AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

An yi min duka saboda na yi ‘Free Zakzaky’ a ofishin ’yan sanda a Abuja -Adamu Yaro Damaturu


Imam Aliyu

Malam Adamu Yaro, dan Damaturu ne a Jihar Yobe, yana cikin ’yan uwan da jami’an tsaro suka kama a lokacin da suke gudanar da Muzaharar ‘Free Zakzaky’ a Abuja a makon jiya. Daga bisani kotu ta bayar da belin su. Ya bayyana mana yadda aka kama shi da kuma dalilin dukan da aka yi masa. Aliyu Saleh ne ya yi hirar ya rubuta mana. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Za mu so mu ji sunanka?

ADAMU YARO: Sunana Adamu Yaro Damaturu.

ALMIZAN: Kana daya daga cikin wadanda aka kama a Abuja a lokacin da kuka je Muzaharar neman a saki Shaikh Zakzaky, ba mu labarin yadda aka yi aka kama ka mana?

ADAMU YARO: Yadda abin ya kasance shi ne, dama an sanya za a tayar da Muzaharar neman a saki Shaikh Zakzaky domin ya je ya samu ganin Likita karshe 12:00nr a Federal Secretariat. An ce duk yadda za a yi mutum ya samu a kansa a wannan wajen a daidai wannan lokacin. Mun shirya mu biyar muka tari tasi, muka kama hanya. Muna isa wajen, sai muka ga jami’an tsaro tsattsaye da makamai ta ko’ina suna ta kama mutane.

Jami’an tsaro din ne suka tsayar da motar da muke ciki, suka bukaci mu muna masu ID Card, na nuna masu, sai aka ce in koma cikin mota. Su kuma sauran sai aka kama su. Sai suka lura ai daya daga cikin mu ne ya biya mana kudin motar mu duka. Sai wanda ya kama mu ya ce ya fahimci tafiyarmu daya, don haka ni ma sai aka fito da ni. Sai suka sanya mu a cikin wata fara Hilux, suka shigar da mu cikin ofishinsu da ke Federal Secretaiat. Sai suka ga muna kara yawa, domin mun kusa 200. Sai muka fara ‘slogans’ na ‘Free Zakzaky’ a wajen. Sai suka ga ba aminci a wajensu a kan su bar mu a wajen. Sai aka rika fitowa da mu ana sanya wa a mota ana fita da mu. A nan ma sai wasu daga cikin mu suka fara yin ‘Free Zakzaky!’

Ni dai na ga cewa na zo yin Muzaharar Free Zakzaky ne, kuma ban kai ga zuwa wajen ba aka kama ni. Shi ya sa na ga wajibi ne in yi Free Zakzaky a nan wajen da aka tsare ni da kuma a mota kafin a tafi da ni. Ka ga na sauke nawa nauyin. Ai fa sun bubbuge mu sosai, musamman ma ni, sun farfasa min jiki. Har yanzu bayana da kaina suna yi min ciwo. Sun zazzaga mana tiyagas fuska, sannan suka jefa mu a cikin motarsu, suka kai mu ofishin ’yan sanda ake kira SARS da ke Abatuwa, suka zubar da mu a rana, suka sa muka kwakkwanta.

Bayan tafiyar su, sai wasu jami’an tsaron suka ce mu tashi, suka sanya mu a cikin wani ofishinsu, har da fanka a ciki. Gaskiya a wajen ba su matsa mana ba. Sun rika barin masu sai da kayan abinci suna kawo mana muna saya. Da yamma suka zo suka dauki bayaninmu (statement). Washegari da safe kuma aka kai mu kotu.

A kotu an kasa mu gida uku. Ni ina cikin kashi na biyu. Sun tuhume mu da cewa wai muna tayar da hankali. Muna dukan ’yan sanda. Muna fasa gilasai. Alkaliyar ta tambaye mu haka ne? Na ce ba gaskiya ba ne.

Ta ce in kana waya, sai aka ce kudinka ya kare sai minti daya, za ka iya tattara duk bayanin da kake so ka yi a cikin wannan minti daya din. Sai ta ce a cikin minti daya in yi mata bayanin abin da ya faru. Na ce mata abin da ya faru da mu shi ne; mun zo daidai Federal Secretariat kawai sai suka kama mu, kuma mu dama abin da ya kawo mu mun zo mu yi kira ne a saki Malaminmu don ya je ya ga Likita.

Ta yi niyyar bayar da belinsu, sai mai gabatar da kara ya bayyana cewa bai dace a sake mu ba, sai kawa ya kawo wani babban mutum da zai tsaya masa. Alkaliyar ta fuskata sosai da wannan maganar. Ta ce masa akwai wani babban mutum da suke da shi da ya wuce Malaminsu da kuka kama kuka tsare? Daga nan sai aka dage karar zuwa ranar Talata 6 ga Maris, 2018. Ta ce a samu mutum daya da zai tsaya mana duka. Kawai ta ce zaman kotun ya tashi.

ALMIZAN: Wannan kamun da aka yi maku ya rage maku karfin gwiwa na wannan fafitukar taku kuwa?

ADAMU YARO: Wannan kamun da aka yi mana ya kara mana karfin gwiwa ne. In ban da ni ban san ko akwai wanda ya taho a washegari ba, dukkanmu an koma an ci gaba da Muzaharori na cewa lallai a saki Jagoranmu domin ya je ya ga Likita.

ALMIZAN: An ga Shaikh Zakzaky yana hira da manema labarai bayan shekaru biyu, kana ganin mazuharorin da kuka yi sun taimaka wajen matsa wa gwamnati lamba ta bar shi ya bayyana?

ADAMU YARO: Lallai haka ne. Wannan matsin lambar da aka yi ta yi na kwanaki biyar a jere sun taimaka. ’Yan uwa sun sadaukar da lokaci, lafiya da rayukansu, sun jajirce, sun hana su sakat a cikin Abuja.Wannan shi ne ya tursasa wa gwamnati ta bari Malam ya fito a gidan talabijin don a ga cewa lafiyarsa lau, musamman da yake fiye da shekaru biyu ba a gan shi a bainar jama’a ba, sun yi haka ne don su samar da lalama, don a rage wannan matsin lambar da ake yi masu.

Wannan kuma sun yi kuskure, domin yanzu muka gane ashe matsin lamba na sa a ci nasara? Shekaru biyu ba su bari Malam ya fito ya yi magana ba, sai bayan matsin lambar kwanaki biyar, ga shi yau Malam ya fito ya yi magana? Ashe in muka ninka matsin lambar da muke yi, insha Allah za a kai ga natija.