AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. JBugu na 1284 ISSN 1595-4474

Rahotanni

Sojoji sun yi wa Mahaifinmu harbi 3 a cikin Husainiyyan -Akilu Ahmad Funtuwa

Daga Umar Babagoro Dukku


soji

Mai karatu wannan tattaunawa ce da Umar Babagoro Dukku ya yi da daya daga cikin wadanda suka rasa iyayensu yayin kisan kiyashin da Sojojin Nijeriya suka yi a Zariya daga ranar Asabar 12/12/2016 kafin su wuce Gyallesu gidan Shaikh Zakzaky (H). Akilu Ahmad Funtuwa ya shaida masa yadda harin da Sojoji suka kai ya rutsa da babban Yayansu. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatunmu.

AKILU AHMAD: Sunana Akilu Ahmad Maiganji, Funtuwa a jihar Katsina.

ALMIZAN: Mun sami labarin kana cikin wadanda suka rasa iyayensu a harin ta’addancin da Sojoji suka kai wa ’yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Zakzaky (H) a Zariya a shekarar da ta gabata, ko za ka bayyana mana wa ka rasa?

AKILU AHMAD: Ai ni dukkan wadanda Sojojin suka kashe ’yan uwana ne, kuma ina jin wannan radadi na kisan rashin tausayi da aka yi masu ba tare da sun aikata laifin komai ba! To amma a gidanmu mun rasa Mahaifinmu da babban Yayanmu a wannan waki'ar.

ALMIZAN: To, shi Mahaifin naka yaushe ya je Zariya?

AKILU AHMAD: A gaskiya ni ba na gida lokacin da ya tafi Zariya, amma na san dama yana zuwa Zariya ya yi aikin Harisanci. Wani lokaci yana yin kamar wata uku, sannan ya koma gida. Don kuwa ya je ya yi ’yan kwanaki, wannan kam ba a magana, to amma Mahaifiyata ta ce a wannan karon ranar Juma’a 11/12/2016 ne ya tafi Zariya.

ALMIZAN: Shin akwai abin da ka dan tattauna da shi kafin sadarwa tsakanin ku ta yanke?

AKILU AHMAD: Akwai. Kamar karfe 5:00ny a wannan rana ta Asabar 12/12/2015 ya kira ni a waya, lokacin ina karantar da yara a Unguwar Sheka a cikin birnin Kano. To, bayan mun gaisa sai ya ce mini; “Akilu ga mu a cikin Husainiyya, kuma dai Sojoji sun kewaye ta!” Sai na ce masa to meye ake yi a Husainiyyar? Sai ya ce mini; “Ka manta ne yau akwai bikin sanya tutar Maulidi a saman kubbar Husainiyya?” Sai ya ce mini kawai dai ku taimaka mana da addu’a! Sai na ce to Allah ya isar mana! Daga nan muka fara addu’a da yara. To, bayan mun tashi karatu da yara, sai na kira shi don in ji halin da suke ciki. Sai ya ce mini; “Ga mu nan dai tukun! Amma sun kashe mutane da yawa, kuma yanzu ma ga shi nan ina hangen ana kara sauke Sojoji a manyan motoci a bakin titi! Ga shi kuma sun kewaye Husainiyyar ta ko’ina! Kawai dai ku taya mu da addu'a!” Sai na ce masa Babana ka yi hakuri ka dake, haka hanyar take. Sai ya ce; “Haka ne! Allah ya isar mana!”

To daga nan sai abokina Shamsuddin Kudan ya kira ni a waya ya tambaye ni zan je Zariya ne? Na ce masa eh. Bayan mun taru, sai ya zama iya wadanda suke da kudin mota sune kadai suka tafi Zariya. Bayan sun tafi sai aka yi mana waya cewa duk wanda ya taso to a gaya masa kar ya je Husainiyya, kawai ya wuce Gyallesu. To, a lokacin mu sai muka shiga addu’a. Sad da na fito domin zuwa Muzahara kamar misalin karfe 12:00nd, sai na ga kiran Babanmu. Ashe ya kira ni da karfe 11:15nd ban gani ba. To, a lokacin sai na kira shi, amma wayar ba ta shiga ba! Wannan shi ne karshen abin da muka tattauna.

ALMIZAN: To shin kun sami labarin (tabbaci) ya yi shahada ne? Ko dai kawai babu labarinsa ne?

AKILU AHMAD: Malam Isah Dutsen Rimi, wanda suka tafi tare, ya zo har gida ya gaya mana Babanmu ya yi shahada, sannan ya yi mana ta’aziyya. To, amma daga baya na je Zariya sai na ziyarci Sista Narjis, Babar Narjis da A’isha a Unguwar Liman, to sai suka tabbatar min cewa lallai sun ga Sojoji sun yi wa Babanmu harbi uku a cikin Husainiyya. Harbin farko a kafa sai a kirji, sannan harbi a ka! A daidai lokacin da Sojojin suka shigo Husainiyya bayan sun ruguza ta da bama-bamai da gurneti. Wannan dai shi ne ya tabbatar mana Babanmu ya yi shahada.

ALMIZAN: To ko akwai wata wasiyya da ya bar maku?

AKILU AHMAD: Kamar ranar da zan koma Kano, na zo yi masa bankwana, sai ya ce min don Allah in kula da abubuwa uku. Na farko ya ce, in zama mai tsoron Allah. Sannan ya ce kar in bar karatu, duk wuya, duk dadi. Sannan ya ce in zama mai faranta wa Mahaifiyata da sauran kannena. Kuma daga wannan rana ba mu sake yin ido hudu da shi ba. To, sai na dauki maganar a matsayin wasiyyarsa gare ni.

ALMIZAN: Mal. Akilu kamar ku nawa Mahaifin naku ya bari?

AKILU AHMAD: Ya bar mu mu 12, maza hudu da mata takwas. A yanzu ni ne babba, tunda shi ma Yayanmu ta yiwu ya yi shahada, amma muna tare da Mahaifiyarmu.

ALMIZAN: Ko akwai abin da za ka gaya mana dangane da shi yayan naku? Kamar sunansa da dan wani labarinsa a kan abin da ya faru da shi?

AKILU AHMAD: Shi Yayanmu sunansa Awwal Ahmad Maiganji. Ya tafi Zariya ne ranar Lahadi 13/12/2015 da safe. Na yi asubanci daga Kano na dawo Funtuwa, sai aka ce mini yanzu ya bar gida ya tafi Zariya. Mahaifiyarmu ta gaya min cewa kafin ya tafi ya yi ta kuka kan wannan bakin zalunci da Sojoji suke yi a Zariya, kuma ya ce insha Allahu ba za su cim ma Sayyid Zakzaky (H) yana raye ba.

ALMIZAN: To shin kun sami labarin ya yi shahada ne?

AKILU AHMAD: A’a. Shi tunda ya tafi har yau ba mu sake jin labarinsa ba.

ALMIZAN: Ko yana da ’ya’ya?

AKILU AHMAD: Eh, ya bar mata daya da ’ya’ya uku.

ALMIZAN: To, kamar a yanzu wane hali kake ciki?

AKILU AHMAD: Ni a yanzu damuwa ta ita ce gwamnati ta gaggauta sako mana Jagoranmu Shaikh Zakzaky (H).

ALMIZAN: To menene kiranka ga sauran yaran da suka rasa iyayensu a wannan harin ta’addancin Sojoji a Zariya?

AKILU AHMAD: Ina yin kira garesu da su gode wa ALLAH (T) daya jarrabe su da irin jarrabawar da aka jarrabi manyan bayin Allah.Don haka ina fata maza daga cikinsu suyi koyi da Imam Aliyu Zainul Abidina (AS) a lokacin da aka kashe masaMahaifi (Imam Husaini) bisa zalunci a Karbala, su kuma mata suyi koyi da Sayyida Zainab.

ALMIZAN: Shin ko kanada wani sako zuwaga gwamnatin Nijeriya?

AKILU AHMAD: Kwarai ma kuwa! Sakona shine gwamnati ta bi umurnin kotu ta gaggauta sako mana Jagoranmu Shaikh Zakzaky (H) da mai dakinsa Malama Zeenatu, sannan a biya su diyyar da kotu tace a biyasu.

ALMIZAN: To mun gode.

AKILU AHMAD: Nima na gode.