Wani Basaraken jihar Imo ya musulunta
ya ba da dalilai
Cif Sylvester O. Dimunah, Mataimakin Shugaban Majalisar Dagatan jihar Imo, ya musulunta.
Basaraken, wanda yanzu sunansa Musa Dimunah, ya ce gaskiyar da ya gani a Musulunci ne babban dalilin da ya sa ya canza addininsa.
Ya ce kyawawan dabi'un wani musulmi mai suna Malam Ibrahim Biobonlomije, tsohon Sakataren Majalisar Dagatan, kuma babban Sakataren Cibiyar Musulunci don samar da zaman lafiya da bincike ta Maishari'a Mamman Nasir ta sa shi ya yanke shawarar rungumar Musulunci.
"Ba na amshi Musulnci ba ne, na koma wa addinin asali ne na kakanninmu wanda shi ne addinin dan Adam tun asali. Irin kyakkyawar mu'amalar musulmi na kaunar kowa da rashin nuna kiyayya ga kowa da yadda suke kaunar Allah da Manzanninsa ba tare da nuna bambanci ba, sun burge ni matuka," ya ce.
"Haka nan kuma 'yan uwantaka da girmama juna da sauran jama'an gari na musulmi, ya burge ne kwarai."
Ya kuma ce, lalle ba wanda ya matsa masa a kan sai ya canza sunansa.
