Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Sojoji sun kai samame gidan Marafan Nasarawa

Daga Aminu Alhassan

Da misalin karfe 9:30 na safiyar ranar Talatar nan ne sojoji dauke da muggan makamai suka shiga unguwar Nasarawa da ke Karamar Hukumar Chukun cikin jihar Kaduna suka bi gidajen Jama'a suka yi masu bincike da sunan suna neman makamai.

Kwamared Nuhu Marafa, tsohon Shugaban kungiyar direbobin tanka ta kasa reshen jihar Kaduna, yana daya daga cikin wadanda Sojojin suka shiga gidansa.

Ya bayyana wa manema labarai cewa ya shirya zai tafi Gusau domin yin ta'aziyar rasuwar kakar daya daga cikin iyalansa, sai kawai aka ba shi labarin ga sojoji nan dauke da makamai cikin motoci akalla ashirin sun shiga layin tanki.

Ganin haka sai ya bukaci da ya san ko su waye? Kuma daga ina suka zo? Wa ya turo su? Kuma me suke nema? Kafin ya zo inda suke, sai kawai ya ji an ce ai ga su nan sun shigo layin gidansa.

Da ga nan sai ya ce wa direbansa Abdullahi da ya juya su koma gida. Kafin su iso gidan har wadannan sojoji sun kama Maigadin gidansa mai suna Abubakar da duka, inda wani ya sa gindin bindiga yana dukan sa, har sai da ya fadi kasa. Daga nan sai suka balla kofar gidan nasa suka shiga .

Shigar su ke da wuya, sai suka tattara matansa suka ce masu su kwanta a kasa, wasu suka shiga cikin gidan suna bincike .

Ana cikin haka ne sai ga Marafa ya iso, sai wani daga cikin su ya ce wai ba zai shiga cikin gidansa ba.

Daga nan Marafa ya ce masu ai ba zai yiwu ba a zo gidansa a ce wai ba zan shiga ba, me suke nema a gidansa? Suka ce aiki suke yi. An taba zuwa aiki gidan mutum a yi bincike, babu takardar shaida daga wajen hukuma? Sai suka ce su dai aiki suke yi.

Ana cikin haka sai jama'ar Unguwa suka ji labarin an zo gidan Marafa za a tafi da shi, daga nan sai suka fito mata da maza, manya da yara suna ce wa "ba mu yarda ba, sai dai a kashe mu, amma ba za mu yarda a tafi da Marafa ba!"

Wadannan kalamai da sojoji suka ji jama'a suna fadi shi ya tsorata su, domin suna tunanin muddin suka bari mutane suka taru, to Allah kadai ya san abin da zai faru, kuma zai iya kawo rashin zaman lafiya a jihar Kaduna baki daya.

Jama'ar unguwar sun fada mana cewa abin da wadannan sojojin suka yi ba shi da bambanci da na 'yan fashi, domin su ma suna zuwa ne su bai wa mutane tsoro da bindiga. Idan ka ba su hadin kai su yi maka sata su tafi, idan ko ka ki ba su hadin kai su kashe ka, kuma su yi maka sata.

Ganin haka sai daya daga cikin sojojin ya ciro wani abu mai kara ya fara busawa, yana cewa sojojin kowa ya fito waje domin jama'a suna taruwa mata da maza.

Fitowarsu ke da wuya sai kawai suka fara harbi a sama, kai ka ce a filin daga suke.

Bayan sojojin sun tafi sai iyalin Marafan Nasarawa suka shiga cikin dakunan da aka yi masu bincike, suka tarar sojojin sun sace masu galila set takwas da kudi Naira dubu dari hudu da kuma zinaren mata da sauran kayayyakin da suka dauka a makwabta.

Tambayar da ake yi ita ce shin gwamnati da gaske ne tana son a zauna lafiya a jihar Kaduna? Don wasu na zargin cewa wani bangaren kungiyar direbobi tanka ne suka ba wasu manyan soja kudi domin biyan bukatarsu kan Marafan Nassarawan.

Da muke zantawa da mai magana da yawun sojoji, Kanar Usman Sani Kuka Sheka, ya karyata zargin da ake yi wa sojojin na satar kayan mutane. Ya ce; sojoji ba sa sata.

"Sojiji ba barayi ba ne. Akwai ka'idojin aiki, babu musguna wa mutum balle a yi masa sata. Ba huruminsu ba ne, su yi sata, balle su mugunawa wasu," a ta bakinsa.

Daga nan ya nemi a sanar da su idan har an samu labarin musguna wa wasu. Mutanen su rika hakuri da su, su rika fahimtar su.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan