AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Haramta Harka Islamiyya, tsararren shirin gwamnatin Buhari

Daga Ibraheem El-Tafseer


Imam Aliy

Duk wanda ya yi nazari da kyau na abin da ya biyo bayan auka wa Shaikh Zakzaky da almajiransa da gwamnatin Nijeriya ta yi a watan Disambar shekarar 2015, zai tabbatar da cewa shiryayyen abu ne. Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, bai yi Allah wadai da abin da ya faru ba, yanayin irin maganar da ya yi a kan abin da Sojojinsa suka aikata a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa, a lokacin tattaunawarsa da 'yan jarida 'Presidential Chat', ya nuna karara cewa yana sane da abin da suka yi, yana jin dadi da hakan. Babu hankali, babu tunani a irin yadda Sojojin suka auka wa Shaikh Zakzaky da almajiransa, da sunan wai an tare wa Shugabansu Tukur Buratai hanya. To da wace doka suka yi amfani wurin auka wa Shaikh Zakzaky da almajiransa? Daman haka abin yake a dokar kasar nan, idan an tare wa Shugaban Sojoji hanya, sai a kashe dukkan wadanda suka tare hanyar, a rusa wurin ibadarsu? Wallahi ko a shirin fim ba a haka.

To, idan an tare wa Shugaban Sojoji hanya a Husainiyya Bakiyyatullah, da ke can kan titin Sakkwato, to meye ya kawo su unguwar Gyallesu, inda gidan Shaikh Zakzaky yake? Nan kuma wa aka tare wa hanya? Wannan yana nuna cewa tsarawa aka yi a yi haka. A gidan Shaikh Zakzaky, Sojojin Buhari, sun kashe almajiran Shaikh Zakzaky sama da 1,000, wanda mafi yawansu matasa ne maza da mata, kuma dalibai. Sun kona wasu da ransu, sun yi wa mata fyade, sannan suka kwashe gawarwakin suka binne su a rami daya ba tare da an yi musu sallah ba, sannan sun kashe 'ya'yan Shaikh Zakzaky guda 3 a gabansa, dukkansu dalibai. Suka yi wa matarsa harbi sama da goma, shi ma suka harbe shi, harbin kisa suka yi masa, amma Allah bai so ya dauki ransa a lokacin ba. Kuma suka kama da dama suka kai su Kurkuku. Idan ka yarda da cewa an yi dukkan wadannan ta'addancin ne, wai don an tare wa shugaban Sojoji hanya, to ka raina wa kanka hankali. Wallahi wannan tsararren shiri ne.

Sannan suka wuce Makabartar Darur Rahma, inda aka binne Shahidanmu, suka kashe 'yan uwan da suke wurin, suka rushe wurin gaba daya, har wanda yake cikin kabari ba su bari ba, suka yi ta harbin kabarin suna rusawa. Nan ma tare hanya aka yi? Ka yi tunani da kyau mai karatu ka san wannan tsararren shiri ne. Suka wuce Fudiyya Islamic Center, da ke Dan Magaji. Suka rusa ta, suka yi watsi da littattafai, ciki har da Alkur'anai masu yawa. Suka je gidan da Shaikh Zakzaky ya binne mahaifiyarsa, Hajiya Hari Jamo, suka rushe gidan gaba daya. A ce duk an yi wannan ta'asa, na kashe rayuka da rushe-rushe saboda an tare wa Shugaban Sojoji hanya?

Tun daga matakan da gwamnatin Nijeriya ta dauka bayan aukuwar waki'ar, muka fahimci Janar Buhari ya karbo kwangilar kawar da Shi'a ne a Nijeriya daga Wahabiyawan Saudiya. Karara kowa ya san Saudiya ce take wannan aiki. Idan a da kana shakka, na san yanzu kam komai ya haska fayau, an san ko su waye suka bai wa Dogo dan Daura wannan kwangila. Bayan aukuwar waki'ar, Saudiya karara ta fito ta yi murna da hakan, ta ce wai yaki ne da ta'addanci. Sannan ga Bala Lau, Shugaban Izalar Kaduna, ya fito ya bayyana wa duniya cewa, ya goyi bayan haramta Harkar Islamiyya (IMN) da Elrufai ya yi. Wannan duk yana kara nuna wa duniya tsararren shirin da Wahabiyawan Saudiya suka tsara wa Buhari ya aiwatar a kan Shaikh Zakzaky da almajiransa. Daman shi Buhari bai san addinin Musulunci ba, bai san komai a kan hukunce-hukuncen addinin Musulunci ba. Shi ya sa daga rantsar da shi a matsayin Shugaban kasar Nijeriya, Wahabiyawan cikin gida da waje suke ta kai-komo, domin su ga sun samu gindin zama, wurin mayar da shi Ahlus sunnar dole. Kafin Buhari ya zama Shugaban kasa ba shi da alkibla, bai san komai dangane da Ahlus sunna ba, amma yanzu sun kakaba masa a dole, kuma wallahi su suka wargaza shirin da ya dauko na gyara Nijeriya, suka sukurkuta masa komai, komai ya wargaje masa.

Kowa ya san 'yan Izala Wahabiyawan kasar nan mayun kudi, kwadayayyu ne. Sai ka rasa a wace jam'iyya suke, kowane Shugaba ya zo sai sun shige masa, su nuna su kadai ne na Allah, sauran kuma kafirai. Wallahi da yanzu dan Shi'a zai zama Shugaban kasa, manyan Wahabiyawan nan da gudu za su dawo Shi'a, har suna wa'azi suna ba ta kariya. Saboda su ba addini suke yi ba, kawai neman kudi suke, kuma ai ba boyayyen abu ba ne, an sha jin su a wuraren wa'azinsu suna zagin junan su har da kafirtawa a kan kudi. Sam Lahira ba ta dame su ba, ka duba Manara TV, da kudin makamai aka bude ta, wannan ba abin kunya ba ne?

Kowa ya ga yadda su Bala Lau da Kabiru Gombe suke ta kai-komo tsakanin Saudiyya da fadar Shugaban kasar nan, suka dinga gayyato Wahabiyawan Malamansu zuwa nan Nijeriya, wai da sunan yaki da miyagun akidu. Akwai wanda suka gayyato shi ma suka sace masa wayar salularsa, wannan abin kunya har ina?

Wahabiyawan nan sai da suka raba Janar Buhari da zuwa Sallar Jumu'a babban Masallacin kasa (National Mosque), saboda limamin Masallacin dan Darika ne, dan Darika kuma a wurin 'yan Izala kafiri ne, shi ne ya sa suka hana Buhari zuwa Sallah Masallacin, suka zuga shi ya bude sabon Masallacin Jumu'a a fadar Shugaban kasa.

Wahabiyawan Saudiya sun shiga cikin gwamnatin Nijeriya sun yi dumu-dumu, duk bayan wasu 'yan watanni sai ka ga tawagarsu ta zo fadar Shugaban kasar Nijeriya. Su ne suke ba shi umarni da shawarwarin yadda zai kawar da Shi'a da Darika, saboda a wurin Wahabiyawan Ahlus Sunna dukkan su kafirai ne. Su ne suke Maulidin Manzon Allah (s), su kuma Wahabiyawan ba sa kaunar ana ambaton Manzon Allah (s), ana fadar darajojinsa da falalolinsa.

Sanannen abu ne cewa Amurka da Haramtacciyar kasar Isra'ila su ne suke bai wa shugabannin Saudiya umurni, su ne suke juya Saudiyya yadda suka ga dama, su ne suka ba da umarnin a kashe Shaikh Zakzaky da almajiransa kakaf, ya zama babu motsin Shi'a a Nijeriya. Saboda Miliyoyin Shi'awan da suke gani a lokacin Ashura da Tattakin Yaumul Arba'in shi ne yake tayar musu da hankali, har suka ba da umurnin a kawo karshen Shi'a a Nijeriya.

Bayan sun yi abin da za su iya yi a Zariya, na kisa da rushe-rushe, sai suka ga babu abin da Harka Islamiyya ta daina gudanarwa, duk da suna tsare da Shaikh Zakzaky a hannun su. Musamman yadda aka gudanar da Muzaharar Kuds a fadin Nijeriya, ya tabbatar musu da cewa lallai ba za su iya kawar da Shi'a ba. To, shi ne suka sake sabon salon yakar Shi'a a watan Muharram 1438, ta yadda za su hana zaman makokin Ashura da Muzahara da Tattaki.

Kwatsam sai ga sanarwa daga gwamnatin Kaduna, wai ta haramta Harka Islamiyya (IMN)! Har da barazanar duk wanda aka kama daurin shekaru 7 a kurkuku, kuma a kama Shugaban Dandalin yada labarai na Harka Islamiyya, Malam Ibrahim Musa. Hakan bai zo mana da mamaki ba, domin mun san tsararren shiri ne daga gwamnatin tarayya. Sai gwamnatin Kaduna ta fara kama masu zuwa zaman makokin Ashura, wanda akasarinsu mata ne da yara, sai kuma maitarsu ta fito fili ranar Muzaharar Ashura, inda bayan an kammala Muzaharar Ashura a Kaduna lafiya, sai hadin gambizar jami'an tsaro da 'yan iskan gari, suka dira Markaz din Kaduna suka rusa ta, suka kona, inda suka kashe 'yan uwa biyar.

Fitar da sanarwar Haramta Harka Islamiyya da gwamnatin Kaduna ta yi, ya jawo rubuce-rubuce da dama daga masana, saboda an rasa a ina gwamnatin jihar Kaduna ta samu wannan iko na hana wasu yin addininsu yadda suka fahimta? Duk wani mai ilimi wanda ya san abin da yake yi, ya kalubalanci wannan doka da gwamnatin Elrufai ta yi a kan IMN. Gwamnonin Katsina, Kano da Filato sai suka mara masa baya. Wai su ma sun haramta wa almajiran Shaikh Zakzaky gudanar da ayyukansu a wadannan jihohi. Tun kan su ayyana ma, mun san tsararren shiri ne da gwamnatin Buhari ta yi bisa umarnin iyayen gidansa, Wahabiyawan Saudiya da hadin kan Wahabiyawan kasar nan. Hakan shi ne ya sa suka auka wa 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky masu Muzaharar Ashura a garuruwan Kaduna, Funtuwa, Sakkwato da Jos, inda aka samu Shahidai kusan 20. Muzaharar Ashura ta duk duniya ne, ana gudanar da ita a ko ina, ciki har da birnin London, Amurka da Saudiya. Kuma fiye da shekaru 30 ana gudanar da ita a birane manya da kanana sama da 30 a Nijeriya.

A garin Funtuwa ta jihar Katsina, bayan sun bude wuta a kan masu Muzaharar Ashurar, hakan bai ishe su ba, sai suka biyo su har Fudiyya suka kara bude wuta, inda suka Shahadantar da 'yan uwa sama da 10, suka raunata da dama. Haka suka yi a Kano ma, bayan an kammala Muzahara, suka yi hayar 'yan daba, suka sassari 'yan uwa, har mutum daya ya yi Shahada, sannan suka kama 'yan uwa da dama suka tafi da su. A garin Jos kuwa, gamayyar Sojoji ne da 'yan iskan gari suka je suka rusa Markaz din 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky, sannan suka kama 'yan uwa da dama suka tafi da su, ciki har da yarinya mai kimanin shekaru uku. Kuma dukkansu suka kai su kurkuku, ba su ba da belinsu ba sai da suka yi kusan wata guda a tsare. A Sakkwato kuwa, 'yan tauri ne suka auka wa wani dan uwa bayan an tashi daga Muzahara da sara da adduna har sai da ya yi Shahada. An yi wa 'yan uwa wadannan ta'addancin ne saboda sun nuna bakin cikinsu a kan cin mutunci da kisan gillar da Yazidu dan Mu'awiyya ya yi wa zuriyar Manzon Allah (s) a filin Karbala, ranar 10 ga watan Muharram, shekara 61 bayan Hijira.

A shekarar 2014, Sojojin Nijeriya sun bude wuta a kan almajiran Shaikh Zakzaky lokacin da suke gudanar da Muzaharar Kuds a garin Zariya, inda suka Shahadantar da 'yan uwa 34, ciki har da 'ya'yan Shaikh Zakzaky na cikinsa guda 3. Duk dai a shekarar 2014 din, bayan tashin Bom a cikin masu Muzaharar Ashura a Potiskum, kuru-kuru kowa yana kallo Sojoji suka bude wuta a kan 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky suna harbi ba kakkautawa har da tankar yaki, har zuwa bakin Markaz din 'yan uwa na Potiskum. Inda suka Shahadantar da 'yan uwa 28 nan take. Amma duk da irin wannan kisan ta'addancin da Sojojin Nijeriya suke yi wa almajiran Shaikh Zakzaky, amma bai taba cewa su rama ba, kullum maganarsa ita ce 'yan uwa su yi hakuri. Kowa ya ji a hirar da sashen Hausa na BBC suka yi da shi, washe garin bude wutar da Sojoji suka yi a Muzaharar Kuds a Zariya, wanda su Sayyid Ahmad suka yi Shahada, cewa 'yan uwa ya yi, "Kowa ya yi hakuri," kuma shi ke nan babu abin da ya biyo baya na tashin hankali daga almajiran Shaikh Zakzaky.

Duk da kisan kiyashin da Sojoji suka yi wa almajiran Shaikh Zakzaky a Zariya, ranar 12-14/12 /2015, amma 'yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky ba su kai wa kowa hari ba, saboda ba irin wannan tarbiyyar Shaikh Zakzaky ya koya musu ba. Sai suka dauki mataki na hankali, irin su addu'o'i, Muzaharori, kai kara kotu da sauran hanyoyin da suka dace, domin ganin an sako mana Jagoranmu da kuma hukunta wadanda suka aikata wannan kisan. Shaikh Zakzaky babu jinin kowa a wuyansa, bai taba umurtar almajiransa su kai wa wani hari ba. Duk da irin wadannan matakai na hakuri da Shaikh Zakzaky yake dauka, idan an auka wa almajiransa, amma gwamnatin Nijeriya ba ta ganin wannan, a kullum ita tana mafarkin yadda za ta kawar da Shaikh Zakzaky da almajiransa.

Abin tambaya a nan shi ne, Boko-Haram sun kashe fararen hula da jami'an tsaron Nijeriya masu yawan gaske. Haka ma 'yan ‘Niger-Delta Avengers,’ suna fatattakar Sojojin Nijeriya, suna kashe su, kowa shaida ne a kasar nan Boko-Haram da 'Niger Delta Avengers' suna dauke da muggan makamai. Amma kullum gwamnatin kasar nan, neman sulhu take da su. To, amma kowa ya san almajiran Shaikh Zakzaky ba su da makami, ba su taba kai wa kowa hari ba. Meye ya sa gwamnatin Nijeriya ba za ta nemi sulhu da su ba? Sai dai a dinga bude musu wuta kawai, don an ga babu makami a tattare da su.

Haramta Harka Islamiyya, tabbas tsararren shiri ne da Sarakunan Saudiya suka tsara wa Buhari. To, wallahi ka shaida musu ba za ka iya ba, saboda Harka Islamiyya kayan Allah ne, kuma shi ne yake ba ta kariya, idan kuma za ka iya fada da Allah, to ka ci gaba ka gani, idan za ka yi nasara. Shugabannin da suka gabace ka ma ba su yi nasara ba, haka kai ma za ka tafi ka bar Shaikh Zakzaky da almajiransa.

Ba tun yau kuke kama Shaikh Zakzaky da almajiransa ba, kun kama kun dake su, kun kama kun kai Kurkuku, kun kama kun karya, kun kama kun kashe, kun harba tiya gas, kun bude wuta iya iyarku har sai da kuka kashe almajiran Shaikh Zakzaky sama da 1000+ a kasa da awa 24, amma 'yan uwa suna nan daram, to yanzu kuma da me za ku ba mu tsoro? To kirana ga gwamnatin Nijeriya ta gaggauta sake mana jagoranmu, Shaikh Ibrahim Zakzaky (H).

Dokar kasar nan ta bai wa kowa damar gudanar da addininsa yadda ya fahimta, to amma yanzu a kasar nan sai ka rasa wane tsari ake bi? Ba sa bin Alkur'ani, ba sa bin tsarin Kwansitushin din da suka rubuta da hannunsu, to wane tsari ake bi? Ko ka yarda, ko ba ka yarda ba, wasu ne daga waje suke ba da umurni ake aiwatarwa a kasar nan. Buhari hoto ne kawai, ba shi da iko na kansa, umurni ake ba shi daga waje.

#FreeZakzaky

#IBelongToIMN

[email protected]


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron