AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. Bugu na 1284 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Kisan kiyashin Sojoji a Zariya: Har yanzu akwai harsasai 5 a jikina - In ji Zainab Sa’id K/mashi


Maulid Sayyada Fatima

Zainab Sa’id, wadda aka fi sani da Zainab Kurmin Mashi Kaduna, tana daya daga cikin Harisawa mata, kuma tana daya daga cikin ’yan ISMA masu ba da gudummawa a bangaren lafiya a Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky.

Tana cikin wadanda harin da Sojoji suka kai wa ’yan uwa a Zariya ya rutsa da ita, a inda aka yi mata ruwan wuta a kafafunta, kuma suka kona ta da wuta. Wakilinmu Abdullahi Yusuf Sambo Richifa ya samu zantawa da ita, kuma ta zayyano masa yadda lamarin ya faru da ita, da yadda ta kubuta daga harin. Ga dai yadda hirar tasu ta kasance.

ALMIZAN: Da farko za muso ki gabatar da kanki ga masu karatunmu.

ZAINAB SA’ID: Ni dai sunana Zainab Sa’id. Amma an fi sanina da Zainab Kurmun Mashi.

ALMIZAN: To da yake waki’ar Zaria ta faru a kan idonki ne, ko za ki gaya mana yadda ta rutsa da ke?

ZAINAB SA’ID: Lokacin da waki’ar ta fara, ina nan Kaduna na samu labari. Malam Awwal K/mashi ya kira ni ya ce na san abin da ke faruwa a Zariya? Sai na ce masa lallai ban sani ba. Shi ne ya ce mun ga Sojoji can sun je Husainiyya Bakiyyatullahi, kuma yanzu haka ma an samu wurin Shahidai mutum goma. Ya ce min, su yanzu haka ma sun kusa shiga Zariya. Sai na ce masa, to insha Allah mu ma muna nan shigowa.

Daga nan ne sai na shirya sai na zo na sami Baban Muhammad (Maigidana ke nan), na ce masa kana da labarin abin da ke faruwa a Zariya? Na ba shi labarin halin da ake ciki. Sai na ce masa, to ya za a yi ke nan? Ni ina so na tafi Zariyan ne. Sai shi ma ya ce yana so ya je. Sai na ce za mu tafi tare ne, ko ko ya za a yi? Sai ya ce tafiyarmu ba za ta zo daya ba. Saboda ba mu san ya yanayin garin yake ba. Daga nan ma kawai shi ya shirya ya tafi. Ya ma riga ni fitowa, saboda na tsaya ina dan shirya kayana.

Na zo bakin titi na samu mota na nufi Zariya. Na shiga Zariya kamar karfe 7:00nd saura dai kadan. Da na shiga Gyallesu sai na kira Baban Muhammad na ce masa yana ina ne? Ya gaya min inda yake. Haka dai muka yi ta waya da shi. Sai can ya kira ni ya ce in fito mu hadu da shi a waje. To da na fito, shi ne yake tambayata ko na zo da rigar sanyi a cikin kayana? Soboda zazzabi ya kama shi a lokacin. Sai na ce masa ai ko ban dauko rigar sanyi ba. Suna tare da abokinsa wani dan da ake kira Awwal a lokacin. Ya ce, to bari su je neman rigunar sanyin, da yake ranar an yi sanyi sosai. Can sai ga shi sun dawo. Ya ce mun ba su samu ba. Sai na ce masa to ko za shi gida ne kawai gobe ya dawo tunda yana zazzabi. Sai ya ce min bari su je wurin mai shayi su sha tea, wata kila su daina jin sanyin. Sai ya sha magani.

To, sun je ba su sami shan shayi ba ma, sai ya kira ni ya ce zai wuce gida gobe ya dawo. Bayan wani lokacin sai na kira shi a waya nake gaya masa Sojoji sun zo Gyallesu. Ya ce min a lokacin ma ya shiga gida ke nan yana bude kofa zai shiga daki. Sun zo Gyallesu kamar karfe 10:00nd da ’yan wasu mintina. A lokacin ma muna tare da Malama Jamila Mukhtar Sahabi da su Sister Jummai Ahmad Karofi, muna cikin gidan Farfesa Abdullahi Danladi a lokacin. Daga nan sai muka fara jin karar harbi. Ana cikin haka sai ga wata Sister ta shigo take cewa Sojoji sun zo har ma sun fara harbi.

Shi ne kawai sai muka fito muka doshi wurin. A lokacin ma har an fara kawo Shahidai. Shi ne sai muka fara kabbara a wurin. Can sai aka ce mana, an harbi wata Sister, sai aka ce lallai ’yan uwa mata su je su dauko ta. Da ni da Hawwa ’Yar Masana da wata Hajiya Habiba, sai na ce mu je mu dauko ta. To mun doshi wajen, sai muka ga har wasu Sistoci sun riga sun dauko ta. Sister din da aka harba ita ce Shahida Nusaiba Sakkwato.

A nan sai muka karbe ta muka shigar da ita gidan Harisawa. Mun juyo za mu fita, sai wani dan uwa ya ce cikin Sistocin nan in akwai ’yan ISMA, to su taimaka su zo, saboda yanzu an fara kawo Sistoci. Shi ne sai na yi wa wata Hawwa magana na ce mata yanzu ya za a yi? Shi ne sai ta ce mun to mu tsaya mu ba da gudummawa. Shi ne sai muka hadu da wata ’yar ISMA guda daya a wurin. Ana cikin haka ma sai na ga an shigo da Nuriyya Birnin Yaro, ita ma an harbe ta. Haka dai aka yi ta shigo da ’yan uwa ana kula da su. Haka dai muka kwana cikin wannan yanayin. Kamar kafe 3:30nd, mun ji sun dan lafa da harbin. A lokacin ne sai na ce wa ita Hauwan bari mu fita.

Da muka fita sai na ga wata Sista ana ce mata Jamilan ’Yan Kwari, muna zaune da ita haka, sai muka hango Malam Muhammad Turi na tahowa ta wurin Banadin. Shi ne sai ya tara ’yan uwa yana mana jawabi. Ya gaggaya wa ’yan uwa abin da ya kamata su yi, kuma ya ce duk abin da mutum zai yi to, ya yi shi don Allah. Ya ce saboda yanzu mauna marhala ne wanda komai zai iya faruwa da mutum. Don haka ’yan uwa su zama masu ikilasi, mu ba Jagora kariya iyakar iyawarmu. Da dai sauran nasihohi da dama da ya yi.

Daga nan da muka dan yi gaba, sai muka hadu da Sista Jummai Ahmad Karofi da kuma wata Mama. Muna zaune a cikin wata ’yan rumfa, kawai sai ga shi sun dawo da harbi, harsashi kawai sai sauka yake yi yadda ka san ruwan sama, da sun dan ga hasken waya an kira ’yan uwa, za su bude wa wurin wuta ne kawai. Haka dai muka kasance a wurin har zuwa Sallar Asuba. Shi ne sai na ce wa wadanda muke tare a wurin su zo mu je mu yi Sallah. To, da muka je yin Sallah, sai na ce wa Duduwa in tana da ruwan zafi ta ban in wanke hijabina, da yake gaba daya hijabin ya baci da jini a lokacin.

Bayan mun yi alwala mun fara Sallah ne, kawai sai muka ji karar harbin ya fi na farko, ma’ana sun karo wani karfi ne sosai. Daga nan dai mu kai sauri muka idar da Sallar. Sai nake ce wa Jamila tashi mu fita. Nan muka bar su Asma’un Malam Muktar Sahabi suna Sallah. Daga nan sai nake ce wa Shahida Hajiya Habiba, to mu mun fita, inda rabon mu gana, to in kuma mun yi shahada, Allah ya kaddara saduwarmu.

Daga nan dai muka fita. Ga shi sun karo karfi, kawai debo Shahidai ake yi. Muna cikin haka sai ga Hauwa ’Yar Masana, ta zo tana ce min; “Zainab masu rauni fa mata sun yi yawa sosai, saboda haka ya kamata ki zo mu ci gaba da duba su”. Shi ne sai muka tafi muka ci gaba da kulawa da wadanda aka harba. Har zuwa kusan kamar karfe 9:00ns ranar Lahadi. Sai ga Mami Badidko ta shigo, take ce min “Zainab ba mu ga fa Hajiya Habiba ba, kuma na kira numbarta ba ta daga ba”. Ni ma sai na gwada kiran numbarta, sai dai ta yi ta ringing, amma ba za a dauka ba. Sai na ce bari in je in duba ta. Na fito zan fita sai wani dan ISMA ya ce; “Malama kin ga dazu kun fita nan, amma ba dukkan ku kuka dawo ba, wasu sun yi shahada, saura ku biyu kawai kuka rage. Yanzu kuma ga shi za ki kara fita. Nan din ma fa aiki ne a gabanmu”. To, shi ne sai na hakura muka ci gaba da aiki.

Zuwa can sai ga shi an shigo da Shahida Wasila Marabar Jos, a lokacin an harbe ta a kafa, shi ne sai na yi mata allura, na kuma wanke mata wurin. Sai muka ajiye ta a gefe. Sai na ce mata Wasila tunda ke ma ’yar ISMA ce, ki dauki wance ‘hand glove’ din a cikin kwali ke ma ki taimaka da aiki saboda ina so zan fita ni ma.

Daga nan ne na fito muka ci gaba da kabbara, sai suka harbo mana gurneti, sai na kwanta na shiga karkashin wata mota. Sai suka kara jeho wani, ko da na dago kaina na kalli ’yan uwan da muke tare da su a wurin, sai na ga duk sun kone, wasu kuma namansu ya yi daga-daga. Daga nan ne sai muka yi baya, muka koma wajen tiransifoman gidan Malam (H), muka tsaya. A lokacin wuraren karfe 10:ns saura. To, muna tsaye a wurin kawai sai suka kara jeho mana wani gurnet din ya tarwatse. Suka kuma danno mu da harbi ba kakkautawa. A nan ne kawai sai na ji wani Buraza ya ce; “Malama jini yana zuba a kafarki”. Sai na duba haka, sai na ce wa wata Sista da take kusa da ni ai ko an harbe ni. Sai ta kara duba mun wajen, sai ta ce mun kwarai kuwa, ga shi nan har waje biyu ne ma jinin ke zuba a kafar. Sai wannan Buraza ya ce a dauke ni a shigar da ni gidan Harisawa. Sai na ce mai ko ma an shiga da ni gidan Harisawa kayan aiki sun kare, saboda allura daya ta rage kafin in fito daga wurin, kuma na yi wa wata Sista kafin in fito. Muna cikin haka sai suka kara jeho wani gurnet din, shi ne wanda ya daki jikin ginin gidan Abba. To, a daidai wannan lokacin kawai faduwar da na yi, sai na murgina cikin kwata. Zuwa can da na dago kaina sai na ga mutanen da muke tare da su duk sun kone. To, daga nan ne sai na ga Hawwa ’Yar Masana a bayana, sai ta ce; “Zainab zo mu shiga gidan Harisawa”. Sai na ce ta taimaka mun da hijabinta guda daya, sai na cire wanda ya baci da kwata, sai na sa wanda ta ba ni, sannan kuma ta yagi dan kwalinta ta daure mun inda jinin ke zuba a kafata waje biyu. Sai muka shiga gidan Harisawa. Ta ce amma ita za ta fita.

A lokacin na iya hango Malam Mukhtar Sahabi yana ce wa ’yan uwa; “Malam Turi ya riga ya yi shahada, don haka masu karamin rauni su fito su ba da gudummawa”. To, da na ji haka, sai na fara jan kafata zan fito don ba da gudummawa, sai wani dan ISMA ya ce Malama kawai ki yi hakuri ba za ki iya ba, sai na ce masa haka nan dai za mu fita har su karasa mu. Sai ya ce Malama don Allah ki yi hakuri ba za ki iya ba. To, da na ji haka shi ne sai na hakura, na jingina a jikin wani benci jini na ta zuba ya ki tsayawa.

To muna nan zaune dai haka, sai ga su Bilkisu Malumfashi, duk su ma an harharbe su. Muna cikin haka sai ga su Kubura sun shigo gidan Harisawan, wai ashe lokacin duk Sojoji sun mamaye wurin ne. To, ana cikin haka kawai sai muka ji maganar Sojojin a nan jikin gidan Harisawa za su shigo. Sai na ce wa wadanda muke tare da su mu kwakkwanta. Muna cikin wannan halin sai Sojojin suka fara sanarwar a fito a yi saranda, in ba haka ba za su sa wa gidan wuta. Wai duk mai rai ya fito ya yi saranda. Mu kuma muka ki fitowa mu yi sarandan.

To, ana cikin haka ne kawai sai muka ji wuta na cin gidan, ba mu san ya aka yi suka saka wutar ba, ko fetur ne suka yi amfani da shi, ko mene ne, mu dai kawai mun ji wuta ta kama ne kawai ko ta ko’ina. Sai na ce ma su Nurayya ku tashi mu fita mu koma tsakar gidan. Muna fitowa tsakar gidan sai muka hangi Malam Mustapha Potiskum ta can wurin bayi, yana ciccire wa ’yan uwa robar da aka yi masu karin ruwa da ita, saboda wuta ta kama robar tana fado masu a jiki don kar wutar ta kona su.

A lokacin ga wuta gaba daya ta kama gidan, amma suna kara ba da sanarwar mu fito mu yi saranda. Duk da haka ba wanda ya fita. A lokacin Malam Mustapha yana ce wa ’yan uwa su yi hakuri su daure, in ma mutum ya yi shahada rai yana fita shi ke nan zai daina jin zafin.

A lokacin muna tare da wani Haris ana ce masa Malam Abdullahi, dan Buruku ne, har yake ce min; “Malama Zainab ashe ke ma an hahharbe ki a kafa?” Na ce masa eh. Muna cikin haka, kawai sai muka ji su ta saman makwabtan gidan, kawai sai harbi fafaa-fafaa ba kakkautawa. A lokacin muna tare da wata Hawwa, ita ma ’yar nan Kaduna ce. Sai nake ce masu su kwanto a jikina, sai Hawwan take cewa; “Aunti Zainab akwai fa harbi a kafarki”. Na ce mata duk da hakan, kuma kar ku sake ku je ku yi saranda gare su.

To, a wannan lokacin da harbin ya lafa sai na ga duk an harharbi mutane, wadanda ma suka shigo daga baya ba harbi a jikinsu, su ma duk an harbe su, wadanda kuma suke da harbi an kakkara musu harbin, ni ma kawai sai na ji sun dagargaza mun kafata ta dama har ma ta kakkarye. Don da harbi biyu suka yi min a kafar hagu na kawai. Ga kuma wuta ta kama jikina tana ci. Haka muka kasance a wannan halin har dare ya yi.

A wannan lokacin ne Bilkisu Mulumfashi take ce min; “Aunti Zainab za mu sha ruwa, idan ba mu sha ba za mu mutu”. Sai na ce mata ku yi hakuri ba inda za a samu ruwa. Akwai wani Yasir dan Funtuwa, sai ya ce; “Aunti Zainab mu yi tawassili, za mu fita mu samo muku ruwa”. Shi ma hannunss daya ya karye sakamakon harbin da aka yi masa. Sannan akwai harbi ma a kafarsa, amma dai na kafan bai karye ba. Suna tare da wani Mansur, shi ma dan Kaduna ne. Bayan mun gama tawassuli, sai suka fita ta baya suka haura ta gidan wasu mutane. To, shi ne suka je suka samo mana ruwa ba mai yawa ba suka kawo mana. Shi ne sai aka samu aka babba su suka dan shassha, cikin su har da wata Fatima Aminu Mai Hoto, ita ma ta yi Shahada daga baya a Asibitin Shika.

To, bayan haka sai Yasir din ya kara ce min; “bari mu je mu duba mu gani in akwai hanyar fita, sai mu ga ya za a yi a fitar da mutanen da ba su yi shahada ba, tunda ni karaya ta a hannu ne ina ganin za mu dan iya yin wani abu”. Har nake ce masa ba za ka iya ba tunda hannunka a karye yake, gara ma Mansur tunda shi gogansa kawai harsashin ya yi a kafa. Ya ce; “haka nan dai za mu duba mu gani Aunti Zainab”.

A wannan lokacin kawai suna fita sai muka ji sun bude masu wuta. To, wai ashe suna gudu suna harbinsu ne a lokacin, sai suka shige wani gida suka boye a kicin din gidan. To, shi ne ma har nake ce wa Bilkisu da Muhammad dan gidan Muhammadu Buhari, shi ke nan su Yasir sun yi shahada. A haka dai muka kasance har gari ya waye, wuraren karfe 8:30ns sai muka fara jin hayaniyar mutane a waje. Zuwa can kawai sai ga wasu ’yan iskan gari sun shigo, sai suka same mu mana kwakkwance. Da yake shi Muhammad Buhari yana ta kalmar shahada. Sai suka ce; “da ma a cikin ku akwai wadanda ba su mutu ba? To bari mu je mu kira su Oga su karasa ku”. Shi ne sai suka je suka kirawo Sojojin. Da suka shigo duk wanda suka ga akwai sauran numbashi a tare da shi kawai sai su yi ta caccaka masa wukar bindiga.

Bayan sun gama caccaka masu wukar sai suka fita. Muna cikin wannan halin har zuwa kusan karfe 4:00ny. To, cikin wadanda muke kwance a wurin sai na ji wani dattijo ya kira wani suna waya. Bayan da ya gama ne sai nake ce masa Baba kai wayarka tana nan ba ta kone ba? Sai ya ce eh. Sai ya tambaye ni ya ce; “ke daga wane gari kike?” Sai na ce masa ni ’yar Kaduna ce. Sai ya ce mun kin san wani Ya’u Liman? Sai na ce eh na san shi. Sai ya ce min ya sunanki? Sai na ce masa Zainab. Sai ya ce; “yanzu in na kira shi na ce masa Zainab zai gane ki?” Sai na ce masa ka ce masa Zainab Kurmin Mashi zai gane ni. Da ya kira shi sai ya gaya masa muna tare a gidan Harisawa. Shi ne sai Ya’un ya ce, to mu yi hakuri ’yan Red Cross suna nan shigowa unguwar.

A lokacin ne ma har ya kira Baban Muhammad yake gaya masa halin da muke ciki. Don su sun dauka ma na riga na yi shahada, saboda wayata ta kone a lokacin. To, zuwa can sai muka ji suna ta iho, kuma muna jin jiniyar ’yar Red Cross din, wai ashe sun zo ne, sun hana su su gudanar da aikinsu. Zuwa can sai muka daina jin jiniyar tasu. To, ana cikin haka sai muka ji motsin Sojojin a gidan Malam (H), wai ashe lokacin suna dibar gwawwawakin ’yan uwa ne. Bayan haka kuma mun ji suna ta share gidan. Wai ashe suna share jinin da ya zuba na ’yan uwa ne.

To, mu dai muna nan a kwance haka sai muka ji shigowarsu inda muke. To, shi ne ma har nake ce wa Dattijon nan, lallai yanzu za mu yi shahada, nake ce masa lallai kar mu yadda mu ce za mu yi masu saranda. Ban ma gama rufe baki ba kawai, sai ga sun shigo, kawai sai na tashi na zauna.

To, shi ne sai wani Soja daga cikin su yake mamaki, yake cewa; “dama akwai masu rai a cikinku?” Yake cewa; “yanzun nan za mu karasa ku. Za mu farfasa maku kai da harsashi”. Sai na ce masa ai dama karasa mu za ku yi, tunda kun harbe mu a jikinmu ba iyaka, kun kona mu da wuta. Na ce don haka ko ka fasa mana kai da harsashi dama karashe ne. Sai kawai ya fara yi min ashariya yana cewa za ki gaya mana maganar banza ne.

Muna cikin haka sai ga wani Soja ya shigo, sai ya ce duk masu rai su tashi su fita waje. Sai nake ce masa cikin mu nan babu wanda zai iya fita da kafafuwansa, saboda duk yawancinmu harbi ne na kafa, kuma duk kafafunmu a karye suke. Sai ya ce masu su je waje su dauko abin daukan marasu lafiya. Sai suka je suka dauko, suka ce mu hau. Shi ne na yunkura zan hau kawai sai na ji ba zan iya hawa ba saboda kafafun duk a karye suke, kuma sun yi min nauyi. Sai suka daga min kafafun na samu na hau suka fita da ni. Daga tsaye ma suke juyar da ’yan uwa a kasa ba ruwansu da karayar da ke jikin mutum.

A nan dai suka gama tara mu, ’yan uwan da muka rage gaba daya a lokacin mu 11 ne. Shi ne sai suka ce kowa ya kife cikinsa ya kwanta. Na ce masu ni gaskiya a halin da nake ciki ba zan iya kifa cikina ba saboda ba na iya motsa kafata. Sai wani a cikinsu ya ce a kyale mu.

Muna nan dai a wurin, su kuma suna ta shiga suna kwaso gawawwaki, suka tattara su a mota suka tafi da su, kuma a cikin Sojojin ma mun ga fararen fata wadanda ma ba ’yan nan kasar ba ne.

Bayan sun gama kwashe Shahidan ne, sai suka juyo kanmu suna ta dukan mu, suna ta tambayar mu a ina muke? Da suka tambaye ni na ce masu sunana Zainab daga Kaduna Kurmin Mashi, sai suka ce karya nake, wai daga ganina irin wadanda Zakzaky yake yo hanyarsu ne daga kasar waje, wai ni ba ’yar kasar nan ba ce. Na ce masu lallai ni ’yar kasar nan ce, a Kaduna ma aka haife ni. Sai suka ce min wai sai na nuna masu inda ‘underground’ din Malam yake. Sai na ce masu lallai ni yanzu ma na taba jin wannan maganar a bakinku. Sai suka ce zan gaya masu gaskiya ko dukan da suka yi min bai ishe ni ba ne, sai sun fasa min kai da harsashi! Na ce ko kashe ni za ku yi, sai dai ku kashe ni, abin da na sani nake fada. Suka ce ke nan ba za ku gaya mana gaskiya ba ko? Nan dai suka dinga dukan ’yan uwa har zuwa wureren 10:00nd. Sai suka zo da mota suka kwashe mu zuwa bariki.

Da muka zo bariki sai suka watsar da mu a tsakar wuri, ga sanyi kuma ana yi sosai ranar. Zuwa can sai ga wani ya zo yana haska mu da cocila. Sai suka je suka kira wani Soja Likita a cikin su, shi ne yake tambayar mu da ina da ina muka ji ciwo? Muka gaggaya masa. Da ya duba ni sai ya ga wasu harsasai sun kunkumburu ta cikin naman kafata, sai ya ce; “ki yi hakuri yanzu za mu zo mu cire miki harsasan nan da suka kumburo waje”.

To, da suka zo sai suka taho da allura za su yi min, sai na ga jikin sirinjin duk jini ne haka, sai na ce masa ya za a yi ka min allura da sirinjin da yake duk jini? Sai yake ce min; “ai ’yan uwanku muka yi wa amfani da shi. Don haka in ma wata cuta ce sai ku kwasa, tunda ’yan uwanku ne”. Sai na ce masa lallai ni ba za ka min aiki da wannan ba. Sai ya ce min; “lallai ko da shi zan yi maki, don a kanku ba za mu zauna muna barnar sirinji ba, don sirinji biyu kawai muka ware za mu muku amfani da su”. Sai wani Soja ya ce; “ke ki juya a maki alluran nan ko na harbe ki”. To, daga nan sai na juya suka min. Zuwa can sai ga shi ya zo aska (zabira), ba su mun allurar kashe zafi ba a wurin, kawai ya kama farde mun kafa, yana ciro wadannan harsasan da ke kafar, sai jini ne kawai ke zuba.

Da ya gama cire min har da jeho mun wani harsashi wai; “ga shi nan in ba ki mutu ba ki nuna wa ’ya’yanki!” Ni ko na dauka na aje din, a yanzu haka ma yana nan na ajiye shi”. Zuwa can da wani ya gan ni a zaune, kuma ya ga halin da nake ciki sai ya je ya samo kananan katakaye ya hada ya daure mun kafar, ya ce za ki dan sami sauki wurin motsa kafar. Daga nan sai suka kawo mana ruwa a cikin robar magani da wani dan guntun burodi, wanda ni gaskiya ban gane wa yanayin ruwan ba, sai na ki sha. Sai wani Sojan ya ce; “kar ki sha din, za ki mutu da yunwa kuwa”. A haka dai muka kwana a waje cikin sanyin nan.

Da safe sai muka ga ’yan Red Cross din sun zo. Suna zuwa suka kama masu ihu, Ogan ya ce in ba ku fita ba za mu bude maku wuta. Sai muka ga sun juya sun fita. Muna nan dai a wurin, sai ga mai sharar wurin ta zo, take cewa mu yi hakuri gaskiya an zalunce mu. Sai na ce mata ba komai wannan abin jarabawa ce a addini. Shi ne sai take ce mun “ya na ga bakinki duk ya bushe, kuma ya tsattsage haka?” Sai na ce mata yau kwanana uku, ba ci, ba sha. Sai ta ce bari na kawo maki ruwa ki sha. Sai na ce mata ta bar shi kawai. Haka dai ta dage sai da ta kawo min ‘pure water’ guda daya. Sai na aje shi a gabana. Daga nan sai ka ga wannan Sojan ya zo ya maka tambayoyi, ya yi isgili yadda yake so, ya sa kafa ya shuri mutum. Wani ma ya zo. Haka dai suka yi ta yi mana.

Ana cikin haka sai ga wani ya zo ya ce min na cire wannan zoben azurfar da ke hannuna, ko ya sa wuka ya datse min dan yatsan. Sai na cire na aje shi a gabana. Sai ya sa kafa ya yi kwallo da shi ya fada kwata. Haka dai suka ci gaba da yi mana isgili har suna cewa wai har gumaka sun gani Husainiyya, kuma sun ga jini yana kwarara a Husainiyya. Wai muna shan jini muna tsafi. Na ce masu mu wannan duk a bakinku muke ji. Na ce masu don Allah su taimaka mana da ruwa za mu yi Sallah. Shi ne sai suka ce dama muna Sallah? “Mu an ce mana ba kwa Sallah, bautar Husaini kuke yi a wannan Husainiyyar!” Sai na ce; “to ku ba mu ruwan in ba mu yi Sallar ba sai ku gani. Shi ne sai suka kawo mana ruwa muka yi alwala muka yi Sallah. A zaune ma yawancinmu muka yi Sallar, saboda yawancinmu kafafunmu a karye suke. Bayan mun gama Sallah, sai wani ya zo ya ce za su dauke mu su kai mu Asibitin 44 ko Shika. Zuwa can bayan La’asar sai ga shi sun zo sun kwashe mu suka kai mu Asibitin Shika suka watsar da mu.

’Yan uwa da Malaman Asibitin suka zo suka shigar da mu ciki, wasu Sistocin ma ko hijabi da dankwali babu a jikinsu. Daga nan dai ’yan uwa suka kawo mana hijabai da sauran kayayyaki, muka samu damar canzawa. Kwanana biyar a nan aka mai da ni Asibitin Kano. A Kano na yi kamar wata uku ina jinya, shi ne aka sallame ni na dawo gida. Zuwa yanzu dai jikin nawa na kara sauki daidai gwargwado. Amma har yazu akwai harsasai guda biyar a jikina, ban da ’yan kanana-kanana masu kama da ’ya’yan boris din nan.

Ba mu san irin harsasan da suka yi mana amfani da su ba. Saboda in abin ya tashi mana za ka ga jijiyoyinmu suna rikewa, za ka ji kamar ana fisgan ma su, ga kuma zazzabi mai zafi. Don haka ba mu san wane irin harsashi suka yi mana amfani da shi ba.

ALMIZAN: Da yake kun hadu da Malam Mustapha Potiskum a gidan Harisawa, kuma kin ce kune na karshen fita daga gidan, ko wane karin haske za ki yi mana?

ZAINAB SA’ID: Gaskiya na ga kafadansa akwai harbi, kuma na ga wuta ta kama masa jiki tana ci. Don lokacin da wuta ta kama jikina, kuma na ga wata kofar katako na ci da wuta tana neman ta kara fado min, garin na wuntsila na kauce wa wannan kofar katakon da na ga zai fado min a jiki, to har ma ina buge shi Malam Mustapha din, na juya na ce Malam ka yi hakuri. Ya ce Malama ba komai. Kuma ko a lokacin da hakan ta faru na ga jini na zuba a kirjinsa, kuma ga wuta na cin jikinsa. To, ni dai rabuwa ta da shi ke nan. Amma ka ga wani Shahid Idris Mando muna tare da shi a gidan Harisawan, shi ma na zata ya yi shahada, sai na ji kuma ana cewa ga gawarsa a dauko ta a kurkuku. To ka ga irin wannan ba za a iya cewa mutum ya yi Shahada, ko yana raye ba.

ALMIZAN: Malama a cikin wannan waki’ar me ya fi ba ki tausayi?

ZAINAB SA’ID: Gaskiya abin da ya fi ba ni tausayi a waki’ar nan shi ne, na farko yadda na ga ’yan uwa suna ci da wuta suna kalmar shahada, ba za su iya motsawa daga inda suke ba, da haka har su cika. Kana jin dan uwa yana kalmar shahada har sai ya kone ba mai taimakon sa. Sai kuma wata baiwar Allah mai yara, a lokacin da ruwan wuta ya tsananta garin ta haura katanga ta jefa danta a tukunyar tafasasshen ruwan zafi. Ka duba yadda uwa ke son ’ya’yanta, amma haka ta tafi ta bar shi. Gaskiya wadannan abubuwan sun ban tausayi.

ALMIZAN: A karshe wane sako kike da shi Malama?

ZAINAB SA’ID: Sakona a karshe shi ne, su gaggauta sako mana Jagoranmu, saboda a fita da shi a nema masa lafiya. Sai kuma sakona ga ’yan uwa ya kamata mu kara daurewa, haka hanyar take. Kuma ina fatan Allah ya tabbatar da dugaduganmu. Don wadanda suka fi mu, su Imam Husaini (AS), an masu abin da ya fi namu. Don haka mu ma mu daure. Haka hanyar take.

ALMIZAN: Mun gode.

ZAINAB SA’ID: Ni ma na gode.