntuba sai a shaida min cewa, matsalar babba ce, kuma soja sun kasa sun tsare sun ce matsalarsu ce, kuma aiki za su yi. Wani kai tsaye ya shaida mani cewa, in kana da wanda zai ji maganarka, ce masa ya bar yankin kafin wuri ya kure, in kuma bai je ba, fada masa kar ya je. Na rika samun bayanai masu ta da hankali.

Wanda ya fara fado mani a rai shi ne Ibrahim Usman, domin ina ganin za mu iya sake farfado da tsarin aikin da muka yi a baya mu canza masa fasali da zamanatar da shi, mu yi shi a yanayin da ake neman shiga. Don haka sai na kira shi, na yi sa’a ya dauka na ce masa ya juyayin yanayin da ake ciki a Zariya? Sai ya fara ba ni bayani, sannan ya ce yanzu yana kan hanya ta zuwa Zariya. Sai na fara ba shi bayanin da na ji, na kuma roke shi da kar ya je Zariya. Ai nan sai gardama ta sarke tsakanin mu, yana min nasihar in ji tsoron Allah. Ya ce shi ya dade da shan alwashi da rantsuwar amsar kiran Malam duk tsanani. Na shaida masa cewa, abin da za mu yi yana cikin amsar kiran na Malam. Muna cikin magana sai ya katse wayar.

Na buga wasu wayoyin, na tsara wani shirin nawa yadda zan iya hana shi tafiyar, sannan sai na sake kiran sa sai na ce ina neman alfarma uku, ya yi min su. Ya ce yana sauraro na. Na ce na farko yana ina? Ya ce da karfi, na san manufarka, ban fada maka inda nake. Na ce na biyu, ina son ka saurare ni mintuna 10 zuwa 15 kacal. Nan ma ya ce; “na san inda ka nufa, ka yi hakuri ba ni iyawa”. Na uku shi ne in ka isa Zariya ka kira ni. Nan ne ya nisa ya ce sai abin da hali ya ba da. Nan muka yi bankwana ya kashe wayar na yi ta sake-sake na. Daga baya na bar wa Allah lamarinsa. Ibrahim Usman ya san hatsarin da ya ka iya fuskanta don na shaida masa abin da na ji, amma kauna da sallamawa ga Sayyid Zakzaky (H) suka kai shi Zariya.

BAYAN ABIN DA YA FARU

Bayan an yi abin da aka yi a Zariya, na yi ta buga wayar, sau daya wani matashi ya dauka, na ce ina mai wayar nan? Sai na ji ana izgili a muryoyin da ke bayan wayar, ana cewa me za a ce ya yi shahada, ko kuwa an kashe shi? Nan na fara gane cewa ba wanda ya san inda yake sai Allah. Matarsa ta bugo min waya tana kuka. Na kasa ba ta amsa har wayar ta yanke. Na rika bin bahasin yadda ya rasu, wanda na ji ruwaya daban-daban, ina ji ina tattarawa ina rubutawa, zuciyata ta kasa amsar cewa ya yi shahada.

Na rika jin cewa wani al’ajabi zai faru a ce ga shi da ransa, ko kuma ga shi can a wani asibiti, ko kuma yana cikin wadanda ake tsare da su a gidan yari. Ana cikin yanayin, Marafan Sakkwato, Marigayi Umaru Shinkafi ya bugo min waya lokacin yana jinya a wani Asibiti a London ya ce, in je Kaduna za mu hadu da wasu mutane don gano gaskiyar abin da ya faru a Zariya. Na hadu da su, ban san su ba, ban taba ganin su ba, kuma ban kara ganin su ba har yanzu. A nan ma na yi amfani da damar na rika binciken ko Ibrahim Usman na da rai. Na nemi wata alfarma aka yi min, inda aka rika bin layin wayar Ibrahim Usman ko za a gano inda yake, muka gano shi a wani juji an jefar da shi.

Na rika bincike a duk wuraren tsare mutane na jami’an tsaro, inda a neman alfarmar na rika tambayar mutane uku. Wadanda sune Ibrahim Usman, Fatima Ahmad Gasuwa da Ibrahim Dutsinma. Na rika fadin cewa daya abokina ne, daya ’yata ce, dayan kuma dan uwana ne, amma duk inda na watsa komar bincikena, sai a ce babu duriyarsu. Fatima Ahmad Gashuwa, ’yar Malam Ahmad Gashuwa ce, wanda yake amini ne na kut da kut. Na san tsananin son da yake wa Fatima, na san yadda ya bugo min waya hankalinsa tashe a kanta, don haka na sanya ta a cikin wadanda na rika neman ina suke?

Alhaji Ibrahim Dutsinma shi ne mai kamfanin Alheri Block Katsina, muna mutunci da shi sosai, a lokacin rayuwarsa. Mahaifiyata makwabciyarsu ce. Da abin ya faru, ta kira ni a waya, tana kuka ta ce don Allah ka bincika wane hali yake ciki? Don haka a lokacin bincike na, sai na dora a kan su ukun. Da fatan in an samu wata kafa ta nasara sai a dora daga kanta. A kara bincike kan nemo sauran, haka muka yi ta yi, har yau muna kan nema ba mu sallama ba.