AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

Rahoto

2019: Tafi ka huta! Cewar Obasanjo ga Buhari

Daga Wakilinmu tare da bbchausa.com


 mallam

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ya kamata ya hakura da neman ta-zarce a shekarar 2019, saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa, don haka ya tafi gida kawai ya huta.

A wata budaddiyar wasika da Obasanjo ya fitar, wacce BBC ta samu kwafi, tsohon Shugaban kasar ya ce, mulkin Najeriya al'amari ne da yake bukatar mutum mai cikakkiyar lafiya, wanda kuma shekarunsa ba su ja ba, saboda aiki ne ba dare ba rana.

Obasanjo ya kara da cewa, Shugaba Buhari yana bukatar lokacin da zai zauna ya yi tunani, ya murmure, ya kuma huta da kyau, ta yadda daga baya zai iya shiga sahun tsofaffin shugabannin Najeriya da suke da gogewa da hikima da basirar da za su dinga bayar da shawarwari don ciyar da kasar gaba.

A wasikar ya kuma tabo yadda rikicin makiyaya da manoma yake daukar wani salo na daban, yake kuma kara muni ba tare da gwamnatin Tarayya ta dauki wani mataki na magance matsalar ba.

"Kuma abin takaicin shi ne yadda bayan kwana guda da kashe kimanin mutum 73 a jihar Benuwe, sai ga shi wasu Gwamnoni da ko sakon jaje ba su aika ba, sun goyi bayan Shugaba Buhari ya sake neman tsayawa takara a 2019.

“Bai kamata su yi hakan a wannan lokaci ba, bai kamata a mayar da batun rikicin manoma da makiyaya na zarge-zargen juna ba. Dole ne gwamnati ta jagoranci kawo mafita kan hakan," in ji Obasanjo.

A ganinsa, raunin gwamnati da suka dabaibaiye kasa sun hada da karuwar talauci da tabarbarewar tsaro da tattalin arziki da azurta dangi da abokan arziki da saba doka da wanke masu laifi, da kuma rashin sanin makamar hadin kan kasa.

Tsohon Shugaban ya ce, wadannan dalilan ne suka sa ya yi watsi da jam'iyyarsa ta PDP domin mara wa 'yan adawa a zaben da ya gabata, domin, a cewarsa, yana ganin matakin shi ne ya fi dacewa da Najeriya da ma Afirka baki daya a lokacin.

"Halin da Najeriya ta shiga ne ya sa jama'a suka fito jefa kuri'a domin kawar da dan’uwana Jonathan".

Obasanjo ya ce, duk da cewa shekaru hudu da suka gabata ya yaga katin jam'iyyarsa ta PDP, tare da fitowa baro-baro ya bayyana yin bankwana da siyasa, amma hakan ba zai sa ya kawar da kai da rashin nuna damuwa ga ci gaban Najeriya da Afirka ba.

Sannan Cif Obasanjo ya ce, tun da farko ya san inda Shugaba Buhari ke da rauni, kuma ya taba magana tare da rubutu a kai tun kafin 'yan Najeriya su zabe shi.

Kuma ya jefa masa kuri'a ne saboda a lokacin ana neman wani zabi sabanin Jonathan.

A cewarsa, wannan ne dalilin da ya sa ya rubuta wa Shugaba Jonathan wasika mai taken "kafin lokacin ya kure", don ya dauki mataki cikin gaggawa, amma kuma ya yi watsi da shawarwarin.

Obasanjo ya ce ya san Buhari tun kafin ya zama Shugaban kasa, kuma ya taba fada cewa, yana da rauni a ilimin fahimtar tattalin arziki, amma ya zata zai iya amfani da kwararrun da za su iya taimaka masa.

"Na san cewa ba za ka iya bayar da abin da ba ka da wadatar sa ba, kuma tattalin arziki fanni ne da ba ruwan sa da bin umurnin soja," a cewar Obasanjo.

Tsohon Shugaban ya ce, akwai 'yan Najeriya da dama da za su iya taimakawa a fannin ci gaban tattalin arziki da kuma harkokin kasashen waje.

Sannan ya ce, akwai manyan zarge-zargen da ake yi game da wadansu da sai abin suke so ake yi a fadar Shugaban kasa da ya kamata a ce tuntuni an dauki mataki a kai.

"Wannan ai yana iya zama rashawa," in ji Obasanjo.

Tsohon Shugaban na Najeriya ya kuma ce, kin yin watsi da irin wannan al'ada tare da kawar da kai, tamkar rufa-rufa ne, maimakon gyara. Kuma tabbatar da adalci ya shafi aiki da hannu masu tsafta.

"Na san cewa shugaba Buhari zai yaki rashawa da tayar da kayar baya, kuma dole a yaba masa a ci gaban da ya samu a wadannan fannonin guda biyu, amma fa har yanzu da sauran aiki".

Cif Obasanjo ya ce, yadda aka bari rikicin makiyaya da manoma ke kara girma ba tare da neman mafita ba, baraka ce ga gwamnatin Tarayya.

Ya ce wani abin bakin-ciki shi ne, yadda wasu Gwamnoni suka fito suna yi wa Buhari kamfen, a yayin da a Benuwe ake zaman makokin binne gawawwakin mutane 73 da aka kasha, amma ba tare da Gwamnonin sun aika da sakon ta'aziyya ba.

Tsohon Shugaban ya ce, gwamnatin tarayya ce ya kamata ta zauna ta samar da mafita ga rikicin makiyaya da manoma domin kare rayuka da dukiyoyinsu.

Obasanjo ya zana abubuwa uku game da gwamnatin Buhari: 1. Gwamnatin 'yan’uwa da abokan arziki, da rashin daukar mataki a kan gurbatattu a fadar Shugaban kasa. 2. Rashin fahimtar siyasar cikin gida. 3. Dora laifin gazawar gwamnati a kan gwamnatocin da suka gabata.