11 Almizan: A TAKAICE KAI TSAYE
AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474

A takaice kai tsaye

HAKURI DA JUREWA BALA’I

Aliyu Saleh


 Dahiru Bauchi

Abi Abdullahi (AS) ya ce: “Ba za ku taba zamowa Muminai ba har sai idan kun zamo amintattu (a wurin mutane), kuma sai kuna ganin yalwar ni’ima a matsayin masifa, domin yin hakuri a bala’i shi ya fi a kan walwala cikin jin dadi”.

Daga Khadeejah Shu’aibu DTM.

BA ZA KU IYA KAU DA MU A KAN FAHIMTARMU BA

Makiya addinin Musulunci, ba za ku iya kau da mu a kan fahimtarmu ba, don ba ku kuka dora mu a kai ba. Abin da ya gagari Mu’awiyya, Abu Sufyan, Yazidu, Ibn Ziyad, Isra’ila da Amurka, ba za ku iya kawar da shi ba. Wallahi karyarku, Shi’a nan gani, nan bari.

Daga Baba Adamu Ridahwiyya Potiskum 0903 313 2422

KUN NUNA WA DUNIYA JARUMTA

Editan Shafi ba ni dama in yi jinjina ga Shugaban Syria Bashar Assad tare da Jagoran Hizbullah. Lalle duniya ta ga namijin kokarinku. Allah ya saka da alheri. Kun can cancanci a yaba maku. Duk kiyayyar mutum a gare ku ya san kun yi maganin makiya kasarku. Kun nuna wa duniya jarumta da sadaukarwa. Kun kwato kasarku daga hannun ’yan ta’addan duniya, har su da kansu sun yarda sun sha kaye a Aleppo.

Daga Magaji Sa’idu Jahun 0808 295 7170

YAUSHE ZA KU FARKA?

Talakawan Nijeriya yaushe za ku farka daga barcin gafala? Yaushe za ku fahimci Mujadaddin zamani? Yaushe za ku amsa kiran Wakilin Manzon Allah? Mafitarmu, addininmu. Na yi yakini da Allah ba za ku samu sauki ba matukar ba ku koma ga Allah ba.

Daga Kabir Abubakar Magama Jibia 0706 300 6035

MUNA JIN DADIN RUBUTUNKA MAI DAUKAR HANKALI

Malam Aliyu Saleh, Allah ya saka da alheri. Gaskiya muna jin dadin rubutunka mai daukar hankalin jama’a mai taken ‘DA WANE LAIFI SOJOJI SUKA KASHE ’YAN SHI’A A ZARIYA?’. Gaskiya muna karuwa sosan gaske, musamman yadda kake amfani tunani da hikima da kuma kwararan hujjoji na Hadisai da Alkur’ani mai girma da tarin hikima. Allah ya karo basira mai tarin albarka. Lallai wannan ma hanya ce ta da’awa. Ni ma ina daga cikin masu ba da shawarar a mai da shi ya zama littafi cikakke. Allah ya kara wa ma’aikatan wannan jarida mai farin jini kariya da nisan kwana. Ya ba mu sabati. #Free Zakzaky.

Daga Sayyida Amina S. Ahmad Gurijigawa.

RANA ZAFI, INUWA KUNA

Na duba Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, duk ban ga hanyar da ta bule ba. Sashen zuciyata ta gaya min cewa hanya daya ce tak take bullewa, ita ce da’awar Sayyid Ibraheem Zakzaky.

Daga Rahama Yusuf Hasan Halkar Dawaki Bauchi

BA KU FI KARFIN ALLAH BA

ALMIZAN ku gaya wa masu fada da mu, in suna ganin sun fi karfinmu, to ba su fi karfin Allah ba. Kodayake kuna da Sojoji da ’yan sanda, kuna da kotuna da Alkalai, amma ba za su gagari Allah ya nuna maku ikonsa ba.

Daga Zulyadaini Potiskum 0703 969 9487

ALLAH KA KARA HADA KAN MUSULMI

Saudi-Amerika ta kama ruhin Nijeriya, wato jami’an mahukuntanta da wasu Malamai domin haddasa wa Musulmi fitintinu. Allah ya sa mu gane, mu hada kanmu, akalla mu kalli junanmu a matsayin Musulmi, sai Allah ya shiga cikin al’amarinmu. Allah ka hada kan Musulmi. Allah ka kara tausaya mana, kar ka bar mu da kawukanmu. Ilahy Ajeeb!

Daga Yahaya Usman Bello Yalwan Dass 0802 382 2770.

ZA MU GA MASU KARYA DOKAR TSAKANIN SU

Wa ke bin dokar kasa, dan kanzagin Yahudu ya ce ’yan IMN ba sa bin dokar kasa. Sai ga shi babbar kotun kasar ta wanke Shugaban IMN, ta ce a sake shi, a biya shi diyya, a gina masa gida a cikin kwanaki 45. Yanzu za mu ga masu karya doka tsakanin gwamnati da IMN. Happy Maulud!

Daga Adamu Sabo Caji Gombe 0706 423 7129

HARKA KAYAN ALLAH!

Azzalumai sun zata cikin awa 24 za su shafe Harka, su mai da ta tarihi abin tunawa. Kodayake zuwa yanzu sun gano mafarkinsu na rusa Harka cike yake da surkulle. Wallahi sai mun kure muku gudu, da kanku za ku ba da bayanin cewa ku azzalumai ne!

Daga Sani Rabi’u R/lemo, Kano 0703 122 8437

ALLAH KA DAUKAR MANA FANSA

Allah ka yi mana maganin wadannan azzaluman. Allah kana gani sun kure zaluncinsu a kan raunanan bayinka. Sun mai da kisa, kamu, dauri, raunatarwa, rushe gine-gine, sharri, kage, ga kuma takunkumi a kan masu riko da addininka abin yi a ko’ina. Allah kai ka ce mu roke ka, mun roke ka da sunayenka tsarkaka, da bayinka na gargaru. Ya Allah albarkacin jinin Imamu Husaini (as) ka daukar mana fansa.

Daga Haura’ulinsiyya Jamilu Shahada (Maman Zee)

ALLAH YA KWATO MANA SAYYID

Allah ya kara mana son Iyalan Gidan Annabi. ’Yan uwa a dage da yin komai na hidimar Mauludin Annabi kamar yadda Abbah (H) ya koyar. Kuma a ci gaba da yin addu’o’in kamar kullum. Allah ya kwato mana Sayyid.

Daga Fatima Bintu M. Sani Katsina 0816 369 9693

KARYA BA TA ZAMA GASKIYA

Na tuna maganar su Sayyid Zakzaky, inda yake cewa ita karya ko shekara 100 za a yi ana yin ta, tana nan a karyarta, ba za ta dawo ta zama gaskiya ba. ’Yan uwa mu ci gaba da bin jagoranci. Tunda suka auka mana, suke ta karerayi da sharri kala-kala, don su dagula lamarin, amma sakamakon bin jagoranci da muke, sun kasa dagulawa. Duk shairin da suka yi sai mu girbi alheri. Sai na tuna lokacin Janar Ta-zarce da suka ga komai ya kubuce masu, sai suka yi wa Malam tayin afuwa. Shi kuwa ya ce wanda ya yi laifi ake yi wa afuwa. Daga karshe suka sake shi cikin izza. To, yanzu ma za su maimaita

Daga Ibrahim Wasiy Liman Cikaji Zaria.

ASHE GOC ADENIYI KA IYA SULHU?

Abin mamaki wai GOC na barin sojoji na runda ta 1 da ke Kaduna, Adeniyi Oyebade ya je Zamfara don sasantawa da wasu barayin mutane da shanu masu dauke da makamai. Daga ciki har da wani da ake kira ‘Buharin Daji!’ Ashe GOC ka iya sulhu da masu dauke da makami, amma ka zabi ka yi kwanaki kana kisa ga mutanen da ba su dauke da ko allura a Zariya?

Daga Mukhtar Sani

HAKA HANYAR TAKE

Ya ’yan uwa ma’abota wilaya, mu yi hakuri da kuncin da muke ciki na rashin Jagora a tare da mu, sannan mu kasance cikin ma’abota bin jagoranci. Azzaluman nan ba za su taba cin nasara a kanmu ba. Wallahi! Mu ke da nasara insha Allah.

Daga Nusaiba (Momyn Kausar) Kano.

A GAGGAUTA SAKO MANA JAGORANMU

Mu ’yan uwa almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky muna kira ga gwamnati ta gaggauta sako mana Jagoranmu ba tare da ka ce, na ce ba.

Daga Adamsy Musa Gombe 0907 595 2104

TAKA MA’ABOTA ADDINI BA RUSAU BA NE A ABUJA

ALMIZAN ku fada wa Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa’i, taka ma’abuta addini ba rusau a Abuja ba ne, wadancan wasunsu irinka ne, amma za ka san da Allah kake ja. Ba a fada da Allah a kwashe lafiya.

Daga Halilu Kebbi State 0703 292 2021

JAMA’AR KASAR NAN YA KAMATA KU HANKALTA

Idan za ku shekara dubu kuna zaben Shugaba, kuna darjewa daga ko’ina a fadin kasar nan, to fa haka za a yi ta yi, ana cewa gwamma jiya da yau.

Daga Abu Mujahed D. K. 0806 677 0596

SHEKARA 1 DA WAKI’A INA ITTIHADU NE?

Edita ba ni dama in mika tambayata ga ’yan uwana masu ba da gudumuwarsu ta hanyar wake (Ittihadu) cewa, yanzu mene ne maudu’in da ya kamata a mai da hankali a kansa cikin wake a Harkance? Abin lura ga Ittihadu a nan, su sani kowane bangare a cikin IMN suna yin komai nasu iri daya, kuma lokaci daya. Misali ISMA, abin da ISMA suke yi Zariya, in ka je Kano shi za ka tarar. Haka abin yake a Hurras. To mu Ittihadu haka muke? To, me ya sa ba za mu zama haka ba?

Daga 0816 431 9350

ALLAH YA TABBATAR DA MU

Kamar yadda Annabi Muhammad (S) ya koya mana fatan alheri da kyawawan addu’o’i ga kawukanmu da mu’uminai kulliya, kar mu yi sakaci gurin addu’a. Allah ka kara wa Abba (H) lafiya da haiba, mu kuma ya tabbatar da dugaduganmu a kan addininsa karkashin wilayar Amirul Mu’uminina da zuriyarsa gaba daya.

Daga Nusaiba Kabir Roni

MUNA TARE DA JAGORANMU

ALMIZAN ku isar mani da sakona ga Malaman Saudiyya da Wakilinsu na kasata Nijeriya cewa, duk sharrinsu ba za su raba mu da Jagoranmu ba, kuma muna nan tare da shi a kowane yanayi insha Allah.

Daga Lawal Bishir Jibia (Baban Ma’asuma) 0814 556 3154

SHAWARA GA MATASAN HARKA

Ya kamata ’yan uwana matasa mu rika biyan hakkin Shuhada, ba sai iyayenmu sun biya mana ba. Ba mu gani yadda ake samun Shahidai a kowane lokaci? Ko da mutum ba ya sana’a, to ya dinga cire wa a kudin makarantar da ake ba shi ko da Naira 20-20 ne, idan ya hada a shekara zai ba shi 1200, kun ga sai mu hutar da iyayenmu ke nan. Allah ya sa mu dace.

Daga Zeenat Isah Nguru

BA GUDU BA JA BAYA!

A kullum muna kara samun yakini a kan Harkar Musulunci karkashin jagorancin Allamah Ibraheem Zakzaky (H). Idan aka kama mu, aka tsare, sai mu tuna tsarewar da aka yi wa Imam Hasan Al-askary (AS). Idan aka kashe mu kuma, sai mu tuna kisan da aka yi wa Imam Husain da Sahabbansa a falalin Karbala. Komai aka yi mana, to an yi wa magabatanmu, kuma bai sa sun bar abin da suke a kai ba, kamar yadda bai hana addinin tabbata ba. Don haka muna nan a Harkar Musulunci, ba gudu, ba ja da baya!

Daga Amina Hasan Yola.

BA ZA MU MANTA KISAN DA KUKA YI MANA BA

Shin wace riba ce ko ci gaba kuka samu da zubar da jinin ’yan uwanmu Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) fiye da mutum 1000 a kasar nan? Shin kisan nan da kuka yi wa ’yan uwanmu dama shi ne matsalar kasar nan? Ko kuwa a kansa ne aka zabe ku, ko kuma aka dauke ku aiki? Ku sani, kuma kar ku manta aikinku ko mulkinku mai karewa ne, haka kuma abin da kuka aikata mana yana nan a zukatanmu, ba za mu taba yafewa ba? Muna rubuce da shi da tawadar da ba ta gogewa, komai daren dadewa ba zai gogu ba. Muna kira gare ku da gaggawa a kan ku gaggauta sakin Jagoranmu, Shaikh Zakzaky (H) tare da ’yan uwanmu fiye da 500 din da kuke tsare da su.

Daga Abdullahi Gambo Shi’it Katsina

WANNAN ITA CE TARBIYYAR GIDAN ANNABTA

Imam Suyudi ya rawaito a Tarikhul Khulafa nasa shafi na 177 karkashin fasali kan Hasan Bin Ali Bin Abi Dalib (RA), daga Umar Bin Is’hak ya ce: “Marwan Bin Hakam ya kasance Shugaba a kanmu (mutanen Madina), kuma yana zagin Ali (RA) duk ranar Juma’a daga kan mumbari, alhali Hasan (RA) yana jin sa, amma ba ya tanka masa”. Wannan ita ce tarbiyyar gidan Annabta. Manzon Allah (SAW) da addinin rahama ya zo, ba addinin tsinuwa da la’anta ba ne.

Daga Sunnah Sak 0813 938 7490

NASIHA GA ’YAN UWA

Tabbas karya za ta gushe, kada ka damu da tambayar yaushe? Gaskiya za ta bayyana komai dadewa. Abin da ya kamata ya dame ka mene ne matsayinka? A kan gaskiya kake, ko a’a? Allah ka ba mu hakuri da juriya a kan jarabobi. Ya Allah kwato mana Sayyid Zakzaky.

Daga 0706 627 9475

KO SAI AN KAI KA GIDAN MALAM NIGA NE?

Ka ce ka soke Harkar Musulunci (IMN) ta ’Yan Shi’a a Nijeriya. Kuma ka dada zuwa kafar yada labarai ka ce wai ‘Kungiyar Alzakzaky’ ka hana, ba Addinin Shi’a ka hana ba. Anya babu motsi a cikin kwakwalwarka kuwa? Ko sai an kai ka gidan Malam Niga ne?

Daga Umar Takai.

MUTANEN GYALLESU

Ni dai ban san su waye mutanen Gyallesu da Gwamna yake nufi ba? Kila Wahabiyawa da ’yan bokon Gyellesu yake nufi? Wadanda wasu tare suka yi karatun boko, wadanda suke yi ma Malam hassada don Allah ya fifita shi a kansu? Saboda su dama ba su san komai ba sai duniya, kila ma addinin nasu suna yi ne don duniya, kamar yadda Manzo (S) ya ce, wasu mutane suna addini ne don biyan bukatar duniya. Gwamnan Kaduna ya ce, IMN ba ta bin dokar kasa, wannan maganar ba gaskiya ba ce, mu ’yan kasa ne, duk abin da dan kasa yake yi muna yi, amma shi yanzu shi ne aka ba aikin kawar da IMN, wai don samun daurin gindi zai hukunta IMN da laifukanta na shekara 30. Shugabannin baya ba su iya aiki ba shi ne ya iya. Ga fili ga mai doki!

Daga Sani Muhammad

NA YI WANI MAFARKI MAI DADI

Allah ya yi min dace na yi wani mafarki mai dadi. Ni da Babana da dan uwana Zainal Abidina, mun tafi Tattaki, sai ga Sojoji suna ta harbi. Sai na ga Imam Mahdi (ATF) ya diro daga sama. Sai na ga Mala’iku suna ta saukowa daga sama, suka shiga tsakanin mu da masu kashe mu. Sai ga Sharafuddini Allama Zakzaky (H) yana murmushi dauke da tutoci dubu 12, duk an rubuta “Ya Rasulullahi!

Daga Jamilu Idris Kwarkiya Minjibir, Kano

KASHE MANA ’YAN UWA BA ZAI SA MANA RAUNI BA

Kamun Malam Zakzaky, ba zai sa mu yi saranda ba. Kashe ’yan uwanmu, ba zai sa mana rauni ba. Rushe-rushe, ba zai sa mana tsoro ba, sai dai karin izza.

Daga Muhammad Sani Salisu Makarfi 0803 501 9381

Wa’azi, hali da ayyukanmu, su zama sun fi wa’azi da zantukanmu

A ci gaba da raya al’amarin Manzon Allah a watan da aka haife shi, a wannan makon shafin na dauke muku da jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda ya gabatar ga miliyoyin al’ummar Musulmin da suka halarci Muzaharar Maulidin Manzon Allah, wadda ta gudana a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal, 1436 (8/1/2015) a Filin Polo, daura da Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta.