AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Waki’ar Tattakin Kano: Satina daya da aure aka kama ni - In ji Malama Nusaiba Muhammad

Daga Aliyu Saleh


Maulid Sayyada Fatima

Mai karatu ga hirar da Wakilinmu Abdullahi I. Ahmad ya yi da Malama Nusaiba Muhammad Sani, wadda aka kama a waki’ar Tattaki na Kano, amma aka ba da belin su a kwanakin baya. Wannan ’yar’uwa, lokacin da waki’ar ta auku, ba ta wuce sati guda da tarewa da Angonta…..

ALMIZAN: Da farko dai za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.

MALAMA NUSAIBA: Ina farawa da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai, Mai kowa, Mai komai, wanda ya kawo mu wannan lokacin. To, ni dai sunana Nusaiba Muhammad Sani. Kuma ni haifaffiyar Kaduna ce, amma yanzu ina zaune a garin Kano saboda a can nake aure.

ALMIZAN: Ko za ki iya ba mu labarin abin da ya faru lokacin tattaki, a Kano?

MALAMA NUSAIBA: A ranar 14 ga watan Safar 1438, wanda ya yi daidai da 14 ga watan Nuwamba, 2017, mun fito tattaki domin tunawa da Imam Husaini Alaihissalam da iyalan gidansa. Mun fito cikin izza, saboda muna da burin ganin mun sami falalar da ke cikin tattakin. Kuma Alhamdulillah da har muka sami nasarar fitowa din. Ya kasance an fara tattakin ne daga gadar Na’ibawa da ke Kano.

Mun fara tafiya, bai fi da kamar minti ashirin ba, sai muka ga motar ’yansanda ta zo ta wuce ta gabanmu. Muna cikin tafiya, wata ma ta kara zuwa ta wuce mu, kwara biyu ke nan. Suna yin gaba, sai suka fara harbo mana ‘tear-gas’. Muna tare da wata ‘sister’ ana ce mata Sumayya, sai nake ce mata kada mu samu damuwa, irin wannan abin da azzaluman nan suke son su yi mana, sun yi wa Jagoranmu a garin Zariya. Kuma kada ki manta saboda wane ne muka fito tattaki, sannan kuma meye makasudin tattakin?

To, har lokacin da ya zama suna ta harba ‘tear-gas,’ har ‘tear-gas’ din ya yi ‘over’ sosai. Ni kuma a fitowa da na yi, na fito ne da burin in ga cewa na yi shahada, don kafin lokacin ma, duk wanda ya yi magana fada nake cewa, shahada nake buri. Haka kuma muka ci gaba da tafiya suna sa mana Tiyagas din. Da ya yi ‘over’ haka, sai na kira Ummana na ce ki sa ni a addu’a, Allah ya cika min burina, saboda na ga azzalumai sun fara kawo mana hari. Sai take cewa, me suka fara? Sai na ce ai ko sun fara sa mana tear-gas, ga shi kuma har ya fara yi wa mutane illa, tunda a lokacin har wasu sun fara faduwa, wasu kuma sun fara jin jiki.

Haka nan dai muka ci gaba da tafiya har ya kasance ‘tear-gas’ din ya yi ‘over,’ har ya zamo mun canza hannun titin da muke na bangaren hagu muka tsallaka muka koma na dama. Bayan mun koma din ma kuma dai suka ci gaba da harba mana ‘tear-gas’ din har dai ya kasance mun sake dawowa wannan titin da aka bari din.

A haka nan dai muka yi ta tafiya har muka isa Kwanar dawaki. A lokacin da muka iso garin, gaskiya mun galabaita sosai, ga shi kuma akwai rana mai zafi, ga kuma kishi muna ji sosai. Duk wanda na hadu da shi a wannan lokacin, zai ce min kishi yake ji. Har da yawa sukan tambaye ni, don Allah ‘sister’ kina da ruwa ki sam min in sha. Saboda gaskiya ranar ta yi yawa, ga kuma ‘tear-gas’ mutane duk sun galabaita sosai.

To, a lokacin ni ma sai nake ce wa wata Nusaiba da muke tare, ta taimaka ta siyo min ruwa, ni ma kishi nake ji. Sai take cewa, ai an ce kada mu sayi ruwa a wani wuri. Sai nake ce mata ni kam dai haka nan za mu karya wannan doka gaskiya, saboda kishin da nake ji ya wuce misali. Nan dai a hakan ta sayo min ruwan. Na bude ke nan zan sha kawai, sai suka harbo wani ‘tear-gas’ ya fado daidai gabanmu. Sai hayaki ya lullube mu. Sai ta samu dai ta ja ni muka fita.

Mun fara gudu, ashe gaban namu ma sun harbo wani. Mutane har sun faffadi a kasa, mu kuma ba mu sani ba. Mun taho, sai muka yi ta faffadawa kan mutane; duk wanda ya zo kuma sai ya fada kanmu. Akwai burazun da ke bayanmu, sai suka zo suka rika daga mutanen da ke wurin. Sun kwashe kowa, sai ni kadai na rage. Can sai wani buraza, mun dai zauna tare da shi a ‘prison,’ amma ban san sunansa ba, ya kasance a wajen; daga ni, sai shi kadai muka rage, ga shi azzaluman sun iso kusa, tazararmu da su bai fi taku goma ba. Shi kuma ya rike ni, yana ja na, su kuma suna ce masa, “Ka sake ta ko mu harbe ka”. Sai na ce wa Burazan, “Ka sake ni ka tafi, kar su harbe ka”. Sai yake ce min ba zai sake ni ba. Ya ce, saboda Sayyid yana cewa, “mu tsaya wajen kare ku (sisters) mu ba da rayuwarmu, to a kan me zan tafi in bar ki?” Na ce masa, “To, amma kuma ga Muzahara ta yi mana nisa, ga su kuma kusa da mu, ko da harbin naka za su yi, nan da nan zai same ka.” Da dai kuma suka iso daf da mu, sai ya sake ni din.

ALMIZAN: Wato a lokacin ke ba ki da karfin tafiya da kanki ne ko kuma gudu ke nan?

MALAMA NUSAIBA: Wannan gaskiya ne, saboda ‘tear-gas’ din ya yi min illi sosai.

ALMIZAN: To da suka iso gare ki, me ya faru?

MALAMA NUSAIBA: Bayan burazan nan ya tafi, sai kawai na tsaya a inda nake, suka iso kaina. Da isowarsu, sai wani dansanda ya daddage ya gaura min mari, wani ma ya kara gaura min. Kawai sai suka hau duka na, daga wannan ya zo ya haure ni, wannan ya tadiye ni. Wani ya zo ya yi kukin bindiga zai harbe ni, sai wani ya ce masa kar ya harbe ni. Sun yi min duka sosai, tsabar dukan ne ya sa ni suma. Farkawa na yi na gan ni a cikin mota, babu hijabi, sun cire min. Wayata da takalmina da kudadena, duk ban san inda suka yi ba.

Ko da na farka kuma a cikin motar, sai na ga ga shi har sun harbi mutane uku, don biyu daga cikin su ma har sun yi shahada. Amma su biyun ban ga fuskokinsu ba. Sai dai mutum dayan da suka hada kafafunsa da hannayensa suka daure, sai yake ta cewa shi ba dan Shi’a ba ne, su taimaka su sake shi; ya zo tsallaka titi ne, saboda haka su taimaka su sake shi, wallahi shi ba dan Shi’a ba ne. Ni kuma da na ji yana wannan cewa shi ba dan Shi’a ba ne, sai na je ina so in kwance shi. To, ashe wani dansandan ya gan ni, ban sani ba. Na kama zan kwance, sai ji na yi wani ya mare ni, ya fara zagi na, “Don Ubanki ba ki da mutunci ne? Ke yanzu mu kamo ki kuma har ke ce za ki kwance wani.” Daga nan ne suka ce, ai idan suka bar ni a bayan motar zan taimaka wa wannan mara lafiyan, saboda haka a dauke ni a sa ni a cikin motar. Sai suka dauke ni suka saka ni a cikin motar.

Duk wanda ya zo wucewa sai ya ce min, “Ke ma yar Shi’an ce?” Sai in ce, “Eh”.

Wani da ya tambaye ni, sai na ce, “Eh, kakana ma dan Shi’ah ne!” Sai yake ce min “Amma ba ki da hankali, yanzu mun kama ki din, ko kashe ki ne za mu iya yi ba abun da zai faru, har za ki bude baki ki ce min kakanki ma dan Shi’a ne?!” Na ce, “Eh, Kakana ma dan Shi’a ne, na fada maka!” Sai ya kai min duka. Sai na ce, “Ya “Rasulul Akram!”. Abin mamaki wai sai suke tambaya ta, wai, “Waye Rasulul Akram?” Su wato ba ma su san waye Rasulul Akram din ba. Sai nake ma tunanin to mutanen ma da ba su san waye Rasulul Akram ba ma, ka tsaya ka yi musu bayani, na me? Ai ba za su fahimce ka ba, tunda dai har ba su san waye Annabinsu ba ma.

ALMIZAN: To, daga nan kuma ina suka kai ku?

MALAMA NUSAIBA: Bayan sun kama mu sun dawo da mu cikin garin Kano ne. Burazu guda biyun da suka riga suka rabauta da samun shahada suka kai su mutuware. A gabana aka shiga da su. Shi kuma wannan guda dayan wanda yake cewa shi ba dan Shi’a ba ne, shi kuma suka kai shi ‘emergency’. Ni sai suka taho da ni ‘police station’ da ke Dala, don da yake ni ba ’yar Kano ba ce, ni ban san wajen ba. Sai dai da muka kai wajen, sai na ga ashe wajen kusa da Markaz din Kano ne. Da muka fito daga cikin motar kuma ba ni da hijabi, sun riga sun cire min, sai suka yi ta dauka ta hoto. Wannan ya dauka, wannan ya dauka suna ta zagi na dai haka.

Wani ma da ya zo zai dauke ni hoton, da na kare fuska ta sai ya ce, idan ban cire hannuna ba zai harbi hannun. Sai na ce masa, da kuwa in cire ya dauke ni hoto gwamma ya harbe ni din. Sai yake cewa wai ni wace irin yarinya ce mai taurin kai? Sun kama ni amma ban yi saranda ba. Ni kuma ina ta kokarin nuna musu ba zai yiwu su taba samun abin da suke so din ba (saranda). Suka shiga da ni dai, zagi iri-iri. Sai dai kuma a ciki, sai na hadu da wani dansandan da nake kyautata tsammanin im ma dai ba dan’uwa ba ne, to yana da zuciyar tausayi. Suna ta zagi na, amma shi bai zage ni ba. Daga baya ma shi ya je ya siyo min abinci da ruwa ya kawo min. Sai na ce masa ba ni da bukata. A lokacin kuma ina so na yi sallah, sai dai kuma ga shi sun kwace min hijabina. Shi wannan dansandan har fita ma ya yi ya ce, bari ya je ya gani ko zai samo hijabi a kusa da wurin ya sawo min. To, kuma da ya fita, sai ya dawo ya ce min wallahi bai samu ba.

Sai kusan gab da Magariba haka, da ya tashi tafiya, sai ya zo ya same ni ya ce min, “To, Malama ni zan tafi, kuma ni da dawowa wajen nan sai gobe. Amma na ji abokan aikina suna kishin-kishin din za su ce ki kwana a nan, da safe su sake ki”. Ya ce, “Duk yadda za ki yi kada ki bari ki kwana a nan. Sun kamo ’yan’uwanki, sun hahharbe su, wasu ma sun kashe su. To, ki ce gwanda su kai ki su hada ki da ’yan’uwanki”. Sai na ce masa, “to, na gode Allah ya saka da alheri”. Sai ya ce min, “amma fa kada ki yi musu da wasa, saboda in kika yi musu da wasa to.. Ina fita ki fara dukan kofa, za su zo su tambaye ki meye? Idan sun tambaye ki, sai ki ce ga bukatarki, a kai ki a hada ki da ’yan’uwanki”. Na ce, “to, shi ke nan ba wani abu”. Ya ce, “amma kada na yi idan yana nan, na bari sai ya tafi, saboda idan na yi yana nan zai iya samun matsala a wajen aikinsa.” Nan dai na kara masa godiya, sai ya tafi.

To, yana tafiya na tsaya, na yi wani nazari, na kuma dauki shawarar da ya ba ni din. Na fara dukan kofar, sai suka zo, “Me ya faru?” Sai nake ce musu, “Ai kun kama ’yan’uwana ko?” Suka ce, “Eh”. Na ce, “Kun ma ce kun kashe wasu.” Suka ce, “Eh”. Sai suka tambaye ni, “Kina da aure ne?” Sai na ce, “eh, satina daya da aure”. Sai wani ya yi dariya ya ce, “Watakila ma har mijinki mun kashe”. Sai na amsa masa, “To, in ma kun kashe shi, ai kun kashe shi a kan addini ne, a kan aikin Allah, saboda haka ko kadan ba zan damu ba! Ni ma kaina na so a ce kun kashe ni kafin ku fara kashe shi. Amma kuma idan haka Allah ya kaddara, za ku fara kashe shi kafin ku kashe ni daga baya, to ‘falillahil hamdu”.

Nan dai na ci gaba da dukan kofar suna tambaya ta ina ce musu, “Ai fa dole ku kaini ku hada ni da ’yan’uwana”. Suka yi ta ce min, Mahaukaciya, ba ni da hankali, in ba haka ba gashi suna so su taimake ni, in zauna a wajen in kwana, da safe su sake ni.” Na ce musu, “Ni ba ni da bukata”. Suka yi yin duniyar nan ta yadda za su shawo kaina, na ki yarda. Sun yi, sun yi nace musu, “Wallahi sai sun fita da ni a wajen.”

Da dai suka ga kamar zan tayar musu da hankali, sai suka zo suka bude kofa suka ce na fito, sai na fito. Suka je suka saka ni a mota suka kai ni inda suka kai sauran ’yan’uwan. Suka kai ni ‘State CID’ kuma ana kiran wajen Bompai. Muna shiga wajen, sai suka shiga da ni wani dogon falo, aka yi ta shiga da ni haka, kamar ‘office- office’ ke nan suna ta, “to wannan ma ’yar Shi’ar ce?” Sai nace, “Eh.” Sai su ce, to Allah ya tsine miki, Allah ya yi miki kaza, Allah ya yi miki kaza. Wani ma ya ce, “Ba ku kuka ce za ku yi fada da ’yansanda ba? Za ku san cewa ’yansanda Allah ya tsaya musu.” Ni kuma na ce masa, “Da wanda ya ce zai yi fada da dansanda, da wanda ya ce zai yi fada da addinin Allah, ku fada min wane ya fi wani rashin hankali?” Sai suka yo ca, wani ya daga hannu zai duke ni sai wani yake cewa, “kar ku duke ta, wannan karamar yarinya ce ba ta da hankali, a irin tunanin da aka dora su ke nan.” Sai na ce musu, “Ai ba rashin hankali bane, amsa ya kamata ku ba ni. Idan kuka ba ni amsa, ni ma sai in ba ku amsar maganar da kuka fada min.”

Nan dai suka fara zagin Abba (H) wai, “Idan ba rashin tunani ba, ta yaya zai rika daukar kananun yara da mata? Dube ki, an ce satinki daya da yin aure, amma duba ki ga shi kin fito mun kama ki, wala’alla ma mun kashe mijinki.” Na ce, “Ai bari ku ji, ko iyayena za ku kasha, ku kashe ga baki daya zuri’ar gidanmu, wallahi ba zai dame ni ba.” Suka ce, “Kin ji ko, an dora ki a kan wani tunani na daban, ga shi nan shi ma Abban an kashe masa ’ya’ya guda shida saboda ya ki bin abin da gwamnati take so”. Sai na ce, “to da ya yi abin da gwamnati take so, da kuma abin da Allah yake so, wanne ne ya fi inganci?” Duka suka kasa ba ni amsa, sai suka yi shiru.

Daga nan sai suka fito da ni, suka kai ni cikin wani katon falo. Kana dosar falon ma za ka rika jin wani irin karnin jinni. Ashe duk burazu ne a cikin wajen, kuma har bakin kofa ma buraza ne a wajen, duk sun zube su, babu ma hanyar wucewa. Sai suka ce min in tsallaka burazun in shiga wajen. Sai na ce bazan tsallaka su ba. Ashe wannan burazan da ya rike ni a baya (kafin a kama ni din ke nan), ni ban ma gane shi ba, sai na ji yana ce min ‘sister’ tsallako. Sai na kalle shi, sai ya ce min na tsallako, sai na tsatsallake burazun na shiga ciki.

Na shiga ke nan, sai wani namiji ya zo, wai shi ne zai caje ni. Sai na ce masa, “Ka taba jikina?” Sai yace, “Eh.” Sai na ce, “Ai wallahi uwarka ta yi kadan”. Sai da dai suka ga ba zan bari ba, sai suka kira wata da ke sayar musu da abinci, wai ta zo ta caje ni kada in shigar musu ‘cell’ da makami. Shi ke nan sai na tsaya ta caje ni, daman babu ma hijabi a jikin nawa, sun riga sun cire, ban ma san inda suka yar da shi ba.

Bayan nan ne suka kaini wani daki, duk da basu hada ni da sauran ’yan’uwa ‘sisters’ din da suka kama a ranar ba. A dakin da suka sa ni suka kulle, na samu wasu mata guda uku, muka gaisa da su dai haka. Bayan nan ne, sai daya daga cikin su ta ce min, “Ga hijabina ki saka, amma zuwa da safe za ta karba saboda idan suka gan ki da hijabina da safe za a samun matsala”. Ni kuma na ce mata, “Idan dai za ki bani hijabi yanzu da daddare ne, na saka da safe ki hana ni, ba ni da bukata, tunda dai kin ga yanzu dare ne, kuma kin ce babu wanda ke lekowa dakin nan sai gari ya waye, ga haske ga kowa da kowa, kuma sai na cire na baki, ba zai yiwu ba. Na gode kawai.

ALMIZAN: Su matan da kika tar da a cikin dakin sistoci ne su kokuwa?

MALAMA NUSAIBA:A’a, ba sistoci ne ba. Wasu mata ne na daban.

ALMIZAN: To kenan ke kadai ce ‘sister’ a ’yan’uwan da ke tsare a nan din?

MALAMA NUSAIBA: A’a, akwai wasu sistocin da suka kulle a cikin wani daki daban, amma a dakin da ni aka kai ni ni kadai ce ‘sister’.

ALMIZAN: Amma sun hada ki da sauran ‘Sisters’ din daga baya ko a’a?

MALAMA NUSAIBA: Eh, washe gari da safe wani jami’in tsaron da ya zo yake cewa, a’a, ai wannan ma ’yar Shi’ar ce, ku dauke ta ku hada ta da sauran ’yan’uwanta tunda ga mata a wajen. Lokacin da suka bude suka ce na fito, a lokacin ne na ga wannan burazan, sai yake ce min “Sister’ ba ki gane ni ba ko?” Sai na ce masa, “Afwan, ban gane ka ba.” Sai ya ce min, “Ni ne fa wanda nake rike ki, kina cewa na sake ki din nan.” Sai na ce masa “Ayya wallahi ban gane ka ba ne”. Sai na tambaye shi, “Ya na ga sun saka maka POP a kafa?” Sai ya ce min, “Ai jiyan muna rabuwa, sai suka harbe ni suka kuma taka ni da mota.” Sai na ce, “Subhanallah! Allah ya tabbatar da mu.” Ya ce, “Ilahee”. Sai suka hada ni da sauran ‘Sisters’, su tara, sai na shiga muka zamo goma.

ALMIZAN: Kin lura ko Burazu kuma su nawa ne a wannan lokacin?

MALAMA NUSAIBA:To, da mu da ‘sisters’ da su burazun duka dai da aka kama mu hamsin da bakwai ne, duk da dai na ji ana cewa bakwai din saman ba ’yan’uwa ba ne, abin ya rutsa da su ne kawai, Allah ya kaddara tunda da su ne ma muka yi zaman ‘prison’ sai da suka yi kusan wata shida kafin su fita.

ALMIZAN: Me za ki ce game da tuhumar da ake muku?

MALAMA NUSAIBA: Gasikiya ni kaina ban dai san me muka yi ba, ji na yi wasu suna cewa wai sun ga dansanda a kwance a kasa wai an harbe shi, wai kuma an ga burazu wai sun rike hannu suna hana bin ta inda yake, amma dai ni ban gani ba. Sai da muka je kotu wai sai na ji suna zargin mun kasha dansanda, kuma mun kwace bindigu, wai ko guda biyu a hannun jami’an tsaro. Ni lokacin da ake karanta takardar ma abin dariya ya ba ni, nake cewa, yanzu sharrin nasu ma ya wuce su ce tare hanya, har ya kai ga su kasha dansanda? Allah na nan. Abun da suke zargin mu da shi dai lallai karya ce, sun fadi haka ne don su rudi al’umma, da kuma wala’alla idan sun matsa mana kila mu daina abin da muke yi, mu kuma babu fashi insha Allah.

ALMIZAN: ’Yan’uwan da kika samu a wurin, wanda aka ji wa ciwo, da wadanda aka harba, da wanda aka taka da mota, sun kai su asbiti ne, ko kuwa sun samar musu da Likita ko wani nau’in kula ta lafiya kafin a kai ku ‘prison’?

MALAMA NUSAIBA: An ce dai sun kai su asibiti, amma lokacin ba a kai ni ba, amma dai akwai wani tsohon da suka raunata a cikin burazas din wanda suka ki kai shi asibiti saboda wai mutuwa kawai zai yi suka ce, so babu bukatar ma su kai shi, sai ka ce su ke rike da rayuwarsa. Ni dai tun zuwana babu wata kulawa da ta shafi lafiya da muka samu. Inda suka ajiye mu a Bompai din kwananmu biyu, amma ko ‘Paracetamol’ babu wanda suka saya wa wadanda suke fama da ciwuwwuka daban-daban. Har ma wadanda ke da ’yan kudi a jikinmu muka ba su jami’an tsaron muna rokon su da su sayo musu ko da ‘Paracetamol’ ne ma, amma suka dai nuna mana hakan ba zai yiwu ba. A hakan kuma da suka kai mu kotu, Alkali ya ce a ci gaba da tsare mu har sai ranar shahudu ga watan Disamba.

ALMIZAN: Me ya fi baki tausayi ne tundaga lokacin da aka fara harba wannan ‘tear-gas’ zuwa duk inda aka kai ku?

MALAMA NUSAIBA: Abin da ya fi bani tausayi gaskiya, shi ne marasa lafiyarmu, ana cikin wannan mawucin halin, mu ga mu da lafiya su kuma ba su da ita. Ka ga ko a cikin mu sistocin sun harbi mutum biyar, wanda dukkan su ba su iya yin komai da kansu, sai dai a yi musu. Hatta tashi sai dai a daga mutum saboda babu dama, wasu harbin su a kafa ne. Akwai kuma a cikin mu wata Batula, wadda irin harbin da suka yi mata, duk mai imani ya gan ta sai ya tausaya mata, da kuma wata Khadija Dauda Hadeja. Harbin da aka yi mata abin tausayi, sai da ta yi kwana tara da bullet a cikin kafarta, ba ma a san da shi ba sai daga baya. Ita wannan ta kai kusan wata uku ba ta iya taka kafar ma.

ALMIZAN: Watanku nawa a ‘prison’?

MALAMA NUSAIBA:Watanmu bakwai babu kwana daya.

ALMIZAN: Me kike ji yanzu haka game da abin da ya faru?

MALAMA NUSAIBA: Alhamdulillah, ni dai wannan jarabawa ba abin da ta kara min sai kwarin guiwa, ta kara min dagiya da kuma kwadayin rabauta da madaukakiyar shahada. Tasirin wannan jarabawa nasara kawai gare ni zan ce don ko zaman ‘prison’ din da muka yi zaman lafiya babu wata matsala a tsakanin mu.

ALMIZAN: Wane kira kike da shi ga ita gwamnati?

MALAMA NUSAIBA: Kirana ga wannan gwamnati shi ne, su farga su gane cewa addini ba siyasa ba ne. Kuma lallai babu wata mafita ga kasar nan tamu Nijeriya da ta wuce kiran Sayyid Ibraheem Alzakzaky. Wanda duk suka fahimta hakan, to kamata ya yi su shigo su taimaka masa, ba su tsaya su yake shi ba. Wadanda kuma ba su fahimci kiransa ba, sai mu taya su da addu’a, Allah yasa su gane, su fahimci wane ne Sayyid a wannan nahiya.

ALMIZAN: Wane kira kike da shi ga ’yan’uwa?

MALAMA NUSAIBA: Kira na ga ’yan’uwa shi ne mu kara jajircewa, mu ba da ranmu da lokacinmu wajen tabbatar da addinin Allah. Ya zamanto ’yar’uwa ta ji cewa za ta iya ba da ranta da na ’ya’yanta da iyayenta da komai nata a kan addinin Allah ya kafu.

ALMIZAN: Yaushe za a ci gaba da tuhumar naku a kotu?

MALAMA NUSAIBA: Za a ci gaba ranar goma ga watan bakwai ‘10th July, 2017’.

ALMIZAN: Kasantuwar cewa satinki daya kwata-kwata da yin aure kafin aukuwar wannan waki’a, za mu son jin irin yanayi da kuma halin da shi Maigidan naki, ko in ce shi Angon naki ya samu kansa.

MALAMA NUSAIBA:Tabdijam! Ai kuwa dai gaskiya bai ji wani abu ba, saboda ko ba komai ya san yadda gwagwarmayar addinin nan take. Saboda ko a lokacin da muka rabu ma, irin rabuwar da muka yi mun rabu ne da niyyar haduwa kuma sai a can, to amma kuma Allah bai yi hakan ba. Don kuwa ko lokacin da yake kawo mana ziyara nan ‘prison’ din da ke Kano, gaskiyar magana duk lokacin da ya zo sai dai ya kara karfafa mana guiwa, bai nuna mana kila ko hankalinsa ya tashi ko yanayin zamanmu a wajen, gaskiya bai taba nunawa ba. Sai dai kawai ya kara karfafa mana guiwa, daman haka hanyar take, mu daure, mu cije, mu cinye jarabawar. Yakan fada min irin wannan jarabawar sai bayin da Allah ya zaba yake kawowa wajen, ba kowa da kowa ba. Gaskiya ya taka muhimmiyar rawa, saboda gaskiya idan da wasu ne, to wala’alla da za a iya samun matsala, to amma kuma shi lallai bai nuna komai ba, kuma ya nuna mana cewa duk lokacin da Allah ya yi fitowarmu za mu fito.

ALMIZAN: To, Alhamdulillah, mun gode Malama.

MALAMA NUSAIBA: Ni ma na gode.