AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Rahoto

Buhari na ’Yan Izala

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Bashi hanji ne, cikin kowa akwai shi. Yauma muna rokon a bi mu bashin mukalarmu mai taken shekaru biyu da aika-aikar dabbobi a kan mutane. Yau za mu yi magana a kan masu Gwamnati. Sune Wahabiyawa masu cin karensu babu babbaka a fadin kasar nan.

Ba su taba boye tarayyarsu da Buhari ba. Ina nufin ’yan Izala. Lokacin da Buhari ke neman shugabanci a wannan karo mafi yawansu, in ma ba dukkan su ba, sun ci, sun sha a wajen Shugaba Jonathan. Sai dai sun ci sun share baki da suka ga cewa Jonathan ya fadi a zabe.

Ka san Izala. Kullun uwar da ke gindin Murhu ita ce tasu. In uwar wasu na mutuwa, shakka babu ta Izala ba ta mutuwa. Su makwadaita ne. Kwadayinsu ya bayyana kamar yadda tozo ke bayyana a gadon bayan Takarkarin Bijimi.

Su na kowa ne. In dai mutum na cikin fada, tabbas shi nasu ne. In ka zama Shugaban Karamar Hukuma ko Gwamna ko Shugaban kasa, ko mai abin hannu, tabbas za su yi maka rowar kaulasan da shin mai ruwa. Za su yi maka rowa da abin da suka fi kyauta da shi, wato kafirci ko shirka.

Da zaran ka rike mukamin Gwamnati, ka samu kau da barar dutsen da suke jifa da shi. Ba sa kafirta masu mulki, duk barnar da suke yi. Kaulasarsu tana kan talaka.

A cikin hikimominsu sun zabi Jonathan don Naira. Amma da Buhari ya ci zabe, sai suka fi mai Kora shafawa. Suka ce nasu ne halak malak.

Sai wa'azozi suka canza, kamar yadda aka canza Gwamnati. Duk addu'a ta fuskanci Buhari. Ba ma addu'a mai kyau gare shi ba, hatta sukar Gwamnatinsa sai da suka samo masa haramci a cikin Kur'ani da Hadisi. Ka san nasu "Kur'anin" bai ida sauka ba har yau.

A yau ba gobe ba, Buhari shi ne komai a gare su. Shi ne Ubangiji abin bautar da babu wani tamfarsa. Shi ne ma'aunin Musuluncin ’yan Najeriya, in kana son sa kai Musulmi ne. In ba ka son sa kai "Kafiri" ne a fahimtarsu. Da ma su kungiya ce da ke bautar masu mulki.

Komai kazantar mai mulki, nasu ne. Kamar yadda aka ji daga bakin Na'ibin Limamin wani masallacinsu a Abuja. "Tunda Buhari ya kashe ’yan Shi’a, ya hana ’yan bidi'a sakewa ya yi mana komai." In ba ka san ’yan bidi'ar da wannan mutumin ke nufi ba, sune ’yan Darika da duk wanda ba ya Izala. Kar abin ya ba ka mamaki. Me kake tsammani daga wanda aka cire duk wani nau'in tunani da tausayi a cikin zuciyarsa, wanda ya dauki tallata akida, ya manta da ibada?

Yanzu Malaman Izala sai safa da marwa suke yi wajen ziyartar Shugaba mai kashe ’yan Shi’a dare da rana, suna sharara masa karya, kamar yadda suke wa mabiyansu. In ka ga Malam Mai fankeke yau, gobe kuma Malam mai Albasa zai je ya kai tasa caffar. Bayan sun cinye wa ’yan kasa kudin makaman da ya kamata a yaki Boko Haram da su a lokacin Shugaba Jonathan, sai ga su yanzu suna bin Buhari don ya ba su kudin jinin ’yan Shi’a.

Su addini a gun su shi ne neman Kudi, su yi aure su hau motoci, su sa kayan ado, su burge mutane. Wannan shi ne iyaka ga iliminsu. Duniya kawai, lahira kuma sai an je. Kai ka ce karya ba laifi ba ne a addinin wadannan masu busassun zukata. Dubi yadda wani Shehunsu mai suna Yakubu Musa Kafanchan, a da amma yanzu Yakubu Musa Katsina ya yi ta sharara karya a gaban Buhari, a lokacin da ya kai tawagar Izala don maula fadar Ubangijin nasu; ya yi ta karya kamar kudin duba.

Cikin karerayin har ya nuna wani daga cikin su, wai da tsintsiya yake kwana, da ita yake tashi. Ni kuma a sanina ko da Kura'ni ka ce wani na kwana da tashi da shi, sai dan Izala ya tambaya wa ya ce ka yi haka balle tsintsiya?Yakubu Musa ya yi wannan karyar don kawai ya dadada wa Buhari rai. Irin wadannan Bambadawa sune a masallatai da sunan masu nuna wa mutane hanyar shiga Aljanna.

Kafin Yakubu Musa Kafanchan ko Katsina, an nuna Abubakar Gero Argungu, shi ma yana fada wa wani Sarki tasirin Izala a gun Buhari. Sune suka taimaka wa Buhari wajen nasarar da ya samu a zaben da ya gabata. Bai tsaya a nan ba ya ce su suka ka da Jonathan. Ya fadi yawan shagunan da suke kira masallatai, inda ya ce sun fi miliyan guda. Amma bai fayyace masallacin na yan tsohon alkawari da ke Garin Jos ne ko na sabon alkawari da ke Kaduna ba? Ka san ba sa kunyar karya.

In karya a kan ’yan Shi’a halas ne, to karyar masallatai shi ma halas ne? Tabbas Izala da Buhari kawaye ne na kut-dakut. Na farko ya yi abin da suke nema, kuma suka fi so fiye da Aljanna, shi ne kashe ’yan Shi’a. Ya kashe ’yan Shi’a yaransu da matansu, samarinsu da tsofaffinsu, Malumansu da Dalibansu. Ya kashe ta harbi da Bindiga da kuna da wuta, wasu ma cikin mata sai da aka yi musu fyade, kana aka kasha su. Wannan duk abin yabo ne a gun ’yan Izala. Tausayi da mutumta dan’adam, duk babu shi a cikin addininsu mai suna Wahabiya. Bayan kashe ’yan Shi’a, sai kashe ’yan Darika wanda suke fata Buhari ya cika musu burinsu in ya dawo a karo na biyu. Hasbunallah!

Allah kar ya cika wa Buhari gurinsa na dawowa a karo na biyu don darajar Annabi a wajen Allah. Wannan addu'a ce daga wanda Buhari ya zalunta.

Bari mu duba mu gani, da wace hujja Izalawa ke nuna wa Buhari soyyayyar da ta mai da shi tamfar wanda ba ya laifi? In Musulunci ne, wace alaka Buhari ke da ita da Musulunci? Babu wani dan Adam da ya taba shedar Buhari a matsayin mai son addinin Musulunci. In suna son sa don Arewanci ne, babu wani mahluki da ya taba cewa Buhari mai kishin Arewa ne.

Duk wani mutum in ba Manzon Allah ba yana kuskure a wani waje, kana ya yi daidai a wani waje, kamar yadda yake a makarantar Ahlissunna da Izalawa ke ikirarin suna bi. Shin Buhari bai yi kuskure ko daya ba a cikin shekaru biyu da ya yi yana mulki? In akwai me Izalawa suka ce a kai? Babu. Shin ba Buhari ba ne ya nunka kudin aikin Hajji? Me Izalawa suka ce masa? Babu!

In jinin ’yan Shi’a ya halasta a zubar, to jama'ar da sakacin Buhari ya sa ake ta zubar da jininsu a kullu yaumin fa? Me izalawa suka ce a kai? Babu! Da aka ce wata mata ta yi kalmomin batanci ga Manzon Allah, har wasu suka zartar mata da hukunci, me Buharin Izala ya yi? Cewa ya yi a kama su a kai su Kotu a hukunta su, hukuncin wadanda suka yi kisan kai. Me Izalawa suka ce a kan wannan goya wa batanci ga Manzon Allah baya da Buhari ya yi? Babu! Sai ma wani abin tsoro ya bayyana daga bakunan Malaman Izala - Fantami da Kabiru Gombe. Buhari na cewa a hukunta wadanda suka hukunta matar, sai wadannan ‘Malumma’ biyu suka ba da fatawar cewa "Haramun ne kashe wanda ya zagi Annabi (saw).” Duk dai don su dadada wa Buhari, kuma su samu shiga a wajensa. Fantami bai tsaya nan ba sai da ya caccaki Imam Khamaini a kan shahararriyar fatawar da ya ba da ta kashe Mujirimi Salman Rushdi Mal'uni. Wannan sayen Jahannama don neman yardar Buhari ina za ta kai Malamen Izala?

In kuma don Arewaci suke son Buhari, ina suke a lokacin da Buhari ya ba da belin Nnamdi Kanu daga kurkuku, kamar yadda kotu tayi umurni, amma ya ki ba da belin Sambo Daski dan Arewa? Ba za mu kawo maganar Malam Zakzaky a nan ba, don mun san da Izalawa muke magana. Amma Dasuki ba dan Shi’a ba ne. Muna iya ba da misali da shi. Me ya sa in Izalawa sun je maula fadar Buhari ba sa masa nasiha a kan wannan zalunci da yake yi wa mutanen Arewa?

Me ya sa Izalawa suka zabi Buhari fiye da Allah da Manzonsa? Don kashe musu ’yan Shi’a kawai? ’Yan Shi’a da Buhari ya kashe, shin da umurnin wa ya kasha su? Aya ko Hadisi? Babu ko daya!

Yanzu Buhari na neman Izala tunda Bera ya dandani zakin Daddawa, dole ya nemi kari. Buhari ya samu mulki da jini da gumin wasu. Bai rasa kowa a zuriyarsa ba. Ko kwarzane babu wanda ya samu daga cikin zuriyarsa a duk tsawon yakin neman zabensa. Jinin ’ya'yan wasu ne ya zuba. Kadarorin wasu ne suka salwanta, shi dai ya tsinci Dami ne kawai a Kala. Don haka babu ruwansa da kowa, sai dai ’yan izala. Wannan ya kamata ya zama darasi babba a gun ’yan Darika da sauran musulmi, in har Buhari ya sake fitowa neman shugabancin kasar nan. Dole su gane cewa lokaci kawai yake jira kafin ya yi musu abin da ya yi wa ’yan Shi’a. Wannan kuma jazaman ne zaman Fir'auna a wuta. Shakka babu Buhari ya nuna wa Duniya su waye mutanensa. Imma ba ka sani ba, sune Izalawa wadanda suke tseye kyam don kare shi, duk da yunwa da matsin da ya kawo wa talakawa. Kana iya cewa a yau ba gobe ba, ko Allah da Manzonsa Buhari ya zaga, wadannan batattu ’yan Izala za su yi masa uzuri, imma ba su goya masa baya ba. Don shi nasu ne. Su kuma nasa ne. Ko mai karatu ya fahimci me ya sa Alkalami ya kira wannan mukala Buhari na ’yan Izala?

ALLAH YA JI KAN ALARAMMA MALAM HALADU

Allah ya yi wa Alaramma Malam Haladu da ke zaune garin Sabon Kauye jihar Jigawa Karamar Hukumar Jahun rasuwa ranar Asabar 5/1/2018 mai kimanin shekara 95. Ya bar ’ya’ya 8, da jikoki 25. Da fatan ’yan’uwa za su sa shi cikin addu’a.