AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

Rahoto

Wa ke kokarin auka wa ’yan uwa musulmi a Gashuwa?

Daga Muhammad Maitela Damaturu da Muhammad Bello Gashuwa


Wuyan mai

An bankado wani yunkurin gamin gambiza tsakanin masarautar Bade da karamar hukumar Bade (Gashuwa) na kokarin aukar da fitina ta hanyar auka wa ’yan’uwa musulmi almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky da ke garin.

Yunkurin, wanda suka tsara shi ta hanyar matakin dakatar da ’yan’uwa gudanar da jawabin tunatarwa a masallacin kofar fadar da suka bayyana da "wa'azi ba bisa doka ba", inda suka aika wa Wakilin ’yan’uwa wasikar dakatarwar, tare da shirya auka wa ’yan uwa matukar sun bijire wa umurnin.

Mabambantan kwararan majiyoyi sun tabbatar da cewa, da dadewa wasu makiya zaman lafiya ke kokarin rura wutar fitinar da sunan addini, wadanda suka zaku tare da kai-komo wajen ko ta halin kaka sai sun hana ’yan’uwa musulmi gudanar da wa'azi a masallacin, yayin da a baya tsohon Sarkin Bade, mai rasuwa Alhaji Mai Saleh Sulaiman ke taka wa irin wadannan bara-gurbin mutanen birki.

Jama'a da dama a garin sun yi matukar ta'ajibin wannan matakin tare da yin Allah wadai da wannan matakin gamin-gambizar da kokarin tayar da fitina, da bayar da hujjar cewa kowane mutum yana da ikon bin fahimtarsa ta addini, bisa yadda yake a kundin tsarin mulkin Nijeriya: dokar Nijeriya ta bai wa kowane dan kasa damar gudanar da addinin sa ba tare da tsangwama ba.

Bugu da kari kuma, yau sama da shekaru 20 da suka gabata, 'yan'uwa musulmi na Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky Gashuwa suke gabatar da tunatarwa a wannan masallacin (Pre-Khuduba) da kuma bayan kammala sallar Jumu'ar, yayin da kuma ba a taba samun wata hatsaniya ba ko tashin hankali.

Wani abin da ya kara daure wa jama'ar garin kai dangane da wannan wasika wadda karamar hukumar ta aike wa Wakilin ’yan’uwa da yammacin ranar Alhamis ta 11/1/2018: BDLG/ADM/S/180/VOL. IV da kwanan wata 11/1/2018 da kuma sa hannun Babale Dubagari Katuzu a madadin Shugaban Karamar Hukumar Bade, ana sanar da shi cewa daga ranar Juma'a 12/1/2018 an dakatar da tunatarwar da 'yan'uwa suka kwashe shekaru suna yi a Masallacin Juma'a na kofar Fada.

Har wala yau kuma, kamar yadda wannan wasikar ta nuna, an aika kwafinta ne zuwa ga Sarkin na Bade daga karamar Hukumar tare da shaida masa cewa an dakatar da tunatarwar da 'yan’uwa suke yi a masallacin, sannan ana bukatar fadar da ta sa ido don daukar mataki a kan duk wanda ya saba wannan umurni, saboda yadda tunatarwar da ake yi ta saba wa Dokokin Wa'azi na jihar Yobe mai lamba 4 na shekarar 1994.

Bisa ga wannan ne ya jawo da daren ’yan’uwa musulmi suka dauki matakan bincike tare da neman sanin dalilin abin da ke faruwa, amma sakamakon ya nuna akwai wani shiri a kasa na auka wa 'yan'uwa. Yayin da kuma wannan ya karade gari tare da kasancewa abin tattaunawa a wuraren zaman jama'ar garin da ma kauyuka.

Wani abin tambaya, wanda jama'a da dama ke son sani dangane da wadannan dokokin da aka ambata, dokoki ne tun na zamanin mulkin Soja, a lokacin Kantoma (Gwamna) Dabo Aliyu a 1994, yayin da kuma a gefe guda akwai kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na shekarar 1999, wanda kuma a ciki ya ba kowane dan kasa ’yancin gudanar da addininsa bisa yadda ya fahimta.

A hannu guda kuma, shin ina wadannan dokokin suke, sama da shekaru 20 da suka shude- wadanda ’yan uwa ke aiwatar da wa'azojin su? Sannan kuma ba a taba kiran ’yan uwa domin bayyana musu kuskure ko taka dokar da yanzu ake kokarin fakewa da ita ba.

Da dama wasu sun jama'ar garin sun so jin, shin wadannan dokokin sun shafi ’yan’uwa ne kadai da suke gabatar da tunatarwa a masallacin fada na Gashuwa kawai ko kuma ta shafi dukkan masallatan Juma'a ko masu wa'azi?

Kuma idan hakan ya shafi dukkan masu wa'azin jihar Yobe ne, shin an aika da kwafin wannan wasikar tare da daukar matakin dakatarwar ga dukkan masu tunatarwa a masallatan Juma'a da wa'azozi na karamar hukumar Bade da na Yobe gaba daya, ko dai dokar ta tsaya kan ’yan’uwa, almajiran Sayyid Zakzaky na Gashuwa ne kawai?

Rashin bayar da amsoshin wadannan tambayoyi, yana iya sa hankula su karkata tare da gaskata wasu bayanai da ke cewa, akwai wadansu mutane marasa son zaman lafiya da suke neman bin duk wata hanya da suka samu ko amfani da duk wanda za su iya amfani da shi wajen ganin sun haddasa fitina a masallacin da ma a garin Gashuwa gaba daya, da sunan addini.

Ballantana kuma, jama'ar garin sun fahimci yadda wasu sabbin matakai tare da kai-komon daukar bakin matakan da ba a saba ganin makamantan su ba a ranar Juma'ar da ta biyo bayan ranar da aka aika wa ’yan’uwa wannan takardar umurnin dakatarwa, a masallacin. Daga cikin irin wadannan sabbin matakan sun hada da sanya ’yan agaji a dukkanin kofofin shiga masallaci. Kofar da Wakilin ’yan uwan ke shigowa ma aka rufe ta, tare da sa masu tsaro a wurin.

Jama'a da dama a garin sun yi ta tambayar junan su, yadda suka ga ta ko'ina an jibge jami'an tsaro; kowace kwana, akalla motoci uku a wasu sassa na masallacin.

Dangane da wannan ne ya sanya Wakilin ’yan’uwa na garin ya tunatar da al'ummar garin da sauran al'umma kan cewa Harkar Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky Harka ce ta kiran mutane zuwa ga koyarwar addinin Musulunci, wadda kuma ta doru a kan ilimi da hankali, saboda haka kamar yadda al'umma suke a matsayin shaida, shekaru aru-aru mabiya Malam Zakzaky ba su taba tayar da wata fitina da kowa ba, kuma har yau ’yan’uwa biye suke a kan tarbiyyar da su Sayyid Zakzaky suka dora mabiyan su a kan ta.

“Bisa wadannan dalilai muna sanar da al'ummar Gashuwa tare da sauran al'umma baki daya kan cewa duk wata fitina da suka ga an tayar, to ba hannunmu a ciki, kuma muna nesanta kanmu da ita. Mun yi wannan ne bisa ga yadda muka lura da wasu da ke kokarin shige-da-fice daga cikin 'yan kwamitin masallaci da kuma ’yan agajin Nurul-Islam don ganin an auka wa ’yan’uwa na garin Gashuwa ta jihar Yobe. Kuma da zarar mun ga wani motsi, za mu bayyana sunayensu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso,” ya ce.

Yadda ’yan Sanda suka yi amfani da 'yan sara-suka a Kaduna

Daga Abdullahi Isah Wasagu

A ranar Lahadin 7/1/2018, jami'an 'Yan Sanda a garin Kaduna, bisa umurnin Gwamna Nasiru el-Rufa'i suka bude wuta da harsasai masu rai a kan 'yan'uwa musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, a lokacin da suke gabatar da muzaharar lumana ta kiran a saki Jagoransu Shaikh Zakzaky, wanda rundunar tsaro ke ci gaba da tsarewa bisa taka umurnin kotu.

An dauko muzaharar ne a daidai shataletalen Leventis da ke kan titin Ahmadu Bello Way, da misalin karfe 4:30 na yamma. Muzaharar ta ci gaba da tafiya cikin lumana.

Jim kadan bayan hawa kan titin Ibrahim Taiwo da ke yankin kasuwar Shaikh Abubakar Gumi, ba zato ba tsammani, kawai sai aka fara jin ruwan tiyagas daga ko'ina, daga nan sai harbe-harbe ya biyo baya da harsasai masu rai. Wani abin al'ajabi da jajircewa na 'yan'uwa shi ne, duk irin ruwan tiyagas da harbi da suke yi, sai da aka rufe muzaharar, wadda Hujjatul Islam Abdullahi Zango ya yi addu'a.

Bayan rufe muzaharar ne, wasu tsayayyun 'yan'uwa suka tare hanyar da 'Yan Sandan suke kokarin cimma goshin muzaharar. Sun yi ta barin wuta na tsawon mintoci 20, amma ba su sami kowa ba, kuma tsirarrun 'yan'uwan ko gezau, ba su gudu ba, illa wadanda suka yi sa'ar harba tun farkon bude wutar tasu.

Bayan sun samu tsawon lokaci suna harbi ne, can sai suka karo motoci da 'Yan Sanda dauke da muggan makamai da kuma 'yan sara-suka dauke da gorori da adduna.

Ganin yadda suka sauke motoci biyu na 'yan sara-suka, sai 'yan'uwa aka ida watsewa.

Bayan watsewar 'yan'uwa, kan ido Wakilinmu suka yi ta yawo a motoci tun daga kan Kano Road zuwa Ibrahim Taiwo zuwa Lagos street, suka yi ta harbi sama suna firgita al'umma. A yayin da a gefe guda kuma wasu al'umma ke tofa albarkacin bakinsu na irin wannan bakin zalunci na ci gaba da tsare Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Madrasatul Fudiyya Islamiyya Funtuwa ta yaye dalibai 93

Daga Awwal Jibril ’Yankara

A ranan Lahadi 4 ga Jimada Ula, 1439 (21/1/2018) ne, Madarasatul Fudiyya Islamiyya da ke Shuwaki Funtuwa a Jihar Katsina ta yi bikin yaye dalibai guda 93 karo na uku.

A lokacin wannan taro, Shaikh Abdullah Zango ne babban bako mai jawabi, inda ya jawo hankalin daliban da aka yi bikin yaye su da cewa, su sani akwai babban aiki a gabansu tunda yanzu suka fara sa tushe a rayuwarsu.

Sannan ya yi kira ga al’umma da su sani fa shi mai neman ilimi da Malami ba karamin daraja ke gare su ba, musamman ma wanda ya yi aiki da karatun.

Shaikh Abdullahi Zango ya ci gaba da cewa, wajibi ne mutum ya sani cewa ya zama wajibi yin aiki da gwargwadon abin ya samu na karatu. “Duk girman karatunka in ba ka gwagwarmaya, to tamkar kai gawa ne a cikin al’umma,” in ji shi.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Lajanar Fudiyoyi, Dakta Nura Azare, ya yi kira ga iyaye da su kara daurewa wajen daukar dawainiyar karatun yaransu.

Da yake nasa jawabin, Mukadashin Shugaban makarantar, Malam Nura Ibrahim, ya fadi takaitaccen tarihin makarantar da irin matsalolin da ta yi ta fuskata kafin samun wurin dindindin. Sai da aka yi ta yawo da ita wurare daban-daban har wuri shida kafin samun inda take yanzu.

Ya kuma bayyana dimbin nasarorin da makarantar ta samu wanda yanzu haka tana da sashe hudu, wanda kowane sashe ana karatu a cikinsa.

Da yake jawabin godiyya, Wakilin ’yan uwa na Funtuwa, Malam Rabi’u Abdullahi, ya gode wa wadanda suka amsa gayyatar da aka yi masu da wadanda suka ga gayyatar a ALMIZAN suka taho.

Wannan bikin dai na dalibai na shekara uku ne aka hade su waje guda sakamakon yanayoyi da aka yi ta shiga a Harka Islamiyya, sai a wannan karon aka samu yin bikin.

’Yan uwa da dama ne suka samu damar halartar bikin daga garuruwa da dama, irin su Mafara, Tsafe, ’Yankara, Faskari, Mairuwa, Malunfashi, Tudun Iya, Marabar Maska, Maska, Gangara, Sabuwa, Kaya, Bakori da sauransu.

An dai yi taron lafiya an tashi lafiya, wanda Shaikh Sulaiman Nadi Bamba Ghana ya bude shi da addu’a, yayin da Malam Sanusi Chikaji Zariya ya rufe shi da addu’a.

Kowace marhala akwai wakokin da suka dace

In ji Alhaji Mustafa Gadon Kaya

Daga Ibraheem El-Tafseer

“Kowace marhala akwai wakokin da suka dace.” Shaharraren mawakin Harkar Musulunci a Nijeriya, Alhaji Mustafa Umar Baba Gadon Kaya ne ya furta haka, a tattaunawarsa da Wakilinmu jim kadan da kammala taron Mu’utamar na mawakan Harka Islamiyya, wanda aka gudanar a garin Potiskum.

Alhaji Mustafa Gadon Kaya yace; “Manufar shirya irin wannan taron na Mu’utamar din Mawaka, asali muna shirya shi ne domin kara kwakkwafa tunanin su mawakan, da kuma ba da shawarwari a kan kasidun da ya kamata a yi a kowace marhala da kuma kowace munasaba.

“Saboda wani lokaci za ka ga ana yin wake din, amma ba su dace da munasabobin da ake ba. Sannan kuma ko da ma munasabar ce, ko halin da ake ciki, to ya kamata a rika lura da marhala, ba duka abin da ya zo bakin mutum ne yake fada a waka ba, ba kuma duka wake ake yi a kowane lokaci ba. Muna yin wannan ne domin kara ba da shawara da kuma saitawa domin yin wakokin da suka dace, suka kuma cancanta, shi ne makasudin shirya wannan taro”.

Ya kara da cewa; “Muna kai irin wadannan taruka yanki-yanki ne, saboda wani lokaci idan muka kira taron mawakan Harkar Musulunci na kasa gaba daya, saboda nisa wasu ba sa samu su halarta. Wannan shi ne ya sa muke kai shi yanki-yanki, saboda bukatar ita ce ta zama ana halarta din. Ka ga yanzu kamar zuwan mu nan, akwai wadanda duk tarukan baya ba su taba zuwa ba. Saboda wurin ya yi masu nisa, amma da aka zo nan kuma sun zo. Akwai fuskokin da ban taba gani sun je taron ba, amma yanzu sun zo. Idan mutane ba za su iya zuwa ba saboda wasu wahalhalu, to mu za mu iya zuwa mu kai sakon, domin ya zama fikirar tana tafiya tare, kuma tana tafiya yadda ya kamata. Mun saka ranar za a yi taro na gaba ne a yankin Kano.”

Alhaji Mustafa ya ce; “Shirya irin wannan taro yana ba da tasiri sosai ga mawaka da ma wadanda ba mawakan ba, saboda in dai muka je muka yi irin wannan taron, to za ka ga kasidun da za a rinka yi daga baya sun canza. Ka ga an samu gyara ke nan. An samu karin fikira da karin wayewa. Sannan kuma su ma ’yan uwa fahimtarsu da tunaninsu ga mawaka din yakan canza.

“Yanzu na tabbatar zaman da aka yi yau da ’yan uwa, bayan an gama zaman mawakan jiya, na san tunanin su ga mawakan ya canza. In da suna dauka abin harigido ne ko hayaniya ne, to lallai yanzu sun gane ba haka ba ne. Sannan mun ba ’yan uwa dama, suna da dama da za su ba da shawarwari da fadin abin da suka ga ya dace a yi”, Alhaji Mustafa Umar Baba Gadon Kaya.

An yi jana’izar Shahid Adamu Salisu Mallam Madori Daga Awwal Ashir

A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka gabatar da jana’izar Shahid Adamu Salisu a gidansa da ke unguwar Dunari a cikin garin Mallam Madori a Jihar Jigawa.

An gabatar da jana’'izar ne bayan kwashe kwanaki tara da yin shahada a sakamakon harbin sa da jami’an tsaro suka yi a yayin gudanar da Muzahar fafutikar neman a saki Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky a makon da ya gabata a Abuja.

Tun bayan waki’ar ne jami’an tsaro suka dauke shi, kuma suke ajiye da shi a Asibitin Gwagwalada, ba su ba da gawarsa ba sai a ranar Alhamis. Daga nan aka dauke shi zuwa Suleja, inda aka kintsa shi a can. A ranar Juma’a kuma aka kawo shi gida Mallam Madori aka yi masa sutura.

Jama’a da dama ne suka yi tururuwa zuwa jana’izar, ciki har da baki daga sassa daban-daban. Malam Yusuf Abdullahi da Malam Bashir Sabon Titi, Malam Ibrahim Kazimiyya, sun sami halarta daga Kano. Sidi Usman daga Guri da Malam Dauda Hadejia da kuma Malam Mansur Gumel duk sun halarta.

Babban Limamin unguwar ta Dunari ne ya yi masa Sallah. Harisawa ne suka dauki Shahid Adamu zuwa makwacinsa, sauran jama’a na biye.

A yayin da ake tafe da shi, masu raka shi kuwa sai salati ga Manzo da Iyalan Gidansa suke yi. A haka aka tafi har zuwa makabarta.

Wakilin ’yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky na garin Malam Ibrahim Umar ya gabatar da takaitaccen jawabi dangane da Shahid Adamu. Daga karshe kuma Sidi Usman Bin Rasheed ya rufe da addu’a.

Wakilin ’yan uwa na Kano, Dakta Sunusi Abdulkadir na cikin wadanda suka je garin Mallam Madori domin isar da ta’aziyyarsu ga iyalan Shahid Adamu Salisu. Ya yi jawabi mai ratsa jiki da kuma karin karfafa gwiwa.

Jama’a sun shaidi Shahid Adam da kyakkyawar mu’amala a harkokinsa, ga fadin gaskiya, mutum ne mai hikima da shashin tsoro.

Abokin tafiyarsa Abuja, Malam Ibrahim Waki’a ya shaida mana cewa tun ranar da za su tafi Marigayin ya yi ta yin wasu dabi’u da halaye irin na bankwana. Ya ce; “Akwai wasu almajirai duk lokacin da za mu yi wuce, Shahid Adamu sai ya ba su sadaka, to amma ranar da za mu tafi mun zo wurin ba su fito ba, har mun wuce mun dan yi nisa, sai ya ce ‘bari mu dawo mu ga ko sun fito, ka san sadakar nan ita take kare mu daga hadari.’ Haka muka dawo ba su fito ba muka juya muka tafi. Amma da muka je Hadejia sai da ya saya wa Almajirai abinci.”

Shi kuwa Ibrahim Adam, daya daga cikin wadanda suka wanke shi, ya bayyana mana cewa ya yi wasu mafarkai da Shahid din gab da shahadarsa, wanda a cikin mafarkin akwai maganar da Shahid din ya yi ta cewa ‘ni fa na sami rahama’.

Bayan nan ya kara da irin karamar da aka gani ga Shahid Adamu, duk da kwanaki takwas da ya yi da shahada, amma jini na zuba a jikinsa, ga kuma duk gabobinsa suna da laushi, kuma wuyansa kamar auduga saboda laushi. “Wani babban abin al’ajabi da ya fi jan hankalin duk wanda ya ga gawarsa shi ne irin gumin da ke fita daga jikinta, kai ka ce akwai numfashi a gare shi,” in ji Ibrahim Adam.

Marigayin dai ya yi shahada ya bar mata daya da ’ya’ya takwas. Kafin shahadarsa dan uwa ne mai kokari.

Ta fuskacin sana’a kuwa, ya kasance shahararre ne a harkar hada daro wato (satalayit), hatta ranar da zai yi shahada ma sai da ya seta tashar Alwilayah a masaukinsu da ke Suleja.

Sannan kuma Shahid Adamu Direba ne mai rijista a kungiyar NARTO. Ko bayan ya yi shahada ma an sami labarinsa ne a dalilin ID Card din kungiyar da yake dauke da shi.

Idan kana son sanin Shaikh Zakzaky ka nemi sanin Dan Fodiye -Malam Muhammad Adamu Abbari

Daga Muhammad Nasir

An bayyana cewa duk mai son sanin waye Shaikh Zakzaky, to ya nemi sanin Shehu Usman Dan Fodiye don duk abu daya suke kira a kai na dawo addinin Musulunci ya yi iko da mu.

Wannan jawabin ya fito ne daga bakin Wakilin ’yan uwa na Gombe, Malam Muhammad Adamu Abbari a lokacin da yake jawabin Mauludi a garin Kuri cikin Jihar Gombe.

Malam Abbari ya ci gaba da cewa, wannan shi ya sa ake zaluntar Shaikh Zakzaky don yana kira irin na Shehu Usman Dan Fodiye.

“Shaikh Zakzaky bai cuci kowa ba, bai batawa kowa, bai lalatawa kowa ba, ya rike gaskiya ne gwamnatin Nijeriya ke fada da shi, inda a ce ya bi gwamnati ana ta shan bidiri, da ka ji shiru babu abin da za a yi masa.

“Shaikh Zakzaky ba da Buhari yake fada ba, balle wasu su ce wai Musulmi ya hau kan mulki ka ji ’yan Shi’a suna ta tsinuwa da tashin hankali saboda ba dan uwansu Kirista ba ne a kan mulki. Ba Jonathan ya fara kashe ’ya’yan Sayyid Zakzaky ba a Azumin Ramadan rana tsaka a Zariya ba?” in ji Malamin.

Tun da farko dai sai da Malamin ya taya al'umma murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (S), wanda ya bayyana da cewa, shi ko da a ranar da aka haife shi dabbobi ba su je kiwo ba, don an haifi Annabi (S) da wani irin kamshi wanda ko da ka kori tumakinka kiwo za su dawo saboda kamshinsa (S).

Malamin ya kuma ce an haifi Annabi (S) da wani irin haske ba irin na sauran mutane ba, domin shi haskensa ko da ba wuta a daki, idan ya shigo cikin dakin zai haska dakin, za ka ga komai a dakin tamkar wutan lantarki.

Matasan Darikar Tijjaniyya sun nemi a saki Shaikh Zakzaky a Giade

Daga idris Ibrahim

A ranar Asabar din da ta gabata ne, gamayyar matasan Darikar Tijjaniya da suka kira kansu AHBABU RASULULLAH a garin Giade a Jihar Bauchi, suka gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna rashin amincewa da ci gaba da tsare Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda gwamnati ke tsare da shi ba tare da ya aikata laifin komai ba. Matasan, sun taru ne a babban filin wasan kwallo kafa da ke garin na Giade a yammacin ranar. Daga nan ne suka fara wannan jerin gwano don nuna rashin amincewar su da tsarewa da ake yi wa Shaikh Zakzaky.

Matasan, wadanda suka bi kusan manyan titunan garin na Giade suna rera wakokin kin amincewa da wannan tsarewa da ake wa Shaikh Zakzaky da maidakinsa, suna dauke da hotuna da kwalaye da aka rubuta ‘Free Zakzaky’.

Tunda farko matasan sun nemi hadin kan ’yan uwa dangane da abin da suka shirya, wanda suka kira shi zanga-zangar tausayawa da goyon baya ga Almajiran Shaikh Zakzaky. Sun sami gudummawar shawarwari daga Wakilin ’yan uwa na garin Giaden, Malam Ishaka Muhammad Sani.

Sun gudanar da zagayen cikin tsari da nutsuwa, cikin sahu suna rera taken ‘Free Zakzaky! Free Zakzaky!! Zagayen ya dauki hankalin jama’a, tare da sanya masu albarka, dangane da irin nuna rashin goyon baya ga zaluncin da ake yi wa ’yan uwansu Musulmi.

Da yake jawabin rufewa, Malam Abdulmumini Muhammad Bawa ya ce; “Tausaya wa ’yan uwanmu Musulmi, ba batun wane dan kaza ne, wane dan kaza ba ne. Duk Musulmi muke. Abin da ya shafi wancan, mu ma ya shafe mu, saboda addininmu daya, Ubangijinmu daya, Annabinmu daya.”

Malam Bawa ya ci gaba da cewa; “Don haka duk daya muke. Abin da ya same su, ya same mu. Mu ba ’yan Shi’a ne ba ne, ’yan Darika ne, amma tunda addinin Musulunci ya hada mu dole mu damu da abin da ya sami ’yan Shi’a. Don haka muna kira da gwamnati ta gaggauta sakin Shaikh Zakzaky ba tare da sharadi ba”.