AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474

Rahoto

Buhari na murmurewa - In ji Sanata Ahmad Lawan

Daga Danjuma Katsina


 mallam

Majalisar dattawan Nijeriya ta tabbatar da samun takarda daga ofishin Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin kara tsawon hutun da yake yi a London. Shugaba Buhari ya nemi karin hutun ne domin yin wasu gwaje-gwaje da Likitansa ya bukaci a yi masa.

Sanata Ahmad Lawan shi ne Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan, kuma cikin wata hira da BBC a ranar Talatar da ta wuce, ya tabbatar da karbar wannan takardar kafin su dage zaman Majalisar domin yin alhinin rasuwar dan Majalisar Wakilai Hon. Bello Sani daga jihar Katsina.

Ya yi bayani a takaice cewa, “Kowa ya san Shugaban kasa da farko ya tafi hutu na kwana goma. Daga bisani saboda Likitocinsa sun ba da shawarar ya ci gaba da zama inda yake kusa da su, su ci gaba da bincike-bincikensu da ba da magani da kuma hutu, ya sake turo wata takarda ta biyu wadda Shugaban Majalisar Dattawa ya karanta. Saboda haka Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi daidai, haka dokar kasa ta tanada. Kuma mu ’yan Majalisa muna masa fatan Allah ya kara masa koshin lafiya, daga baya ya dawo ya ci gaba da aikinsa na Shugabancin Nijeriya.”

Sannan aka tambaye shi, kamar a wannan karon ya nuna muku yawan kwanakin da yake so? “A’a. Ai bai zama dole ba Shugaban kasa ya ce ga yawan kwanakin da yake so yayin da ya kasance akwai maganar Likitoci suna bincike ko ana shan magani.”

Aka kuma tambaye shi, a matsayinka na daya daga cikin shugabannin Majalisar Dattawa, kun zo nan London don ganin halin da yake ciki, ko me za ka fada game da yadda kuka same shi? Sai ya ce, “Shi Shugaban Majalisar Dattawa ta kasa, Sanata Dk. Abubakar Bukola Saraki, bayan mun ga Shugaban kasa ya yi amfani da wannan dama ya gaya wa ’yan Nijeriya irin halin da muka je muka sami Shugaban kasa. A gaskiya babu abin damuwa, Shugaban kasa yana murmurewa sabanin irin abin da wasu ko abokan adawarmu ko masu yi wa Nijeriya fatan sharri suke ta rurutawa. Shugaban kasa alhamdulillahi, mu da muka gan shi, mun gode wa Allah da ya kara masa koshin lafiya, kuma yana murmurewa.”

Sai aka ce masa, da ka yi maganar murmurewar nan, mutane za su ce ke nan ya yi rashin lafiya, domin ana cewa lafiyarsa lau, babu abin da ke damun sa. Sai ya ce, “Ka san ni ba mai magana da yawun gwamnati ba ne. Ni dan Majalisa ne. Kuma Shugaban kasa dan Adam ne, yau in ya ce Likitoci na masa gwaje-gwaje, kuma ya dan bukaci lokaci ya dan huta, to ka ga a nan ni fahimta ta ita ce lokaci ne wanda Shugaban Kasa za a iya ba shi wasu ’yan magunguna bisa yadda su Likitocin suka ga ya dace da kuma dan hutu haka. Saboda haka ni ban ga wani abu ba. Dan Adam ko yaya yake dole wani lokaci sai ya ji ba yadda yake so ba, saboda jiki da jini.”