Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Yadda aka so yi wa tsohon Gwamnan jihar Yobe 419

Sanata Bukar Abba Ibrahim ya ce kyautar lambar girmamawa ta Mo Ibrahim da ke tafe da kudi Dala 100,000, wacce aka ce an ba shi ba da gaske ba ne, wasu 'yan 419 ne suka nuna masa cewa ya ci kyautar.

Sanatan, wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan jihar Yobe, ya shaida wa manema labarai haka a ranar wata Laraba a kwanakin baya.

"Kira ta waya na samu da kuma sakon gidan wayar DHL daga wani wai Farfesa a Jami'ar Cape Town cewa na samu kyautar girmamawa ta aiwatar da kyakkyawan shugabanci a Afrika na shekarar 2012, wanda Mu'assasar Rockefeller da Mo Ibrahim kan dauki nauyi.

"Ma'aikatana suka tambayi masu shirya ba da kyautar, wadanda suka ce mu mika sunayenmu ga Jami'in tuntuba na ofishin jakadancin Afrika ta kudu don samun biza.

"Sam ba su tambaye mu wasu kudi ba, kuma sun ba da sunayen wadanda za mu tuntuba, abin da ya sa muka zaci hakan da gaske ne, muka raya cewa lalle muna hulda ne da Mu'assasar ta Mo Ibrahim da Rockefeller da ke Afrika ta kudu.

"Wannan ya sa ni kuma na zaku har na rika shaida wa abokaina da iyalina, ana ta taya ni murna.

"Wasu abokan nawa ma har suka kai labarin ga kafafen yada labaru, don haka labarin ya bazu nan da nan.

"Ganin cewa jama'a sun soma shirin kashe kudade don yin biki, sai na ga bari in tsananta binciken da watakila su ma'aikatana ba su iya yi ba. Masu bincikenmu sai suka gano ashe wata gagarumar zamba aka shirya wa manyan mutane daga duk fadin Afrika.

"Muka tuntubi ofishin Mu'assasar Mo Ibrahim da ke London kan batun, wacce nan da nan ta buga sanarwar karyata batun. Mun kuma shaida wa Jami'ar Cape Town, Farfesa Ali Mazrui, Minista Ibrahim Patel na Afrika ta Kudu da wasu da dama wadanda aka sa sunayensu a cikin wannan zamba.

"Na kuma dauki matakin gargadin abokaina da sauran masu yin fatan alheri da abokan aikina a kan kar su tsaya shirin kashe kudi kan batun shirye-shiryen buki.

"A gaskiya na yi mamakin kwarewar wadannan 'yan 419 din. Akwai darussa da dama da za a koya: Ba wanda ya tsira daga irin wannan, ba mutanen gari ba, ba 'yan siyasa ba," ya ce.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan