AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Jimada Ulai, 1436 JBugu na 1172 ISSN 1595-4474

Rahoto

Kisan Farfesa Ahmad Falaki:Alh. Atiku Abubakar ya yi kira ga ’yan sanda

SSANU da NAAT da NASU sun yi kira da murya daya Daga Ibrahim Muhammad da Nasiru Adamua


 NAFDAC

Tsohon mataimakin Shugaban kasar nan, Alhaji Atiku Abubakar ya nemi rundunar ’yan sandan kasar nan ta zo da cikakken bayani game da kisan gillar da aka yi wa Shehin Malamin nan na Jami’ar Ahmadu Bello na Zariya, Farfesa Ahmad Mustafa Falaki.

A wata takarda da ofishin Alhaji Atiku Abubakar ya fitar, an ce bayanan da ’yan sanda suka bayar game da yadda Farfesan ya rasa ransa ba mai gamsarwa ba ne.

Ya kara da cewa shi kansa bayanan da ’yan sandan suka yi abin kunya ne ga kasar nan a idon duniya, domin abin takaici ne a ce ’yan sanda sun gaza gane kimar mutumin da ya kai matakin Farfesa ko da ma a fuska ne, kuma har a gabansu a zarge shi da cewa dan wata kungiya ne ta ’yan ta’adda, a kashe ba tare da bincike ba.

Takardar Atikun ta ce a yadda Farfesa Ahmad Falaki ya rasa ransa, akwai alamun cewa ya yi imanin samun kariya daga ’yan sanda, amma sai ga shi ya rasa ransa a kan idanun ’yan sandan da ya kamata a ce sun kare shi.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce, rashin Farfesa Ahmad Falaki babban rashi ne, ba ga al’ummar Kano kawai da Jami’ar Ahmadu Bello ba, rashi ne ga kasa da nahiyar Afirka gaba daya.

A wani labarin kuma, gamayyar kungiyoyin ma’aikata da ba na koyarwa ba a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sun yi kira da kakkausar murya ga gwammatin Tarayya kan bukatar bin diddigi domin zakulo wadanda suka yi wa Farfesa Ahmad Mustafa Falaki da ke koyarwa a sashen aikin gona, kuma Shugaban shashin binciken harkokin noma (IAR) kisan gilla a kauyen Fala da ke Karamar Hukumar Kibiya ta jihar Kano a kwanakin baya.

Kungiyoyin sun yi bayanin ne ta bakin Shugaban kungiyar SSANU, Malam Iliyasu A. Bello a yayin zantawa da ’yan jarida ranar Talatar da ta gabata a ofishinsu da ke harabar Jami’ar da ke Samaru, inda ya yi nuna takaicinsu kan yadda jami’an ’yan sanda suka jagoranci jama’ar gari wajen yi ma Farfesa Falaki kisan gilla da sunan Boko Haram, duk da ya nuna masu katin shaidar aiki (ID CARD) na cewa shi Malamin jami’a ne. “Wannan na nuna cewa jami’an tsaron kasar nan ba su mutunta katin shaida (ID CARD), ko kuma ba su da ilimin fahimtar sakon da katin shaidar ke isarwa,” in ji shi.

Daga nan Malam Bello ya nuna tsoronsa kan irin wannan danyen aiki na ’yan sanda “wannan na nuna cewa dubban mutanen da ba su san hawa ko sauka ba na rasa rayukansu da sunan yaki da Boko Haram a hannun ’yan sandan kasar nan.”

Daga karshe ya bukaci gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da an bayyana ma al’ummar kasar nan sakamakon binciken da za a gudanar, a kuma zakulo baragurbin da ke cikin jami’an ’yan sanda masu kisan jama’a da sunan Boko haram.

Ya kuma mika ta’aziyyarsu ga Hukumar gudanarwa na jami’ar A.B.U. da abokai da ’yan uwan Farfesa Falaki dangane da wannan babban rashi.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron