AlmizanAlmizan logo
Jum'a 12 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1275 ISSN 1595-4474

Labaran Harka Islamiyyah

Idan na yi shahada a sa min wannan hoton mai ‘glass’ a ALMIZAN - In ji Shahid Hamza Shariff Idris


Maulid Sayyada Fatima

Shaheed Hamza Sharif Idris yana daga cikin ’yan uwan da suka sami shahada bayan harin da jami’an tsaro suka kai wa masu Tattakin Arba’in na Imam Husaini (AS) daga yankin Kano. Cikin wannan zantawar da Wakilinmu Muhammad Sakafa ya yi da Mahaifinsa, ya bayyana mana yadda Sharif din ke tsananin son shahada. Kullum burinsa ke nan har Ubangiji ya cika masa hakan.

A cikin hirar akwai tarihinsa da mu’amalarsa da jama’a da kuma wasiyyar da ya yi na idan ya sami shahada a saka masa wannan hoton a jaridar ALMIZAN, hade da sauran abubuwan da suka wakana a rayuwarsa. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu.

SHARIF IDRIS: Sunana Sharif Idris, kuma ni ne Mahaifin Shahid Hamza Idris.

ALMIZAN: Mene ne tarihin rayuwar Shahid Hamza?

SHARIF IDRIS: An haifi Shaheed Sayeed Hamza ne a ranar 02/11/1993 a unguwar Yakasai cikin burnin Kano. Ya taso ne a gaban Mahaifansa biyu; kuma ya cika dukkan sharudan zama da ta kowane bangare sai hamdallah. Da tasowar Shaheed Hamza ya fara karatunsa na firamare a nan Shahuci a shekarar 1999, ya kammala ta a 2005. Daga nan kuma ya ci gaba da karatunsa na gaba da firamare a Sabuwar Kofa. A nan ya kammala ‘junior’ da ‘senior’ daga shekarar 2015 zuwa 2011. Bayan haka ya ci gaba karatunsa ne a Federal College of Education Kano. Zuwa yanzu matakin karatunsa NCE3. Baya ga karatunsa na addini da yake bibiyar Malaman zaure, babban Malaminsa shi ne Malam Aliyu Kofar Waika.

ALMIZAN: Ko za ka fada mana wasu daga cikin halayensa?

SHARIF IDRIS: Kadan daga cikin halayensa, yaro ne mai biyayya, mai hakuri, gaskiya da rikon amana. Ga zumunci da taimakon iyaye da sauran al’umma. A duk cikin ’ya’yana babu kamarsa. Wallahi mun yi babban rashi, amma hakan ma babbar nasara ce. Alhamdulillah.

Ta bangaren abokai kam lallai ya samu shaida wurin wasan wasa kwakwalwa da barkwanci da ban dariya ga maza ko mata, yara da manya, kowa ma abokinsa ne. Matukar ya san ka, to zai yi zumunci da kai.

ALMIZAN: Ko za a bayyana irin yadda yake riko da Harka Islamiyya?

SHARIF IDRIS: Duk cikin ’ya’yana ya fi su riko ga Harka Islamiyya. Don ko ba shi da kudin mota yakan yi Tattaki da kafa domin zuwa gurin taro, matukar taron na Harka ne. Kuma ba za a san hakan ba, sai an tambaye shi daga ina kake? Sai ya ce, ai daga gurin taro nake.

ALMIZAN: Ko akwai wasu alamu da kuka gani na shahadarsa kafin lokacin?

SHARIF IDRIS: Lallai mun gani. Lokacin zai fita ya ce wa Mahaifiyarsa cewa; “Umma za mu tafi Tattaki, idan na yi shahada, to ga hotona nan da za a sa min a ALMIZAN. Domin hoton ya yi kyau, kuma shi nake so, domin za ki ga na sa gilas, kuma gilas din ya yi min kyau”. Sai ta ce; “Ka je dana, Wallahi na bai wa Imam Hussain kai kyauta”. Cikin murmushi ya hau motata. Sai ya ce; “Hal min nasirin yansurna!!!” Sai na amsa da labbaika ya Husain!!

ALMIZAN: Mene ne sakonka ga makasa Shahid Hamza?

SHARIF IDRIS: Abin da zan ce masu kawai shi ne su gaggauta sakin Jagoran Harka Islamiyya, Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ba tare da wani sharadi ba.

ALMIZAN: Mun gode.

SHARIF IDRIS: Ni ma na gode.