AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. Bugu na 1284 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Yadda na samu labarin shahadar ’yata Nusaiba a Gyallesu - Malama Shafa’atu Umar Sakkwato

Daga Ibraheem El-Tafseer


Imam Aliy

Malama Shafa’atu Umar Sakkwato, ita ce Mahaifiyar Shahida Nusaiba Abubakar Abdullahi Sakkwato da Sojoji suka harbe a gidan Shaikh Ibraheem Zakzaky da ke Gyallesu. Wakilinmu Sulaiman Musa Bodinga, ya tattauna da ita, inda ta yi bayani kan yadda labarin shahadar Nusaiba ya riske ta da kuma har ila yau sakonta ga wadanda suka haifar da waki’ar ta Zariya. Ga yadda hirar tamu ta kasance:

ALMIZAN: Muna son ki gabatar da kanki ga masu karatu.

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Sunana Shafa’atu Usman. Muna zaune a nan Halkar Danbuwa Sakkwato.

ALMIZAN: Lokacin da Sojoji suka kai wa ’yan uwa hari a Zariya kina Sakkwato?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Ina nan Sakkwato, sai dai lokacin da abubuwan ke faruwa hankalina duk yana Zariya.

ALMIZAN: Malama kina daya daga cikin wadanda ’ya’yansu suka yi shahada a Zariya, ta yaya kika samu labarin?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Ina zaune a gida lokacin da waki’ar ke faruwa, sai dai ba mu da labari yara sun tafi makaranta. Sai wata ta zo yi min gaisuwar ta’aziyyar wata Yayata da ta rasu. Bayan ta yi min gaisuwa za ta tafi, sai muka raka ta kofar gida muka gaisa da Maigidanta, sai yake ce da mu ba mu san abin da yake faruwa a Zaria ba ne? Muka ce ba mu sani ba. Sai ya ce ana waki'a ne. Yanzu haka har ma an fara samun Shahidai a Husainiyya.

To muna nan haka sai Muntazar ya kira abokiyar zamana da wata waya, ya ce da ita; “Umma komai na yi maki ki yafe min, don muna nan a Husainiyya Sojoji sun kewaye mu, harbi suke yi ta ko’ina”. Sai na kira wayar da Muntazar ya kira na ce ina Muntazar, sai shi yaron da ya dauki wayar ya ce ba su tare da shi yanzu, amma in ya gan shi zai ba shi. Sai kuma na kira ita kanwar Nusaiba, Suhaila, na ce mata me yake faruwa? Ta ce; “Mama ai ni ina gida da muka dawo daga makaranta ban tafi Husainiyya ba. Amma dai Nusaiba na can ita da Muntazar”. Nan da nan kuma na kira Jamila Mukhtar Dankwarai na tambaye ta ko ta ga Nusaiba? Sai ta ce min ga su nan tare, ko ta ba ni ita? Sai na ce, eh ta ba ni ita mu yi magana.

Ta ba ta waya muka yi magana. Take cewa; “Mama muna nan Gyallesu bayan mun dawo daga makaranta, mun nufi hanya mun tafi Husainiyya, ko da muka zo sojoji sun datse hanya, amma Muntazar yana ciki”. Da muka ji haka sai ya zama daidai lokacin Muntazar din muke tausaya wa shi da sauran ’yan uwan da ke cikin Husainiyya. Lokaci-lokaci sai in kira Jamila wani lokaci sai ta ce min ba su tare da Nusaiba, har zuwa lokacin da Sojojin suka shiga Gyallesu.

Wani lokaci in na kira Jamila sai ta ce min ba su tare da Nusaiba, tana jin tana can tare da yara. Sai na kira wayar wata da Nusaiba ta kira ni da ita, sai ita ma ta ce min yanzu ba su tare da Nusaiba. Daga baya in na kira wayar ta yi ta ringin ba a dauka. To, ni duk lokacin hankalina bai ba ni ba, duk ina jin yanayi marar dadi haka a jikina. Sai na zo na yi alwala na shiga daki, sai na ji abokiyar zamana tana waya na ji ta ce, Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Sai kuma na ji tana cewa eh tana daki. Da na ji haka ni kuma sai na fito na ce mata me ke faruwa? Ta ce min in bari ta zo. Tana ta kewaya tana fitowa, ta yi shiruu! Sai ta ce min ki zauna. To ni tuni na fahimci lallai akwai abin da ya faru. Sai na ce mata ni ko ma mene ya faru ki fada min. Sai ta ce min Nusaiba ce aka ce an harba, sai dai tana jin a hannu ne, ko a kafa. Na ce mata ke ba ki Gyallesu, Malam shi ma ba ya Gyallesu, ta ina kuka san inda aka harbe ta? Sai na kira Jamila ita ma sai ta so ta boye min. Sai na ce Jamila me za ki boye min?

Allah ne ya ba ni ita, kuma lokaci ya yi da ya ga dacewar karbar abarsa. Jin haka da na ce sai ta ce; “Shafa’atu ki yi hakuri, Nusaiba Allah ya azurta ta da samun shahada. Yanzu haka ina kan gawarta”.

Muna nan sai muka ga an saka hoton a Facebook, cikin wadanda suka yi shahada. Sai Mahaifiyata da wasu da suke gidan suna muhawara kan cewa ba ita ba ce, ni kuwa ina dubawa na shaida Nusaiba ce. Ka ji yadda aka yi.

ALMIZAN: Ko za ki iya tuna maganar karshe da kuka yi da ita kafin ta yi shahada?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Maganar karshe da muka yi da ita, akwai wayar wata da suke tare ta yi min 'flashing', na kira wayar, sai ta ce min ba su tare yanzu, amma in ta gan ta za ta ba ta. Ina nan sai aka yi 'flashing' na kira. Sai ta ce; “Mama Nusaiba ce”. Na tambaye ta wane yanayi ake ciki yanzu? Har nake ce mata ko za ta samu damar wucewa gida? Ta ce; “Mama daga nan Gyallesu muna jin karar harbin da Sojoji suke yi a Husainiyya, ku yi mana addu’a don sun datse duk hanyoyi”. Wannan ce maganar karshe da muka yi da ita.

ALMIZAN: Galibi ku iyaye kun fi shakuwa da ’ya’ya musamman mata, me za ki ce a kan halayyar Shahida Nusaiba?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Hakikanin gaskiya Nusaiba tana da halaye na kwarai, kusan duk yaran da suke gabana Nusaiba ta dara su ta janibobi da dama. Tana da lura kwarai, kuma akwai ta da tausayi, musamman na kananan yara, da yawa ko wani abu ta kai da na fito na dube ta kai tsaye, sai ta fahimci ina nufin wannan abin da take bai dace ba, sai ta bari, ba sai na buda baki na yi mata magana ba. Allah ya jarrabe ni da rashin lafiya, Nusaiba tana kula da ni sosai da tausaya min a kan wannan lalura din, ko yaushe tana kaina. Wani lokaci sai in yi barci in farka sai na gan ta zaune kusa da ni tana karanta min wasu addu’o’i. Har ma sai na ce Nusaiba ba a kwanta ba? Irin wannan halayyar tata ne bayan faruwar lamarin, wani lokaci sai in dan ji wani abu haka, tunani na rashin ta, amma kadan-kadan Allah ya sa wannan tunanin ya bar tsaya min a zuciya.

ALMIZAN: Akwai wasu da dama da suka rasa ’ya’yansu a wannan waki’a ko akwai wata shawara da za ki ba su?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Shawara ko maganar da zan yi a kan wannan shi ne ga su wadanda kilan wannan waki’ar ta shafa kamar matan da suka rasa mazajensu, ko ’ya’ya, su ci gaba da hakuri, kuma su kalli Jagoran Harka, don in har suna juyayin rashin da suka yi, to shi ’ya’yansa nawa ya rasa? Duk da yake shi na daban ne, ba ruhinmu daya da shi ba, ’ya’yansa ma ba kamar naka ba ne, amma dai kana duba jarabawar da ta sami na gabanka wanda ka san ta fi taka zafi, duk da dai wannan jarabawa ba a saba ganin irin ta ba, amma da haka din in an jure aka dake, to akwai nasara gaba. Don haka ina kira ga iyayen da waki’ar ta shafa kada ki ce an kashe mijinki kilan kin yi sabon aure ba za ki fito wajen taron addini ba, a kashin gaskiya ba mu gaji haka nan ba. Ba mu gaji tsoro ba. Malam Zakzaky (H) a wani jawabinsa yake cewa za mu haifa su kashe, za mu yi gini su rusa, wata rana za su kashe mu, wata rana za mu yi galaba a kansu. Don haka wannan yanayin da abubuwan da ke faruwa a yanzu alamu ne na bayyanar Limamin karshe, Imam Mahdi (AF). Fatanmu Allah ya tabbatar da mu.

ALMIZAN: Kyawawan halaye da tarbiyya sune tubalin farko da mutum zai iya kai wa ga samun matsayi na shahada, me za ki ce kan rawar da Maigidanki yake takawa wajen ba ’ya’yanku tarbiyya?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Gaskiya maigidanmu yana iya kokarinsa wajen sauke nauyin da yake kansa na bai wa ’ya’yanmu tarbiyya. Unguwar da muke ba ma tare da ’yan uwa sosai, hakan ya sa mutane na ganin Maigidanmu yana tsanantawa, ko yana da tsattsauran ra’ayi. To, mu kuwa da yake mun san abin da yake nufi, ba mu taba jin wata damuwa ba, ai ba shi ne ya sa su wannan abin da yake umurtar su su yi ba, umurnin Allah ne. In ka gina yaronka kan hanya ta gari kai za ka ji dadi, in kuwa ka bar shi ya lalace ba ka kula ba, kai ne za ka shiga damuwa.

ALMIZAN: A harin da Sojoji suka kai sun kashe mata da jarirai, abin da ba a saba gani ba, wasu na ganin sun yi hakan ne don su tsorata ku, ku daina karfafa ’ya’yanku a kan wannan Harka me za ki ce?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Ina! Ko kadan ba mu tsorata ba, ba mu kuma samu rauni ba. Muna nan a kan wannan Harka, mu da ’ya’yanmu, ba gudu ba ja da baya. In suna ganin sun kashe mana ’ya’ya sun kashe mana mazaje a kan wannan Harka din don su tsorata mu a banza, wadanda suka kashe din Allah ne ya ba mu su, in kuma ya karbi abin sa ta wannan hanya din ba mu yi hasara ba. In mun yi hakuri kan rashinsu da muka yi daukaka ce gare mu. Fatanmu Allah ya ba mu shahada kamar yadda wadannan ’yan uwan namu suka yi shahada.

ALMIZAN: A naki tunani ya kike kallon makomar wannan gwamnati da ta yi wannan ta'addanci mai muni ga yan'uwa?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Wadanda suka yi mana ta’addancin dai ba zan ce su ji tsoron Allah ba, don na san ba tsoron sa suke ji ba, sun yi abubuwa masu muni a kanmu, sun ci zarafin mu matuka, muna da yakini makomarsu ba mai kyau ba ce. Allah Ta’ala, yadda suke ganin sun yi amfani da karfi sun tarwatsa mu, Allah ya tarwatsa al’amarinsu. Ba za mu daina fadar zaluncin da suka yi mana ba. In sun fito sun harbe mu da bindiga muntane sun gani, mu kuma za mu yi ta yi masu addu’a da nufin Allah ya daukar mana fansa. Muna kara kai wa Allah kuka, yadda suka tarwatsa gidaje, suka dauke miji suka bar mata, suka dauke uwa suka bar ’ya’ya, suka dauke ’ya’ya suka bar iyaye, ka yi mana sakayya da hakan, ya kwace mulkin daga hannunsu suna kaskance. Wannan shi ne abin da zai faru da su insha Allahu.

ALMIZAN: Ganin har yanzu gwamnati na tsare da Shaikh Zakzaky da Almajiransa, wane kira kike da shi?

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Kiran da nake da shi ga gwamnati shi ne ta gaggauta sako mana Jagoranmu da maidakinsa da sauran ’yan uwa da suke tsare da su. Wasu daga cikin su matasa ne dalibai, su sako su, su dawo su ci gaba da karatunsu, sa’annan a dawo zancen biyan diyyar jinainan ’yan uwanmu da ke kansu.

ALMIZAN: Mun gode.

MALAMA SHAFA’ATU USMAN: Ni ma na gode kwarai.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron