AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

Rahoto

Daukaka kara ba ta hana zartar da hukuncin sakin Shaikh Zakzaky ba Cewar wani Alkalin kotun daukakaka kara


 UN

Mai Shari’a Muhammad Ibrahim Damaturu (Mun canza sunansa), Alkali ne da ke aiki a kotun daukaka kara (Court of Appeal) da ke Damataru ta Jihar Yobe. A cikin hirar da ya yi da Aliyu Saleh a makon nan, ya nuna mamakinsa a kan yadda har yanzu gwamnati ta ki bin umurnin kotu ta saki Shaikh Ibraheem Zakzaky. Ya bayyana cewa, da a wata kasar ce, da Alkalin-Alkalai da sauran masu rufa masa baya sun yi ritaya, sun bar aikinsu tunda gwamnati ta nuna ba su da amfani. ALMIZAN: Yallabai shekara daya ke nan da kotu ta yanke hukuncin a saki Shaikh Zakzaky, amma har yanzu gwamnati ba ta bi wannan umurnin ba. Ita tana cewa ta daukaka kara, amma kuma ba a fara sauraron karar ba; dama ana iya yin haka a shari’ance?

MAI SHARI’A: Da farko dai harkar shari’a wani abu ne da yake a bayyane, duniya ta sani, musamman wadanda suka kware a wannan bangaren. Kuma duk wani abu da ya shafi harkar shari’a ba kara-zube ake yi ba, akwai ka’idoji sosai. Idan mutum ya kai kara, aka saurare shi, ko Wakilinsa (Lauyansa), aka saurari Lauyan mai inkari, wato an saurari Lauyoyin bangarori biyu, zai zama fa daga lokacin da Alkalin ya ji bangarorin zai koma ne ya yi bincikensa, sai ya ce rana kaza ga watan kaza za ku zo ku saurari hukuncinku (judgment), ba tare da la’akari da wa zai ji dadi, ko zai ji haushin hukuncin ba, shi dai dole ya karanta.

Bayan nan zai ba da wasu adadin watanni, kamar watanni uku (ya danganta da kotun). Daga nan za a ci gaba da sauraron wanda wannan hukuncn da aka yanke bai yi masa dadi ba ya daukaka kara. A karkashin hukucnin da ya yanke zai rubuta cewa; “Duk wanda hukuncin nan bai yi masa dadi ba, ko bai yarda ba, yana da damar ya daukaka kara zuwa kotu ta gaba.”

ALMIZAN: Shaikh Zakzaky ya shigar da kara ne a Federal High Court, Abuja, wace kotu ce ta gaba, wacce ce za a kai wannan shari’ar, kuma wata nawa zai iya dauka kafin a fara sauraron karar?

MAI SHARI’A: Tunda dai Federal High Court ce, akwai Court Of Appeal a gabanta, ita ma in ta yanke hukunci za ta ce in ba a yarda ba a tafi Supreme Court, wato koton Allah ya isa! Daga nan dukkan abin da aka yanke shi ke nan.

ALMIZAN: Idan an kai maganar Court of Appeal, watanni nawa ake bukata don fara sauraron karar?

MAI SHARI’A: Ba a daukaka kara sai da dalilai. Ita wannan kotun ta farko in ta saurari shari’ar sai ta bayyana cewa abin da ta sani shi ne ta ba da damar a daukaka kara zuwa kotu ta gaba na wannan yankin, muna da su yanki-yanki, kamar wannan yankin namu na Jihar Yobe da sauransu ana ce mana Court of Appeal Jos. Daga lokacin da aka bayar, galiban bai wuce watanni uku. In har wata uku ya wuce, wannan yana nuna wanda aka yanke wa hukunci na cewa abin ya yi ba daidai ba ne, kamar ya yarda ke nan tunda bai daukaka kara ba.

In har watanni uku sun cika bai daukaka kara ba, kuma yana so ya daukaka din, akwai abin da ake kira ‘motion’, ma’anarsa shi ne dalilin jinkiri da ya sa ba ka daukaka karar ba, yanzu ka zo kana so a bude maka kofa, domin lokacin da aka yanke hukuncin nan bai maka dadi ba, ko ba ka da lafiya ka tafi ganin Likita, wato wani abu dai ya taso wanda ya cinye watanni uku ba ka samu dama ka tafi ba. Wannan din ma za ka dauki Lauya ne ya rubuta wannan ‘motion’ din ya shigar a gaban Alkali, idan sun yarda da wadannan dalilan naka sai su bude maka kofa, su ce sun gamsu da dalilan jinkirin, in ba su gamsu ba, a wajen za su ce dalilin jinkirin naka ba su wadatar ba.

ALMIZAN: A baya ka ce ba zai yiwu a daukaka kara ba, sai da abin da kuke kira dalilai, wadanne dalilai ne wadannan?

MAI SHARI’A: Gaskiyar magana Appeal ba a yin sa sai da dalilai, abin da ake kira da Turanci ‘Grounds of Appeal’. Idan ka je kotu za ka dauko daga ‘grounds one’, har zuwa 100 (in kana da su). Sai ka zayyano dalilan naka. Na farko za ka je kotun ce, ka ce hukuncin da ka yanke a kotu kaza, wanda kuma kotun ta ba mu damar in hukuncin bai yi mana dadi ba, mu taho nan. Daga nan zai fara zayyano dalilan da cewa da Alkalin da ya yanke hukuncin bai yi adalci ba, domin bai saurare mu ba sam-sam, bai saurari bangarenmu ba, bai bari mun kawo shedu ba. Bai ziyarci inda aka yi abin ba, ko kuma bai tura Wakilansa ba. Alkalin bai bar mu mun yi wa wanda ya kawo kara tambayoyi ba, kawai Alkali ya yi gaban kansa ne.

Da yake su Lauyoyi suna taimaka wa Alkali wajen yanke hukunci ne. Da Lauyan mai kara da wanda ake kara da Alkalin kansa, suna haduwa ne su fitar da hakkin mai hakki su ba shi hakkinsa. Za a taru ne a taimaki kasa da al’ummarta. In dai ba Lauya na son wahalar da masu shari’a da shari’ar ba, kana kawo masa ‘case’ yana dubawa zai fahimci inda gaskiyar take, domin abin da aka koya masa ke nan. Don in har an je kotu aka gamasar da kotu da shedu, kuma aka yanke hukunci, dole Lauyan ya mika wuya. Yin hakan zai taimaki gwamnati, domin an ajiye shari’a ne don a samar da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma. Duk Lauyan da ke da lasisin da zai iya tsaya wa ya wakilci kowa, in ya ga abin da ba daidai ba yana ba da shawara, ya fadi gaskiyar magana ga yadda take. Don haka da Lauyoyin da Alkalin Dodo daya suke yi wa tsafi.

Daga nan za a yi abin da ake kira ‘notice of appeal’, zai rubuta wasika guda biyu ya tura kotun farko da ta yanke hukunci, sai a ce masu su tattaro wadannan ‘record’ din a kawo wannan kotun ta gaba. Record din yana nufin tun daga ranar da shigar da karar har zuwa lokacin aka yanke hukuncin, duk bayanan da aka yi a kotu, tun daga A har zuwa Z, za a hado su a kai wa kotun gaba don ta duba. Dama kuma an rubuta ana ba su shafuka, don in an zo Appeal din a samu saukin kai wa ga bayanin da ake son samu.

Daga lokacin da ka kai wannan wasikar kamar kana sanar da kotun ne cewa ka daukaka kara, kuma ga takarda. Ita wannan takardar a ka’ida ya kamata ne a gan ta a duniya, ba da baki ake cewa an yi appeal ba. Za a zuba wannan record din a cikin file din da aka bude.

Idan an zo a ranar farko ta fara sauraron daukaka karar, za su zauna a gaban Alkali. Shi Lauyan wanda aka yi kara zai tashi ya yi bayanin cewa wannan Appeal ne wanda ya taso daga Federal High Court, muna da dalilan (Grounds of Appeal) daukaka kararmu kamar haka: Sai ya fara zayyano su. A karshe sai ya roki kotu da cewa; “bisa wadannan dalilan namu na daukaka kara muna rikon Alkali ya yi watsi da wannan hukuncin da Alkalin kasa ya yi.”

Ita kuma kotu bayan ta saurari dalilan, in ta rushe hukuncin, suna da damar su sake sauraron karar, ko kuma a sake mai da ku kotu da darajarta ke daidai da wancan da ya yanke hukuncin domin a sake sauraron karar, ko kuma Alkalin da ya yanke hukuncin a sake mai da masa shari’ar a ce ya sake nazarin hukuncin da ya yanke, don gyara kura-kuran da ya yi. Ko kuma ta tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke.

ALMIZAN: Akan ce in an yanke hukunci, ko da an daukaka kara, ba yana nufin ba za a aiwatar da hukuncin baya ba, musamman in ya shafi hakkin bil’adama?

MAI SHARI’A: Gaskiya ne. A doka in an yanke hunkunci, in dai abin da ya shafi dan’adamataka ne, ba ya hana a zartar da hukunci, ko da an daukaka kara. In ka ga an daukaka kara, kuma an hana zartar da hukunci, to sai abin da bai shafi hakkin dan’adam ba. Kamar misali gida, aka ce wannan gidan kotu ta mallaka maka, sai masu gidan suka yi Appeal, sai a dakatar, dole sai an zartar da hukuncin, za a zartar da hukuncin, in sun yi appeal a can sai su yi watsi da hukuncin, ko su tabbatar.

ALMIZAN: Idan ana tsare da mutum ba bisa ka’ida ba sai ya kai kara, sai kotu ta ce a sallame shi, idan gwamnati ta daukaka kara ba za a sake shi ba ke nan?

MAI SHARI’A: A ka’ida idan mutum ya shigar da kara cewa, an tsare shi ba bisa ka’ida ba, wajibi ne a sallame shi ko da kuwa an daukaka kara. Abin da aka sani in dai mutum ne, ko da an daukaka kara in dai an yake hukuncin a sake shi, dole a zartar da wannan hukuncin, in ya so daga baya kotun sama za ta iya sokewa, amma bayan an sake shi. Daukaka kara ba ta hana zartar da hukunci. Amma da wani gida ne, ko fili, ko mota, ko kuma duk wani abu da bai shafi ran dan’adam ba, hakkinsa ne yake so ya karba, sai Alkali ya zartar da hukunci, sai aka daukaka kara, za a dakatar sai an yanke hukunci.

ALMIZAN: Ita gwamnati tana cewa ta daukaka kara a kan al’amarin Shaikh Zakzaky duk da kuwa kotu ta ce a sallame shi, ga shi kuma bai da lafiya, amma har yanzu ba a sake shi ba bisa dogaro da cewa an daukaka kara?

MAI SHARI’A: Dogaro da cewa an daukaka kara ba zai hana zartar da hukunci ba. Kuma ai daukaka kara a bude yake, kowa yana iya sani, ko ba ka yi karatu ba in an daukaka kara za ka iya sani, za a iya ganin takardar. Yanzu ma harka ta zamani in an ba da notice of appeal din ma ana iya daukar sa a waya a haska kowa ya gani. Amma gaskiya maganar Sayyid Zakzaky, ba wata takarda da take cewa an daukaka kara, ba a fadi kotun da aka daukaka karar ba, ba a ba da ranar da za a zauna don sauraron daukaka karar ba. Sai dai kawai an fada da baki ne cewa an daukaka kara.

Gaskiyar magana tsare Sayyid Zakzaky da ake yi ya saba wa kowace irin doka ta duniya. Ana tsare da shi ne ba bisa ka’ida ba. Ana tsare da shi ne kawai bisa isa, mu muka yi dokokin, in mun karya su ba wani abu da zai faru! Domin mu ke da mulki. Mune muka yi doka, kuma mun karya ta!

Don haka gaskiya wannan abin da gwamnatin nan ta yi a kan tsare Shaikh Zakzky ya kamata Alkalin-Alkalai na Tarayya ya yi fushi ya yi ritaya, saboda an ci mutuncin Alkalai ne. Duk wani mutum da yake a layin shari’a, gwamnatin nan ta ci mutuncinsa. Kun rantsar da mu mu zo mu yi aiki, kuma mun yi aiki, kun ce ba za ku bi ba. Gaskiya kasar nan ba ta shirya bin dokokinta ba. Kowa yana karkashin doka ne, wanda zai ba da hukunci kuma Alkali ne, wanda zai ba da misalin aiwatar da hukuncin Shugaban kasa ne. A kasa ba wani mutum da in ya yi magana wajibi ne a saurare shi a tsarin doka na kasar nan kamar Alkali. Don haka in ya yi abin da ya kamata kuma aka ki zartarwa, sai Alkalin-Alkalan ya yi fushi ya bar masu aikinsu tunda ba a shirya karbar gaskiya ba. Wannan zai faru ne a kasar da suka san ’yancinsu ke nan, amma kamar a nan in ba za ka yi abin da gwamnati take so ba, ba za a yi da kai ba. Ba ka ga a Amurka wani karamin Alkalin wata kotu ne ya zartar da hukuncin dakatar da Shugaban kasar, Donald Trump a kan shirinsa na hana wasu kasashen Musulmi bakwai shigowa Amurka. Duk al’ummar da za ta bi doka, za ta ci gaba a rayuwarta.

ALMIZAN: Wane mataki ya kamata Lauyoyin ’yan uwa su dauka ke nan?

MAI SHARI’A: Da yake magana ce ta shari’a, kuma ana yin ta, an ci zarafin bil’adama, wajibi ne su ’yan uwa su ci gaba da wayar da kan jama’a a kan abin da aka yi da ya saba wa doka. Hatta Lauyoyin Harka suna da rawar da za su taka, ya kamata su nuna wa sauran Lauyoyin gari cewa, kar su dauka wannan abin da aka yi ya shafi wani bangare ne. Ana kokarin a rushe duk wata doka ne. Ya kamata su hada hannu waje guda don su ceto bangaren shari’a. Wannan abin da suka yi yana nuna a tsarin shari’a akwai dan lele, akwai wanda ya fi karfin doka. Idan kana zargn wani ya ki bin doka, kai ma kuma ba ka bi doka ba, kamar ka koya masa ne. Mutumin da ya fi dacewa ya girmama doka, shi ne Shugaban kasa saboda ya kiyaye darajar kasarsa, wadanda suka san abin da suke yi a sauran kasashen duniya za su yi masa kallon bai san abin da yake yi ba. Bai kamata kai ka ki bi ba, kai kuma ka zo ka sa wani ya bi. In dai kotu ne ta yanke hukunci, komai dacin abin, tilas ka zartar da shi.