11 Almizan: A TAKAICE KAI TSAYE
AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

A takaice kai tsaye

GYARA KAYANKA

Aliyu Saleh


 Dahiru Bauchi

Annabi (S) yana cewa; Cetona ga alummata, sai wanda yake son Iyalan Gidana. Jamius Sagir na Imam Suyudi Mujalladi na 2, shafi na 69.

Daga Abbas Abu Turab Potiskum 0806 060 6666.

HIRAR DA KUKA YI DA SHAIKH LAZARE TA SA NI KUKA

Aliyu Saleh don Allah a isar min da jinjinata ga Shaikh Saleh Lazare a kan tattaunawar da kuka yi a kan zuwansa Iran da Iraki. Wallahi da na karanta raddin da ya yi wa wannan da ya kira da dansa ko jikansa, sai da na yi kuka saboda farin ciki, kuma ya sa na kara jadadda baia ga Sayyid Zakzaky. Shaikh Lazare ka farkar da mu daga dogon barcin da muke yi.

Daga Muhammad Nguru

AKWAI LAUJE CIKIN NADI

Me ya hana Buhari dawowa watanni uku? Me ya sa ba shi da lokacin dawowa bayan an ce ya samu sauki? Wadannan suna daga cikin tambayoyin da talakawa ke yi wa kansu sakamakon rashin dawowar Baba Buhari. Kai gasikiya akwai lauje cikin nadi.

Daga Muhammad Salim Sufih Abu-Trab Potiskum 0806 568 3130

DUNIYA BA WAJEN JIN DADIN MUMINAI BA CE

An ruwaito daga Baban Jaafa, Imam Bakir (AS) cewa Manzon Allah (S) ya ce, Allah Madaukaki na cewa, ya ke duniya ki je ki ziyarci bawa Mumini da nauka na balai daban-daban da abin da ke cikin sa na alamuran duniya. Ki kuntata masa a cikin rayuwarsa, kada ki yi masa sakwa-sakwa. A cikin Littafin Mustadrak, shafi 141, Hadisy na 3. Biharal Anwar mujalladi 72, shafi 52, Hadisy 73.

Daga Shana Islam Shadadi Jihar Neja 0701 925 9795

IDAN KUKA CI GABA DA KUNTATA MASA

ALMIZAN ku gaya wa azzalumai cewa, Wallahi Shaikh Zakzaky ne zaman lafiyarsu. Idan suka kuntata masa, za su ci gaba da murmurewa. Domin Allah yana shirya yaki ne da duk wanda ya yi adawa da Waliyyinsa.

Daga Zulyadaini Potiskum 0703 969 9487

ADDUAR WANDA AKA ZALUNTA BA TA DA SHAMAKI

Allah Sarki! Sama da kwana 600 aka dirar wa Jagoranmu da mabiyansa, wasu suna nuna halin ko-in-kula. A karshe ma murna suke. Mu dai kullum muna adduar Allah ya daukar mana fansa a kan wadanda suka zalunce mu da masu murna da zaluncin da aka yi mana. Mun san kuwa babu shamaki tsakanin Allah da adduar wanda aka zalunta.

Daga Musa Kutama 0803 951 6952

KARYA FURE TAKE BA TA YAYA

Allah ya taimaki gaskiya, karya fure take ba ta yaya. Shia jirgin tsira. Yan uwa a kara hakuri, haka hanyar take.

Daga M. Shair

MUN GODE DA RUBUTUNKA

Ba abin da za mu ce a kan rubutun M.I. Gamawa, sai dai mu ce Allah ya saka da alheri, saboda Ustaz Shelleng da Alhaji Mika, Gwarazan duk dan Shia ne a Afrika. Mun gode da rubutunka.

Daga Ahmad Tijjani Isah 0803 836 1928

SARA SA SASSAKA BA YA HANA GAMJI TOHO

Karya fure take ba ta yaya. Wai shin ku a tunaninku za ku iya rushe addinin Allah, to a yi dai mu gani, sara da sassaka ba ya hana gamji toho. In rana ta fito, tafin hannu ba ya kare ta. Kainuwa dashen Allah ke nan. Mu zuba mu gani.

Daga Alhassan Abubakar Kano 0803 828 6357

WANDA YA YI NISA BA YA JIN KIRA

Ga tambaya? Shin dama kirarin da ake wa mai girma Shugaban kasa, Malam Muhammadu Buhari da ake ce shi Mai Gaskiya ne, dama gaskiyar ke nan? Talaka ya yi laifi a yanke masa hukuncin da ya fi karfin laifinsa, mai kudi ko mai mulki ya yi laifi a kyale shi?

Daga Buhari Airport Katsina 0813 066 3742

SUN JAHILCI ABIN DA MUKE YI

Har yanzu alumma sun jahilci maanar ranar Kudus ta duniya. Abin mamaki wani mutum kuma dan Zariya ne yake tambayata meye maanar Muzaharar Kudus da muke yi? Don haka yan uwa mu kara wa alumma bayani, domin sun jahilci abin da muke yi.

Daga Sayyid Muhammad Sakkwato 0905 467 6466

YANZU KALLO YA KOMA SAMA

Bayan auka wa yan uwa da gwamnatin Nijeriya ta yi, wanda ya jawo mutuwar sama da mutane 1,000, sai ta yi zargin sun kafa gwamnati cikin gwamnati ne. To, ga shi yanzu Mista Benjamin Onwuka ya shelanta kafa gwamnatinsa. Yanzu kallo ya koma sama. Ko su Burutai za su auka masu?

Daga Umar Sanda Elgwenty 0803 858 1823

YA NUNA MANA HANYAR TSIRA

ALMIZAN ku isar min da sakona ga azzaluman da suke son ganin bayan Sayyid Zakzaky. Wallahi babu wanda ya isa ya yi wa masa abin da Allah bai masa ba. Muna nan a bayansa, ba za mu bar koyarwarsa ba, saboda ya nuna mana hanyar tsira duniya da lahira.

Daga Shamsu Melastin Bauchi 0812 153 0457

KADA KU YI FUSHI DA SHI

Alummar Nijeriya ku kuka zabi Shugaban da kuke ganin shi ne mafita gare ku. Jagora mai kawo sauyi da canji, mai taimako, masoyi na hakika gare ku. Don haka kada ku yi fushi da shi, kada kuma ku yi kuka da kowa. Na san ba ku manta an kashe Musulmi sama da 1,000 a Zariya, wasunku suna ta murna da dariya ba.

Daga Khamis

MANUFARMU KYAKKYAWA CE

Manufar daawar Sayyid Zakzaky (H) kyakkyawa ce, kuma alheri ga alummar wannan nahiya. Kira ne ga alumma don su fahimci tafarkin tsira. Jagoranta na matukar tausaya wa halin da al'umma suke ciki na danniya da zalunci. Ta yaya ake ci gaba da tsare wannan mutum mai kyakkyawar manufa kwanaki 607, duk da cewa kotu ta ce a sake shi? #FreeZakzaky. #FreedomForZakzaky.

Daga Amina Hasan Yola

MU DA YAN SHIA ABU DAYA NE

Mu yan Darika da yan Shia dukkan mu mun hadu ne wajen son Annabi (S) da Iyalan Gidansa (AS), amma game da Sahabbai su ba su yarda cewa dukkan su mutanen kirki ba ne, dole a ba su yardar ALLAH. Sun ce sun ba su matsayin da Allah ya ba su ne na cewa daga cikin su akwai mumumai, kuma daga cikin su akwai munafukai, inda suka kafa hujja da wasu Ayoyin Alkurani, mu kuwa mun yarda da cewa dukkan su adilai ne, kuma Allah ya yarda da su, in ma sun yi laifi, Allah ya yafe masu.

Daga 0906 133 8283

GASKIYA KUNA KOKARI

Jinjina ga dukkan maaikatan ALMIZAN. Gaskiya kuna kokari, Allah Taala ya kara basira, Allah ya kara tsare ku daga sharrin azzalumai, mashayan jinin bayin Allah. Jinjina ta musamman ga Editan Shafin nan Malam Aliyu Saleh. Allah ya kara sabati. #FreeZakzaky dole.

Daga Shamsiyya Ibraheem Radda (Ahlil Bait 4life).

KA YI MURMUSHI DON SUNNAR ANNABI CE

Ka yi murmushi, domin Sunnar Annabi ce. Ka yi murmushi, ko da makiyi zai ji hushi. Ka yi murmushi, don masoyinka ya ji dadi. Ka yi murmushi, domin shi kansa sadaka ne. Ka yi murmushi, yayin da ka hadu da dan uwanka Musulmi. Ka yi murmushi, domin yana kara kwarjini da kyan fuska. Ka yi murmushi, don yana kara farin jini a tsakanin alumma. Ka yi murmushi, don yawan kwansare fuska bai da amfani.

Daga Khadija Muhammad Maraba, Abuja

BA MU DA WANI ABU DA YA WUCE WANNAN!

ALMIZAN ku ba ni dama in yi tsokaci kan wasu abubuwa biyu; na daya matsa wa Hukuma su bi ummurnin kutu ta saki Jagoranmu ba tare da bata lokaci ba. Na biyu kira ga yan uwa su sauke hakkin Shuhada yanzu ba tare da bata lokaci ba.

Daga Lawal Bishir Jibiya (Baban Maasuma) 0816 431 9350

HABA SISTERS!

Don Allah Sisters mu gyara halayenmu da tarbiyyarmu. Bai kamata a ce har yanzu muna sa-in-sa tsakanin mu da mazajenmu ba, ko da abokan zamanmu ba (da ake kira kishiyoyi). Mu tuna zamantakewar Shahidi Muhammad Turi da Malama Maimuna akwai dimbin darasi a ciki.

Daga Nusaiba Kabir, Ummu Kulsum Kabir Kanhawa

BAYARWA TANA KANA KAWO BUDI

Duba da nauyin da ke kan Muassasatus Shuhada da ayyukan da ke kanta, ya kamata mu sake ba ta kulawa ta daban. Misali yan kasuwarmu da masu sanaar hannu, duk wanda ya yi wata harka ya samu wata falala, ya tuna da Shahidanmu, ya ware wani kaso a ciki ya mika masu. Wannan fa ba wai hakkin wata ba ne. Mu tuna bayarwa tana kawo budi. Kuma kyauta ba ta kawo talauci. Daga Ahmad Abdullahi Funtuwa 0803 212 2892

SU WAYE ZA SU TSIRA A LAHIRA?

Manzon Allah (S) yana cewa: Ba wani bawa da zai tsira a lahira har sai wanda ya yi aiki da abin da Allah ya saukar.

Daga Zainab Umar Abukur

ALLAH ZAI DAUKAR MANA FANSA

Kwanaki 600 da doriya Jagoranmu Sayyid Zakzaky (h) na tsare a hannun azzaluman kasar nan. Duk da kotu ta ce a sake shi, amma sun ki, kuma sai ci gaba da takurawa mabiyansa ake a kowanne lungu da sako. To, za mu ci gaba da fada wa Allah wanda ba ya barci, kuma zai daukar mana fansa a kan wadanda suka zalunce mu.

Daga Kashifu Yusuf Chula 0703 124 1412

MUNA YI MAKU FATAN ALHERI

ALMIZAN ina yi muku fatan alheri da kuma adduar Allah ya tarwatsa makiyanku, kuma Allah ya kwato mana Jagoranmu daga hannun azzalumai.

Daga M. Prince Baber 0703 838 3721

MUN KARANTA HADISIN SALMANUL-FARISI (RA) KUWA?

Yan uwa don Allah mu yi ta nazari. Mun ji yadda wannan bawan Allah ya sha fama da radadin mutuwa da tambayoyin Mala'iku a cikin kabari. Shi ma ke nan mutumin kirki da ya yi kyakkyawan karshe, kuma dan Aljanna. Ina ga mu wadanda ba mu san inda muke ba? Allah ya sa wannan Hadisin na Salmanul-Farisi a kan mutuwa da abin da ya kunsa, ya zama tambihi ga mu rafkanannun bayi. Allah protect our leader Sayyeed Zakzaky (H).

Daga Yahaya Abu Sumayya Yalwan Dass 0802 382 2770.

HARKA KAYAN ALLAH!!!

ALMIZAN ku isar min da jinjinata ga Shaikh Saleh Lazare. Muna da yakinin duk inda Malam Zakzaky yake Allah zai kare shi. Ga shi ta kara bayyana a kasar Iran, makiya sun sha kunya a idon duniya. Ya Ubangiji ka cika wa Malam burinsa.

Daga Abbas Muhammad Sabon Gari Zaria 0816 366 8661.

INA KWAMANDAN NASU YAKE NE?

Ku tambayo min Rarara na Tsoho baban yaro. Tsohonsa ya tsare mana Malami, shi ma Allah ya tsare shi a London. To, ina Kwamandan maharba a yi amfani da makaman Amurka a kwato shi mana!

Daga Awwal Senior Kwala Alkaleri Bauchi

ALLAH SARKI SHIATU ALI (AS)

Allah Sarki Shiatu Ali (AS), kun zama hantsi leka gidan kowa. Babu gadan da babu ku. Wallahi har a gidan makiyanku sai an samu dan Shia. Labbaika ya Al-zakzaky!

Daga Lawal Jume Kadafawa Katsina 0813 372 7371

KUN BUDE WA YAHUDAWA HANYA

Saudi Amerika sai ku zuba ruwa kasa ku sha! Kun buda wa iyayengidanku Yahudawa hanyar cin zarafin yan uwanku Musulmi. Ya kamata ku sani, mulki da zalunci ba ya dorewa ko da da Muslunci, amma mulki da adalci yana tabbata ko da kafirci! Tashar Aljazeera Allah ya shirya. #Free Zakzaky (h).

Daga Alh. Yakuba Jalingo 0803 339 4932

ALMIZAN ALLAH YA SAKA MAKU DA ALHERI

Hirar da kuka yi da Shaikh Saleh Lazare, ta sanya ni zubar da hawaye. Allah ya saka maku da alheri. Allah ya tabbatar da mu, a kan kauna da biyaya ga Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky. Allah ya kwato mana shi.

Daga Jafar Aliyu Unguwar Naladi Dabai 0903 831 5017

KU ISAR MIN DA WANNAN SAKON

ALMIZAN Allah ya taimake ku, shin ta yaya za mu yarda cewa Shia kafirai ne, alhali Izalawa da wasu Kadirawa har da jemagu sukan hadu a kan a kau da Shia? Tambayata a nan gare ku ita ce; gaskiya da karya suna haduwa a kan kau da karya? Ko kuma dai dukkankuku karasa da kanku.

Daga Abu Ubaida Abubakar Nassarawa, Kano Nassarawa

KUN SAN ILLAR DA KE CIKIN HAKA KUWA?

ALMIZAN ku isar min da sakona ga yan uwana mata masu ce wa namiji abokina, ko namijin da ke ce wa mace kawata. Kun san illa da zunubin da ke cikin sa kuwa? Don haka sai a kiyaye.

Daga Bintu Shaheed Abdullah (Rafidiyya) Zariya

RIJIYAR LEMO KE NAN

Shaikh Sani Rijiyar Lemo ka ce sakon kiran da Annabi ya yi wa Muawiyya bai je gare shi ba. To, Sahabban da Manzo ya aika ne suka yi laifi ke nan, ko kuwa? Mun dai san a akidarka dukkan Sahabbai ba sa laifi. Amma ina matsayin wanda Manzon Allah (S) ya aike shi ya ki zuwa?

Daga Adam Daurawa 0706 074 1750

MUNA FADAR ABIN DA TARIHI YA TABBATAR NE

In da ba don yan Izala ba, da ba a san wani abu wai shi zagin Sahabbai ba. Don mu ba ma zagi, amma muna fadar abin da tarihi ya tabbatar ne. Allah kwato mana Jagoranmu.

Daga Ahmad Muhammad Rabi'u Saminaka 0803 159 3654

ALMIZAN ku isar min da sakona ga mahukuntan kasar nan, su sani cewa lallai alamarin Shaikh Zakzaky (h) na Allah ne, kuma ci gaba da tsare shi yana kara nuna wa alumma irin zaluncin da aka yi masa ne. #FREE SAYYED ZAKZAKY (H)

Daga Muhammad Sani Salis Makarfi 0708 716 7389

KUNA SAYEN ALMIZAN KUWA?

Yan uwa mu daure mu dinga zuba jarinmu a inda ya dace. Ina nufin mu rinka sayen Almizan duk mako, saboda tallafa wa Harkar Musulunci, domin ana isar da sako, musamman a kan halin da muke ciki a yanzu saboda kauce wa jita-jita.

Daga Adam Umar S/gari Zaria 0803 548 4000

ANYA WANNAN IRIN SHIAR IMAM HUSAINI (AS) CE?

Idan ka bibiyi tarihi za ka ga irin yadda aka takura gidan Manzon Allah (S) da kisa da sanya guba, kisa da takobi, dauri, walakanci kala-kala. Bayan waki'ar Karbala an yi wata waki'a da ake ce mata waki'atul Fak, wadda aka kashe Ahlul Bait da magoya bayansu wajen 600. Ba don komai aka yi wa Iyalan Annabi wannan taasar ba sai don sun tsaya a kan gaskiya. Sai ga wasu a Nijeriya sun ce su yan Shia ne, amma makasan Shia ne suke ba su kudi da kariya. Anya wannan irin Shiar Imam Husaini (AS) ce?

Daga Muhammad Sani Hadejia 0903 135 0232.

A DUNIYA AKWAI ABIN MAMAKI

Kai lallai in kana cikin duniya ba abin da ba za ka ji ba. Wai yau irin su Shugaban Turkiya ne ke ce wa Musulmi su tashi su kare Birnin Kudus. Shi kuma (Abu Mazim) shi ne mai cewa sun dakatar da tattaunawa da Israila. Na ce wato yau kanku za a ji ke nan?

Daga Magaji Saidu Jahun 0708 571 8447

SISTOCI DA BURAZU KUN BIRGE NI

Ku isar min da sakon jinjinata ga Sistoci da Burazu a kan shiru da suka yi game alamarin bakon London. Mu ci gaba da abin da ke gabanmu na neman ganin an saki Jagoranmu (H). Sannan ina jinjina wa Sistoci, musamman na Dairar Jos a kan irin yadda suke bai wa Harka lokacinsu. Allah ya kara juriya.

Daga Musty Yusuf (Baraa) da Adam Sabo (Caji) Gombe 0903 540 5093