AlmizanAlmizan logo
Juma'a 20 ga Safar, 1435 Bugu na 1161 ISSN 1595-4474


Rahotannimu

 UN
Al’umma na gamsuwa da tattakin Funtua zuwa Zariya
ShaikhKasimu Umar Sakkwato

Dubun-dubatar ’yanuwa musulmin sukayi tattakinArba’in din shahadar Imam Husain (AS) daga Funtua zuwa Zariya Bakiyyyatullah, dauke da tutoci, kuma sanye da bakaken kaya.

Wuyan mai
Tattaki jaddada bai'a ne ga Imam Husaini(AS)
In ji Malam Adamu Ahmad Tsoho Jos

A zantawarsa da Wakilinmu a yayin tattaki, rana ta biyu daga yankinPambeguwa zuwa Zariya a kasa, Wakilin 'yan uwa na Jos, Malam Adamu Ahmad Tsoho ya ce, Tattaki kamar jaddada bai'a ne ga Imam Husain, da kuma fito da hakikanin abin da ya faru da shi ga al'umman duniya.

 NAFDAC
Nasarorin cikin wannan tattaki suna da yawan gaske
In ji Imam Yakubu Kurna

Wannan ita ce tattaunawa ta musamman da muka yi da Mal. Imam Kurna, Shugaban Halkar, Rasulul Akram, dake Kurna, Kano, kuma Shugaban Kwamitin fadakarwa ga ’yanuwa kan illar oba-lodi a motoci da mashina, sannan shi ne, Shugaban tafiya Tattaki daga Kano zuwa Zariya, wadda wannan santa, ta hada, Kano, Fataskum, Jigawa, Maiduguri, Guru d.s.s.

Sauran rahotanni


Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H): Zakzaky (H)


Bidiyo (H)

Hoton Bidiyo:

Jawabin Sayyid Zakzaky (H) ranar maulidin Sayyada Zahra (SA) a Zariya


Albishirinku

Almizan
Android
Duk mai na'ura ko waya da ke da "Android" yanzu zai iya karanta AlMizan ta na'uran ko wayar tasa.

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.


Free counters!Labaran Harka Islamiyyah


Tunatarwa:

Zakzaky (H)

Tare da Sayyid Zakzaky

Wane ne aka farlanta a yi masa da’a dole?

Wannan shi ne jawabin da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi a daren rana ta 5 da fara zaman juyayin Ashura a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta muku./span>

IN DA KOWA ZAI BA DA HAKKIN SHUHADA

Sakamakon ’yan uwa suna gyara kaburburan Shahidai har wasu ma sun fara koyo. To, amma inda mutum zai je sauran duniyar musulmi zai ga cewa, wannan abu ne zaunanne. Ana kyautata makwantan mutane, ana kuma tunawa da su ta nan. To, Shuhada’u ‘khasatan’ da ma dukkan sauran wadanda suka mutu. Amma ‘khasatan’ Shuhada suna da wannan hakkin.

Sannan kuma suna da hakki na kula da iyalansu, ainihin abin da suka bari baya - matansu da ’ya’yansu da iyayensu. Har wala yau, wannan yana dan dada sanyaya rai. Ya dan kwantar da hankalin mutum, ya rika tunawa da nasa. Da zafi mun sani. Da zafi! Da zafi, amma kuma zai dan sa shi ya yi tunanin cewa, ran dansa, bai tafi a kawai ba, insha Allah...
Ra'ayin Almizan

Wakilanmu
Almizan
Sharri Kayan Kwalba!

Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...


Daga Gidan Annabta

Tare da Abubakar Abdullahi Almizan

Salati
Ayyukan ban kwana da watan Rajab

SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB

Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR

Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...


Katun

Mutane ke tuttudowa su ji daga bakin da ke fadin gaskiya
Katun
Ba da bindiga muke tara mutane ba


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA BIKIN NISFU SHA'ABAN
  Imam KhomeiniAna sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi bukukuwan NISFU SHA'ABAN na bana wanda za a gudanar kamar haka:

  Rana:
  Juma'a 2 ga Zulhijja 1435

  Lokaci:
  Yamma zuwa dare

  Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

  Rana:
  Asabar 16 ga Sha'aban 1435
  Jawabin Yaumul Taklif da sallah da yara

  Lokaci:
  Safe zuwa rana

  Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah

  Rana:
  Asabar 16 ga Sha'aban 1435

  Lokaci:
  Yamma zuwa dare

  Gagarumin majalisin mawaka wanda Alh Mustapha Umar Baba Gadon Kaya jai jagoranta

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah

  Rana:
  Lahadi 17 ga Sha'aban 1435

  Lokaci:
  Safe

  Gasar fareti da Harisawa zasu gabatar
  Mai karbar fareti: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
  Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

  Wuri:
  Filin Polo gefen Hussainiyyah Bakiyatullah
  Allah ya ba da ikon halarta


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan Arba'een na bana 1436 AH

  • ashh1Hotunan Arba'een na bana 1436 AH
  • ashh2
  • ashh3
  • ashh4
  • ashh5
  • ashh6
  • ashh7
  • ashh8
  • ashh9
  • ashh10
  • ashh11
  • ashh12
  jquery photo gallery by WOWSlider.com v5.3


Ra'ayoyinku na baya-bayan nan zai bayyana nan gaba kadan...

Tambihi:

Muhammad Sulaiman

Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna

Ranar Arba’in din Imam Husain (AS)

Ranar Arba’in din Imam Husain (AS) rana ce, wadda take da muhimmanci, musamman ma ga mabiya Ahlul bayt (AS).