AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474


Rahoto

Kaduna tsohuwar Jiha da sabon Gwamna

TARE DA M.I. GAMAWA 09071965492


>

Kaduna, kamar yadda tarihi ya nuna, ta samu sunanta daga Kada. Jam'in kada, kamar yadda aka ji daga bakunan Gwarawa shi ne kadduna. Amma Hausawan ainihi ba haka suke kiran jam'in kada ba. Kama-kama har Mai gajeren wando, Bature, ya zo ya sake bata Hausar zuwa Kaduna.

Ala ayyi halin, ALKALAMI ba darasin Hausa zai koyar a nan ba. Sai dai zai yi magana a kan yaro man kaza. Kana iya kiran sa sabon mutum, wanda ya jihilci duniya da yadda take juyawa. In ta ga dama ta mai da Akawu kuku, ko ta mai da kuku Akawu. Duk halinta ne.

Ta ba ka dama a yau, gobe ta kwace damar. Ka zama mai fada-a-ji a yau, gobe ka jira wani ya fada, kamar yadda wani ne ya fada shekaran jiya. Jiya ba taka bace. Yau, ta zama taka, gobe ta zama ta wani. Haka abin yake. Da zarar mai jiran gado ya hau gadon mulki, to ya sani daga ran nan za a fara jiran sa kamar yadda ya jira.

Ba wanda ya san Sarkin karshe, kamar yadda babu wanda ya san Gwamnan karshe a kowace jiha, har da jihar Kaduna. In an ce ka nuna tsuhuwar jiha a Arewacin Najeriya, shakka babu, dole ka ce Kaduna. Kaduna ta yi shugabanni kama daga Gwamna Lugga, zuwa mafi kaskancin tunani da rashin basira a cikin su, wato Nasiru.

Kaduna ta zama abin alfahari ga ’yan Boko, wadanda Arewanci ya yi wa tasiri a zukatansu. Nan ne gida a gare su, kuma cibiyar fitsarar da Bature ya kawo. In kana neman garin da ya yi kama da Lardin Najadu a yanki da Shehu Mujaddadi ya yi jihadi, to Kaduna ke nan. Nan aka yaye zaratan da aka yi wa hukumar Musulunci da Shehu ya kafa bugun karshe. Nan ne tushen fitsara a Biladil Hausa bayan jihadi. In kana neman Bariki, inda kowa ke abin da ya ga dama a kasar Hausa, garzaya Kaduna.

Abin bai tsaya a nan ba, Kaduna ta zama matattarar Malaman fada, wadanda aka ce gara Shaidan da su. A lokacin Turawa, duk wanda aka wanke masa kwakwalwa, to Kaduna ce wajen zamansa. An samu kowa a Kadunan wancan lokacin banda wadanda ke neman dawowar abin da Shehu ya koyar. 'Yan Kadunan wancan lokacin sabbin mutane ne, wadanda Bature ya koya musu irin tasa rayuwar, don su koyawa na baya. Garin da Bature ya yi fitsararsa, iya iyawarsa don tabbatar da kafircinsa a Biladil Hausa ko Biladis Sudan; duk sunan na iya zama daidai.

Lokacin da Lugard ya bar Lokoja, babu inda ya hara sai Kaduna, domin iyayengidansa su ji dadin mulkar wadanda suka ci da yaki. Kafin a ankara Kaduna ta zama cibiyar Gwamnatin abin da ake cewa Arewa ayau. Daga Sakkwato zuwa Maiduguri. Ta gefe daya kuma har Kogin Kwara. Kaduna gari ke nan ta wannan janibi.

Sai wadanda suka mulki Kaduna. An samu Birai an samu Aladu kuma an samu beraye duk a hali. An samu Kulba, an samu kadangare. Masu tausayi sun karanta, duk daga cikin wadanda suka mulki Kaduna. Mugga sun yawaita. Masu kaki sun mulki Kaduna, farar hula sun mulke ta. Wasu sun kunna wutar fitina. Wasu sun tsagaita ta. Amma babu wanda ya kashe wutar fitinar gaba dayanta. Turawa sun kirkiri Kaduna don biyan bukatarsu, to mene ne hikimar mai da Kaduna alkibla bayan tafiyar Bature?

Dalili shi ne don ci gaba da abin da Bature ya fara. Bature ya kawo fitsara da lalacewa, hada da yanke zumunci da ninanci. Son juna da tausayi suka fara sukurkucewa. Gimshikan addinin Musulunci suka raunana a zukatan musulmi, imma ba a ce sun fita daga zukatansu gaba daya ba.

Amana ta yi karanci. Gubar maguzancin Bature ta bulla a Kaduna, ta yi naso zuwa duk garuruwan Arewa a cikin shekarun da ba su kai dari ba. Kama-kama, Kaduna ta koma jihar Kadunawa, sabanin yadda take a jamhuriya ta farko. Ta rasa babban suna, wato hedikwatar Arewa zuwa hedikwatar jihar Kaduna. Tun wancan lokaci haka abin yake har yau.

In za mu gajerta labari mai tsawo, za mu iya kiran Kaduna hanjin jimina. Akwai na ci, akwai na zubarwa; akwai na bai wa ’ya’yan banza. Haka ta kasance ne sakamakon hada mutane masu tarin yawa da Kaduna ta yi a lokacin da take hedikwatar jihohin Arewa baki daya. Duk da an mai da Kaduna jiha don Kadunawa, amma an bar baya da kura. Tunda dokar kasa ta bai wa kowane dan Najeriya damar zama a inda ya zaba, don haka Kaduna ta zama tamkar kogi, wanda ya tara haram da halal, mai tsafta da kazami, mai tausayi da maketaci, mai hakuri da marar hakuri. Wannan abin da aka samu a Kaduna ke nan. Zaman Kaduna a matsayin garin da ke iko da duk fadin Arewa ya bai wa Kaduna damar tara kowace kabila daga cikin kabilun kasar nan.

Tunda an sami mutane zaune karkashin wadanda Bature ya bai wa irin tasa tarbiyya da tsarin rayuwa, to dole a samu wasu dabi'u da suka dace da irin wadannan mutane. Dabi'un sune zaman ’yanci, kowa ya yi abin da ya ga dama. Don haka Kaduna ta zama Bariki. Inda za ka yi abin da ya saba wa addinin Musulunci ba tare da tsangwama ko fargabar wani ba. Amma ba'a hana gina masallatai da tsangayoyi ba.

Akwai addini, amma an manta da al'adar addinin. Za a yi salla, amma za a rayu karkashin dokar wanin Allah sabanin abin da aka gada daga jihadin Shehu Usmanu Mujaddadi. Wannan shi ne abin da Kaduna ta ginu a kansa, kuma ta watsa wannan gubar a duk fadin Arewacin kasar nan.

A kan wannan akidar Bature aka samu Maluma na daban, wadanda a cikin karantarwarsu babu bara'a balle wila'a. Wilayarka ita ce ka bi shugabanni a duk halin da suke. Sun ginu ne a kan Addini ko waninsa.

Maganar dai na da tsawo. Tafiya ta yi tafiya, zamani ya kawo Nasiru Elrufa’i. Wada mai dogon buri, kamar yadda Obasanjo ya kira shi. Nasiru mutum ne mai neman duniya, kamar ba zai mutu ba. Don ita ya sani. Bai san waninta ba. Duk karfinsa da basirarsa hada da fikirarsa suna masa aiki don taimaka masa ya biya bukatarsa ta duniya ce kawai. A gunsa lahira labari ne, wanda ba dole ya zama hakika ba. Wa yaje ya dawo? Addini wargi ne kawai.

Amma zai yi, don biyan bukatarsa ta siyasa. Ko ba komai addini na da wadanda za su ba shi kuri’a. Tun yana gararamba daga ofis zuwa wani ofis, har Allah ya yi masa gyadar dogo ya zama yaro abokin manya. Daga nan ya fi mai kora shafawa wajen neman duniya. Da bukata ta biya, sai halinsa na ainihi ya bayyana ga kowa.

Babu wanda mutuncinsa ko jininsa ya yi masa tsada, in har mutunci ko rayuwar wannan mutumin sun tare masa hanyar cimma burinsa na neman duniya. Babu girmama babba ko tausayawa yaro a cikin lissafinsa. Wajen raba mutum da duniya kuwa, babu mace, babu tsoho ko tsohuwa, madamar bukatarsa ta siyasa za ta biya. Kai hatta wadanda suka taimake shi, sai da ya ci mutuncin wadanda cin mutuncin kawai zai iya. Wasu kuma ya zama sanadin zuwansu lahira. Marigayi Mai shari’a Sambo ya isa babban misali.

Guguwar canji ta taso har ta kada Nasiru cikin gidan Sir Kashim a Kaduna. Ba a matsayin mai sharan ofis ba, a matsayin Gwamna mai wukar yanka. Ga fili ga mai Doki. Ko in ce mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura. Zamansa Gwamna ya fi kama da, zani ta tad da mu je mu. Ga mulki, ga girman kai, ga mugunta, ga munafurci kamar Maisangon Magana jari. Ga fid da rai daga rahamar Allah kamar Shaidan. Duk abin da Allah ba ya so wannan Wada ya tara shi.

Tabbas! Kaduna ba za ta ji ta da mai irin wannan hali ba. Dama tsautsayi ya zo da shi. Kuma kaddara za ta mai da shi inda ya fito. Ya shiga Kaduna da kafar hagu, zai kuma fita da ita. Aikinsa na farkon shigarsa gidan Sir Kashim shi ne wahalar da ma'aikata. Sai kisa, abin da ya fi kwarewa a kai, wato makirci a kan Sayyid Zakzaky da mabiyansa. Inda ya sa aka yi rashin mutum sama da dubu. Kana ya rusa duk abin da ke da alaka da Sayyid Zakzaky.

Bayan haka ya je ya binne wadanda ya sa Ubangidansa Buhari dan London ya kashe ta hanyar karensu Buratai a Mandon Kaduna. Yana gama wannan abin kunya, sai Kudancin Kaduna, inda ake zargin ya biya makasan da suka kashe musu mutum kusan dubu. Bai yi nadama ba. Kisan Zariya, alwashi ya yi na gurfanar da Sayyid Zakzaky a gaban kotu, bayan wannan aikin dabbancin da ya yi wa Sayyid. Kudancin Kaduna kuwa, cewa ya yi ya biya makasan ladan kisa. Ma'aikata cewa ya yi ba zai biya su guminsu ba, sai ya gama abin da ya sa a gaba, wai tantance ma'aikata. Wannan shi ne aikin sabon Gwamna.

Zuwan Nasiru ya jawo samun marayu da gwagware fiye da dubu goma a karamin takdiri a jihar Kaduna. Ba abin da Kaduna suka samu da zuwansa, sai kisa da yunwatarwa. Musulminsu da kiristansu. In ma akwai wadanda yake saurara ma sune Wahabiyawa makiya Allah da Manzanninsa, wadanda ko wanda bai yarda da samuwar Allah ba ya fi su tausayi. Masu halasta masa jinin wadanda ba su ba daga musulmi da kirista. Alakarsu da shi ta ban goro da mahauci ne. Samma kal.

Yaro man kaza! Ga yarinta ga giyar mulki. Giyar mulki ta fi kowace giya bugarwa. Labarin da ke riskar mu a ’yan kwanakin nan shi ne wai yana neman a dawo masa da Sayyid Zakzaky don ya hukunta shi, duk da cewa Ubangidansa dan London ya ki bin umurnin kotun kasa na a saki Sayyid, kuma a biya shi diyya bayan an sama masa gida. Kotun kasa da ke Abuja ba kotu bace tunda ba ta yi abin da Buhari dan London da dansa Nasiru Mai gurfani ke so ba.

Tunda Nasiru ya bugu, ya buge da giyar mulki, wacce ta fi kowace giya bugarwa, watakila mu yi hasashen abubuwan da zai hukunta Sayyid Zakzaky a kansu. A watan baya ya ce, zai tuhumi Sayyid da laifin da IMN ta aikata a cikin shekaru talatin. Watakila in giyar ta kara bugarwa ya kara shekarun zuwa sittin. Wannan zai ba shi damar hukunta Sayyid da laifin kawo shahararriyar yunwar da ake cewa 'yar Gusau da juyin mulkin Nzeogwu da kashe Janar Murtala da Farin da aka yi a shekarun baya a duk fadin Najeria, kai duk Afrika, da ambaliyan Teku a Lagos da mace-macen da aka yi a tsawon shekaru sittin da suka wuce. Kar ya manta kama Sayyid da laifin gudun hijirar da shi (Nasiru) ya yi zuwa Amurka a lokacin Umaru ’Yar'aduwa, balle mutuwar diyarsa Yasmir.

Kar ya manta hukunta Sayyid kan wawure kudin Birnin Tarayya Abuja a lokacin Obasanjo. In yana neman laifin lalacewar hanyoyi da rashin magunguna a asibitoci a cikin shekaru sittin, duk ya tuhumi Sayyid. Kar ya manta rashin aiki da tsadar rayuwa, hada da cutar sak da ta dami mutanen Kaduna a ’yan kwanaki. Su ma ya tuhumi Sayyid a kansu. Zan tuna masa wani laifin da zai kara da shi in ya zo tuhumar Sayyid. Rashin lafiyar Buhari dan London. Tunda Gwamna na da Alkalai da Lauyoyi, watakila su daure masa Sayyid shekaru dubu. Shi kuma ya shekara dubu yana Gwamna. Wani abu sai Nasiru a Kaduna. Yaro ga mulki, ga giyar mulki. Wannan shi ne tsohuwar jiha da sabon Gwamna!