AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474

Rahoto

Kotu ta ci tarar Radio Nigeria Pride FM Gusau Kan Kin sa tafsir na Shaikh Zakzaky

Daga Yasir Ahmad Salisu


Wuyan mai

A ranar Alhamis 16/1/2017 Alkalin Babbar Kotu ta 2 da ke Gusau jihar Zamfara ya yanke hukunci a karar da ’yan uwa suka shigar dangane da kin sanya tafsrin Alkur’ani mai girma na Shaikh Ibraheem Zakzaky a gidan Rediyon Pride Fm Damba, Gusau.

’Yan uwa sun shigar da karar ne tun ranar 15/12/2014 bisa ga rashin sanya tafsir din Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakazky da gidan rediyon suka yi, duk da yarjejeniyar da ’yan uwa suka yi da su tare da biyan su kudin sanya tafsir din Naira 210, 000.

Tunda farko Mai Shari’ar Bello Aliyu Gusau, ya dauki tsawon akalla mintuna 45 yana karanto hukuncin, inda ya sossoke hujjojin da Lauyan gidan radiyon ya gabatar a matsayin hujjoji na kin sanya tafsir din Shaikh Ibraheem Zakzaky.

Daga cikin hujjojin da Lauyan gidan radion ya gabatar har da cewa, Shaikh Zakzaky bai da mabiya da yawa a Zamfara, sannan bai da takardar shedar yin wa’azi ta jihar, don haka ba zai dace a sanya tafsirinsa ba a gidan radiyon.

Alkalin ya fara karanto dokoki a sashi na 38 na karamin shashin 1 a kundin tsarin mulki na shekara 1999, wanda ya ba kowane dan kasa damar bayyana da’awarsa da tunaninsa, hadi da addininsa kamar yadda ya fahimta, tare da yada addininsa ko da shi kadai ne. Bisa ga wannan ne Alkalin ya ce, gidan rediyon ba su da hujjar cewa Shaikh Zakzaky bai da mabiya da yawa a jihar Zamfara.

Kazalika Alkalin ya ce ba zai tilasta gidan radiyon su sanya tafsir din Malam Zakzaky ba saboda Majalisar Dokokin jihar Zamfara na cewa, ba a sa wa’azin wani sai da lasisi.

A karshe Alkalin ya umurci gidan rediyon da su biya ’yan uwa kudinsu Naira 210,000, sannan su biya diyyar Naira 100,000 na kin sanya tafsir din Shaikh Ibraheem Zakzaky da suka yi kamar yadda aka yi yarjejeniya da su cewa za su sa a 27/04/2015.

Alkalin ya kara dorawa gidan rediyon na Pride Fm tara ta N50,000 na aikata laifi, wanda jimillar kudin tarar da za su biya ya kama Naira dubu 150.

Mai Shari’a Bello Aliyu ya umurce su da su biya kudin cikin kwanaki 30 daga ranar da ya yanke hukunci.