AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. Bugu na 1284 ISSN 1595-4474

Rahoto

BUKATAR GAGARUMIN SAUYI A: BIYAN HAKKIN SHUHADA!

Daga Danjuma Katsina


 mallam

Da sunan Allah Madaukaki da ke fada a littafinSa mai tsarki;“Ka da ka tsammaci wadanda aka kashe a tafarkin Allah matattu ne, a’a, rayayyu ne a wurin Ubangijinsu ana azurta su.Suna farin ciki da abinda Allah Ya ba su daga falalarSa, kuma suna albishir ga wadanda ba su riske su daga bayansu ba cewa ba tsoro gare su, kuma ba za su yi bakin ciki ba”K3:169-170.

Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabin rahma, Manzo Muhammad (S) da Alayensa Tsarkaka.

Na so rubuta wani abu akan wannan maudhu'i tun watannin baya. Sai dai hakan bai yiwu ba sai yanzu makwanni kadan kafin Yaumus Shuhada, 1438 H. Kafa Mu'assasatus Shuhada da Shaikh Ibraheem el-Zakzaky (H) ya yi shekaru 25 da suka gabata ba ya rasa nasaba da matukar hangen nesa da kasancewar Harkar ta Allah wadda jarrabawowin da suka samu managartan magabata za su samu ba makawa. Bisa tsari, ayyukan Cibiyar sun hada da; kula da bukatun rayuwar iyalan Shahidai na yau da kullum; tabbatar da cikakkiyar tarbiyyar Musulunci da ilmantar da ’ya’yan Shahidan a dukkan matakai da jibintar sauran al’amuran da suka shafi iyalan masu albarka gaba daya.

Tun bayan kisan kiyashin gwamnatin Buhari na Disambar 2015 a Zariya da wadanda suka biyo baya a garuruwan Kano, Kaduna, Katsina, Plateau da sauransu, kididdigar Cibiyar a halin yanzu ta nuna akwai Shahidai kimanin 1000 da suka bar ’ya’ya kusan 2,200 da mata da sashin iyaye masu rauni fiye da 1,500. Baya ga bukatun rayuwa na yau da kullum da ’yan uwa ke dauka bisa tsarin Cibiyar, babban nauyin da take dauka shi ne dawainiyar karatun ’ya’yan Shahidai inda takan kashe kusan Naira miliyan takwas a kowane zangon karatu!

Akwai kuma dimbin matsalolin lafiya da suka shafi iyalan da ma na haya ga sashin Shahidai wadanda duka dai na kan Cibiyar. Babu shakka wannan babban kule ne ga wannan Cibiya da ayyukanta ke fadada a kullum.

Bayan tsarawa Cibiyar ayyuka, Shaikh (H) ya shata mata hanyoyin samun kudade don gudanar da su. Hakkin Shuhada ne mafi muhimmanci wanda wani dan mikidari ne da ake neman kowane dan uwa da 'yar uwa su bayar mai kimar N100= a wata ko N1200= kacal a shekara.

A fili yake cewa wannan tsari na da kyau da matukar sauki. Sai dai abin takaicin shi ne yadda hadin kai da goyon bayan 'yan uwa ya wuyata a wannan aiki mai matukar muhimmanci. Gaskiyar lamari mafi yawan 'yan uwa ba sa biyan hakkin duk da jaddada bukatar hakan da ma bayarwa a aikace da Shaikh din (H) ke yi don karantarwa a ranakun Shuhada. Kowa ya san yadda yakan bayyana hakkokin Shahidai biyu manya na kudi don kula da iyalansu da yi musu addu'a, inda yakan ba da nasa da na iyalansa, mai kauri har ya kan sanar da sigar addu'ar da yake yi masu! Sai dai duk da 'yan uwa na da yawa, amma hakan ba ya bayyana a hakkin.

Alkaluman Cibiyar na 2014 sun nuna Naira miliyan 51 kacal aka tara har da azuzuwan musamman masu daraja da sashin 'yan uwa suka shiga. Wannan alkalami ya nuna mutum 42,500= (dubu arba'in da biyu da dari biyar kacal ne suka biya) kenan. Kuma karin damuwar ma shi ne alkalamin ya sauka ne bayan waki'ar 2015 maimakon ya nunnunka. Inda 'yan uwa miliyan daya na biyan Naira darin, da za a dinga hada miliyan dari da ashirin duk wata cikin sauki!

BABBAN KULEN DA KE GABAN MU'ASSASAH

Gaskiyar lamari, lokaci ya wuce da dan uwa zai yi sake wajen ba da hakkinsa da na iyalai baki daya. Don me muke sakaci wajen ba da wannan muhimmin hakki mai girma? Hakkin na da yawa ne? Ko ko ba a hore mana abin bayarwar ne ba? Katin waya nawa muke sawa a kullum? Kuma me ye kimar N1,200= a tsawon shekara? Ba bu shakka mai abin Ya hore mana, karewa ma banda namu da iyalai da yawanmu na da damar shiga aji na musamman sai in ba mu yi niyya ba. Kuma yana da kyau mu gane cewa duk abin da muke yi natijar dai kanmu za ta dawo.

A zahiri mafi girman kulen yana kan Wakilan 'yan uwa wadanda iyaye ne, kuma murshidai gwargwadon hali a cikin su. Za mu iya tuna gagarumin sauyin da aka samu a yankin Kano shekaru biyu baya sakamakon matakin da Shaikh Shahid Muhammad Turi (Allah Ya kara masa kusanci) ya yi, inda yankin ya koma na daya daga na uku da tazarar miliyoyi tsakaninsa da na biyu! Muna iya ganin irin wannan kira da Shaikh Yakub Yahya ke ta yi a halin yanzu. Don haka akwai bukatar Wakilai su kalli gazawar nan daga janibinsu ta yadda kowannensu zai zama dakarin wannan aiki a fagen da yake. Wannan kam ba ma a hakkin Shuhada kawai ba, har ma a dukkan muradan Harkar Musulunci.

Su kuwa Wakilan Cibiyar da ke aiki cikin kulawarsu da ma Wakilan sassa kamar Harisawa, Matasa, 'yan uwa mata, ISMA, AFIMN, RF, Sharifai da dai sauransu na da bukatar tallafawa aikin gadan-gadan ta fuskar wayar da kai, fadakarwa, zaburarwa da kula da amanar wannan muhimmin aiki cikin gaskiya, iklasi, hakuri da jajircewa. Kuma akwai bukatar auna rawar da ake takawa da natijar da ake samu don sauya salo in bukatar hakan ta zama dole.

BUKATAR ZAGE DAMTSE DON KAIWA GA NATIJA

Ko ba komai tsayawa da dukkan bukatun rayuwar iyalan Shahidanmu masu girma wajibi ne. Ballantana ma akwai dimbin falala wajen musharaka a hidimar. Ya zo a Hadeethul Kudsi; “Ni ne Halifan Shahidi a cikin iyalinsa”. Kun ga mai musharaka a wannan aiki Allah Ya sanya shi cikin wadanda yake amfani da su wajen hakkakar da muradansa. Imam Khome’ini (KS) ya ce;“Shahada babbar falala ce gare mu. Saboda kumajin neman shahada ne da azamar sadaukarwa al'ummar da ba komai a hannunta ta yi galaba akan Dawagitai”. Ya kuma tabbatar da gwaggwaban lada da fifikon hidimar Shahidai akan sauran hidimomi wajen karfafa gwiwar irin wannan babban aikin lada a Jamhuriyar Musulunci ta Iran da ma wanda masu fafutika musamman na Hizbullah ke yi a Lebanon.

Domin neman albarka Mu’assasah ta nasabta tsarin yankuna da manyan managartan bayin Allah da Ya karrama da matsayin Shahada kamar Imam Bakir (AS) -Zariya da kewaye, Sayyidus Shuhada, Imam Husain (AS) -Kano da kewaye, Shahid Hamza (RA) - Katsina da kewaye, Shahid Ja’afar (AS) -Bauchi da kewaye, Shahid Ammar (RA) -Jos da kewaye, Shaheedah Sumayyah (RA)-Sakkwato da kewaye da Shahid Abbas Musawy (RA) -Potiskum da kewaye.

Kuma bisa al’ada, an saba gabatar da musabaka a tsakanin wadannan yankuna ta fuskoki daban-daban wanda har yanzu kuma ba a sauya ba.

Shin mai karatu ko ka/kin biya wannan hakki ko ko ka/ki na cikin lisssafin masu niyya a yayin da makwanni suka rage ga Yaumus Shuhada? Anya talbiyyarka/ki ga Shaikh (H) da gaske ne? Ko ko cika wuri ake wanda ba ma fata.Wannan dai tunatarwa ce kuma mafi kyawunta Malam ya dade yana mana a baya.

Biyan wannan hakki ko ba da gudummawar kudade na iya kasancewa a kowane lokaci ta Asusun ajiyar cibiya ko amintattun Wakilanta na manyan garuruwa.

Da fatan ’yan uwa za su tashi tsaye su jajirce domin kawo gagarumin sauyi a 'yan makwannin da suka rage. Allah Ya ji kan wanda Ya amsa kiran Shaikh (H) ya yi aiki na nasihohinsa masu albarka!