AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. Bugu na 1284 ISSN 1595-4474


Rahoto

Zaben Buhari: Mai bata abinai ya bata (I)

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


Lokacin da aka kada gangar juyi daga soja zuwa farar hula, wasu daga cikin talawan Najeriya sun yi murna. Suna tsammanin adalci da rashin tursasa wa talaka zai ragu. Wai talaka zai wala, ya huta, ya sa ransa a inuwa, don mahaukata, gwanayen kisa, wadanda aka raba su da zama a cikin mutane sun koma dazuzzukan da suka dace da su, wato Bariki.

Ka san mahaukacin kare, kamar yadda daya daga cikin su, wato AVM Nura Imam ya kira su? Watakila mafi yawan mutane ba su san dalilin mai da soja cikin daji ba. Da sun karanta tarihin yadda Bature yake daukar mutum natsattse, mai tausayi da hankali a da, ya mai da shi dabbar da ba ta dace ta zauna da mutane ba, da fahimtar tambayata ba za ta yi wuyar amsawa ba.

Wajen koyon aikin soja, za a cire tausayi da kunya don a maye gurbinsu da rashin imani da kafirci. Ubangijinka shi ne babbanka a mukami. Komai ya ce ka aikata, dole ka aikata kawai, kar ka nemi dalili. In ka aiwatar, kana iya tambayar dalili. Wadannan mutane sune suka mulke mu na shekaru masu yawa a nan kasar. A lokacin mun ga kwamacala iri-iri, wasu ma alkalamin tarihi zai ji kunyar rubutawa.

An yi yakin kawar da soja daga kan karagar mulki. Amma wadanda suka yi aikin, sune masu fafutukar dawo da dimokaradiyya a cikin Yarabawa da kadan cikin ’yan kadan na ’yan Arewa da Ibo, hada da ’yan kudu maso kudu, kamar yadda ake kiran yankin da ke da arzikin man fetur, wato Neja-Delta.

Shakka babu Yarbawa sun ba da gudummawa sosai ta wannan janibi. Wani dalilin Yarabawa shi ne, kasuwarsu ta yi kasa, su ke da tarin lauyoyi, amma sojoji, sun mai da tsarin mulki cikin Mala, suna yadda suke so. Don haka ofisoshin lauyoyi sun bushe, sun yi karkaf kamar tsohuwar rijiya a sahara. Muna iya takaita magana a nan da cewa, an kori mahaukata daga mulki. Mahaukatan da bisa dabi’a ba a barinsu a inda mutane masu hankali suke zama. Don haka mafi yawa in ka ga Barikin soja a cikin gari, to gari ne ya same shi.

A kasashen da ake kira ci gababbu ta fuskacin watsi da addini da bautar ciki da biyayya ga duniya sau da kafa, ba ka ganin soja da kayan Sarki yana yawo a cikin gari. Ba ka sakin mahaukacin kare a cikin jama'a, ko da ka sawa karen chali, balle ba a sa wa kare chali. Ko ka sa masa chali, zai yi barna da faratunsa.

Na'am an kori soja zuwa bariki. Wannan da taimakon kasashen duniya, wadanda suke bukatar cimma muradinsu in haka ta samu. Ba za mu yi maganar muradunsu a nan ba. Akalla a yau. Sai da mu bude maganar abin da ya biyo bayan korar soja daga mulki a cikin kakin Soja. Tasirin soja yana da karfi a fagen siyasar Najeriya. Sun yi mulki na shekaru masu yawa, sun saci kudin al'umma, sun tsiyatar da ’yan siyasa fitattu. Ko da aka kada gangar siyasa su ke da kumbar susa. Dole suka nemo daya daga cikin su wanda suke da tabbacin zai rufa musu asiri, suka mara masa baya. Wannan shi ne Obasanjo. Ba ya bukatar a yi bayanin ko shi wane ne a nan.

Wannan kadan ke nan daga hanyoyi masu yawa da aka bi don kau da wadannan miyagu daga fadodin gwamnati. Ma’ana an dauko daya daga cikin su don karfafa mukin farar hula.

Idan mai karatu zai karanta littafin Shehu Shagari da ya rubuta shekaru bayan sojoji sun kifar da gwamnatinsa, za ka ji yadda sojoji a karkashin jagorancin su Janar Buhari suka yi ta shirya masa, da gwamnatinsa munafurci iri-iri. A shafi na 457 a cikin littafin Shagari na Turanci mai suna ‘Beckoned to serve,’ ya ba da labari, ko labarai masu sosa rai kwarai da gaske a kan Buhari da abokansa, ’yan siyasa a kakin soja. Ga daya daga ciki: "A watan Nuwamban 1983 na je Jos don yaye daliban makarantar kumbiya-kumbiya da dabarun mulki (NIPSS) da ke Kuru. Kamar yadda aka saba, Gwamnan farar hula na jihar ne ya tarye ni a filin jirgin sama. A lokacin da muke cikin mota a kan hanyarmu zuwa cikin garin Jos, sai ya ce mini yana da wata muhimmiyar magana da yake son ya yi da ni, kafin in koma Lagos. Da muka isa masauki, Gwamna ya ce mini ya samu wani labari na sirri, wanda ya shafi tsaron kasa daga matarsa, wacce take suruka ce ga wani babban Soja. Matar sojan, wacce take ’yar’uwa ce ga matar shi Gwamnan ta damu sosai yadda mijinta ya dingi dawowa gida da tsakar dare a wadannan lokuta.

“Da ta takura shi don neman dalilin haka, sai ya bayyana mata cewa suna shirya juyin-mulki ne. Amma kar ta fada wa kowa. Amma duk da haka ta ga ya dace ta bai wa ’yar'uwarta, matar Gwamna wannan labari, don su san yadda za su tunkari wannan abu mai cike da hadari. Cif Lar ya ce mini ya so ya yi magana da Janar Buhari a kan wannan labarin tunda shi Buhari memba ne a Kwamitin tsaro na jihar, don kasancewarsa GOC na babban Barikin Soja da ake kira Runduna ta uku da ke Jos. Amma yana so ya nemi shawarata kafin ya tuntube shi. Dangane da haka na umurce shi da ya yi magana da GOC. Na kuma ce ko zai fadada bincike a kan maganar bisa taka-tsantsan. Gwamna ya amince amma bisa sharadin cewa zan sanar da Janar Buhari kafin in bar Jos cewa shi (Solomon) zai gan shi don su tattauna wani abu. Haka na yi kafin in bar filin jirgin saman Jos, bayan an gama bikin rakiya."

Akwai wani abu muhimmi da ya kamata mu duba game da wannan maganar. Kamar yadda Shagari ya ce, bayan ya aiki Solomon Lar gun Buhari. Ya ce, "Buhari ya nuna mamakinsa kwarai da gaske da abin da Gwamna ya fada masa. Nan take ya kira Shugaban Hukumar tsaron kasa ta farin kaya, NSO, Umaru Shinkafi a waya, yana neman su hadu a Kaduna cikin gaggawa. Shinkafi ya sanar da ni, ni kuma na ba shi izinin ya je su sadu. Da ya dawo (Shinkafi) daga Kaduna, ya ce mini Buhari ya yi barazanar zai yi murabus daga aikin soja domin babban Kwamandan Askarawa bai aminta da shi ba. Nan Shinkafi ya ce masa in da Shugaba (Shagari) bai yarda da shi ba, da bai aiko Gwamna wurinsa ba."

Da wannan labarin abin da ya faru tsakanin Buhari da Shagari, ban yi mamakin abin da Buhari ya yi bayan kisan kare dangin Zariya ba, lokacin da dan jarida Mannir Dan Ali ya tambaye shi kan abin da aka yi mana a Zariya, sai ya yi kamar a lokacin yake jin labarin. Kamar bai ma san an yi haka ba. Hali zanen dutse!

Duk da abin da ya fada wa Shagari ta hanyar Shinkafi, wane ne ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da Shagari? Wane ne ya jagoranci rusa gwamnatin da jama'a suka zaba? Wane ne ya yi ta daure mutane shekaru dari da abin da ya fi haka? Daurin da Sabo Bakin Zuwo ya kira daurin Aljanu.

Wane ne wanda wadanda ke aiki da shi suka yi duk abin da suka ga dama, babu abin da aka yi musu? Shakka babu shi ne Buhari. Kama daga kama makudan kudade a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagos, zuwa karya dokar da Mataimakinsa Janar Abdulbaki Baba Tunde Idiagbon ya yi na tafiya aikin Hajji da dansa karami bayan dokar da gwamnatin Buhari ta kafa ta hana haka. Da mujallar Newswatch ta tambaye shi cewa, me ya sa na kasa da shi ke karya doka ba a yi musu komai? Sai suka kawo misali da abin da Idiagbon ya yi, na tafiya da karamin dansa aikin Hajji. Amsar da gogan naka ya ba da ita ce, "wannan ne kawai ya dame ku, ku ’yan jarida?" Tabas da wani ne ya yi haka, watakila da an daure shi shekaru masu yawa. Buhari ke nan. Wanda ke neman saka Buhari a ma'aunin dattaku ko mai gaskiya, ya nemi littafin Tarihin Shehu Shagari, wanda aka rubuta da Hausa; zai ga sojojin da aka yi wa lakabi da,"Yan siyasa a rigar soja." Zai fahimci wane ne Buhari da abokansa. Zai ga yadda suka ci amanar kasa, ta hanyar makirci da kutungwila da abin da dattawan kirki ba sa yi.

Bari mu dawo maganar soja bayan an kora su Bariki. Na je Katsina lokacin aurar da ’yar Shugaban kasa Umar ’Yar'aduwa, na sauka a wani otel da ake kira Liyafa. Fitowata daga daki ke da wuya, sai na ga wani tsohon Janar mai ritaya, wanda ya yi Gwamna a Katsina lokacin yana Kanar. Ina gaishe shi, sai ya ambaci sunana, ya ce, "Ku farar hula ku ke jin dadi mulki ya koma hannunku. Ba abin da za mu ce. Watakila bai ji dadin irin tarbar da aka yi masa ba. Ga shi tsohon Gwamna, amma aka kawo shi otal maimakon gidan gwamnati. Ya fada mini haka yana murmushi, amma ta ciki na ciki. Shi wannan sojan ya yi Gwamna a jihohi biyu. Bayan haka ya koma fadar Abuja, sai da tasu ta hadasu da ’yan uwansa aka yi masa ritaya. Ko da aka dawo mulkin farar hula na sha ganinsa gidan manya ya kai gwauro, ya kai mari don neman mukami. Ya yi kokari matuka don zama Sanata, abin ya ci tura.

Duk da cewa masu murda akalar kasar nan daga waje sun kawo Obasanjo don sojojin da suka koma Bariki su fahimci har yanzu suna nan, ba a rabu da Bukar ba, kamar yadda Janar Ishaya Bamaiyi ya fada a sabon littafin tarihinsa da ya fito kwanan nan. Wadannan sojoji da aka kira "’Yan siyasa a rigar soja,” sune suka yi ruwa da tsaki wajen dora Obasanjo a karagar mulki. A tunaninsu zai bai wa daya daga cikin su mulki in ya yi shekara hudu. Shi kuma ya nuna musu ba ran salla kadai ake ado ba. Nan take ya yi watsi da alkawarin da ya yi da su, bayan ya tabbatar madafun iko sun shiga hannunsa. Obasanjo da ya ji dadin damben sai da ya sa kafa, ya nemi zarcewa a karo na uku.

Da zarcewa a karo na uku ya gagara, sai ya dauko wanda ba soja ba, amma wanda ya ci gajiyar soja, kuma kanin Mataimakinsa a lokacin da ya yi muki da kayan sarki, wato Janar Shehu ’Yar'aduwa. Ya kawo Umaru ’Yar'aduwa don abu biyu. Na farko ba ya so wani soja ya yi suna irin nasa. Ma'ana sojan da zai fi shi tsawon shekarun mulki. Na biyu zai samu duk wani rufin asiri daga kaninsa Umaru.

Babban tsaiko kan dauko Umaru shi ne rashin lafiyar Umaru. Nan ma ya nemi magani tun ba a yi nisa ba. Shi ne dauko wani daga cikin kananan kabilun da ba su taba mafarkin samun shugabancin kasar nan ba. Ko cikin nasu, sai da ya nemi dan bi-tsami, wanda bai san inda aka fuskanta ba, wato Jonathan Ebele Goodluck.

Haka dai abin ya yi ta gudana har guguwar fitowar Buhari siyasa. Ka san wanda ya saba da gidan Gwamnati, abin kamar wasa har ya zama gaskiya. A yau dai shi ne Shugaban Najeriya. Ya nema har sau hudu. Ka san wanda ya saba zama a fada, in ka kai shi Tsangaya, dole ya dawo, ko da ka daure shi a Malwa. Duk da cewa Buhari ya yi shelar daina siyasa, kowa ya shaida, amma alkawari ba komai ba ne a gun wanda ya saba karya shi. “Ranar biyan bukata, rayuwa ba ta da amfani,” in ji kuda.

Shi Buhari ba za ka ce, gwarzo ne a cikin sojoji ba. Shi yana cikin wadanda za ka kira cokali a sa ka a dadi. Ya rike mukamin Gwamna, ya rike mukamin Minista, ya rike mukamin GOC a Bariki. Duk mukamai ne na siyasa. Da ya bar wadannan mukamai da na ambata a sama banda GOC, sai ya kuduri aniyar tabbatar da burinsa na karshe, shi ne ya shiga Barikin Dodon a matsayin Shugaban kasa, kuma babban Kwamandan askarawan Najeria. Ya je yakin Basasa a matsayin karamin Soja. Kuma an ji sunansa a matsalar Chadi, wacce ta ja hankalin Najeriya har Najeriya ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Amma bayan wannan duk rayuwarsa ta soja a gidan gwamnati ce.

Ba kamar irin su Janar Maman Shuwa, ko Birgediya Benjamin Adekunle ba ne, wadanda za ka kira bayin kakin soja. Ba abin da suka sani, sai in daji ya baci, su je gyara. Tunda ya rike duk mukamen gwamnati, abin da yake nema bakin rai, bakin fama shi ne shugabancin kasa. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa, ’yan siyasa a kakin soja dawowa mulki ta hanyar cin amanar kasa.

Buhari ya jagoranci, hambare Shagari, kar kace an hambare, aka kira shi. Da ya ki karba mana in ba ya so? Yammacin duniya suna da irin wadannan Sojoji masu tsananin kwadayin mulki a duk kasashe masu tasowa. Don haka suka rika gindaya musu wasu ka'idodi na kasashensu a matsayin ladan da za su biya don kau da kai ga zalunci, kama-karya da wawushe dukiyoyin kasashensu.

Masana’antar Tama da karafa ta Ajoakuta ta isa babbar misali. An yi kashi saba'in cikin dari na wannan jan aikin a zamanin Shagari, da Turawan yamma suka ga haka, sai suka dauki matakin gaggawa wajen tsayar da aikin. Matakin shi ne amfani da ’yan siyasa a kakin soja don hambarar da gwamnatin Shagari. Turawan yamma suka bai wa su Buhari duk goyon bayan da suke bukata don ruguza tattalin arzikin kasar nan, wanda a karshe su Turawan ne za su amfana da hakan.

Lokacin da sojoji suka dandani dadin mulki, sai suka rika munafurtar junansu, da dayansu ya ga bai samu mukamin da ya dace a cikin wannan gwamnati ba, sai ya nemi hanyar kifar da gwamnatin da ke ci, don kafa tasu. Haka abin ya yi ta tafiya daga Ironsi zuwa Abacha. Janar Abdusalami ya tsinci dami a kala ne. Ko can baya cikin ’yan siyasa a cikin kakin soja, duk da yake, an fara jawo shi kusa don ya sami rabonsa, amma dama ta samu gare shi lokacin da Janar Abacha ya murmure.