Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Safar watan bala'o'i: Ga al'amuran da ya kunsa (II)

Daga Alkazeem M. Al-Hasan 0806 274 0226

A wuni na farko ne na watan Safar a shekara ta 37 aka fara Yakin Siffin, a tsakanin Imam Aliy (AS) da Mu'awiyya dan Hindu diyar Utubah, a Yakin ne Mu'awiyya da jama'arsa suka kashe Ammar Bin Yasir, Sahabin Annabi (S). A cikin sa ne kuma a bisa wasu zantukan a shekara ta 61 bayan Hijira aka shiga Damashk da kan Shugaban Shahidai, Imam Husain (AS). Sai Banu Umayyah suka sanya wannan wunin ya zama Idi gare su, alhali kuma wannan wuni ne da bakin ciki yake sabuntuwa a cikinsa. Ya kasance Zaman Makoki a Iraki. Mutanen Iraki suna Zaman Makoki a wannan wunin, su kuma Banu Umayyah a kasar Sham yana daga cikin idodinsu. A cikinsa ne har wala yau a bisa wasu zantuka na Malamai, ko ko a uku gare shi a shekara ta 111 Zaid Bin Aliyu Zainul Abidin Dan Imam Husaini (AS) ya yi Shahada a cikinsa.

Sayyid Bin Tawus ya ruwaito a littafinsa, a wuni na uku ana so a yi Salla a wannan wunin raka'a biyu. A karanta a raka'ar farko Alhamdu da Surar Innafatahana. A raka'a ta biyu Alhamdu da Kulhuwallahu. Za a yi Salati ga Annabi Muhammad da Iyalan gidansa bayan Sallama. Sai a fada sau 100 "Allahumma il'an Aali Abu Sufyana." A nemi gafara sau 100, (Astagfirullah 100), sannan mutum ya roki bukatarsa.

A wuni na bakwai ne Imam Hasan Al-Mujtaba (AS) ya yi Shahada a cikinsa a shekara ta 50, a bisa fadin Shahid da Kaf'ami da waninsu (a sanadiyyar gubar da Ja'adatu Bintu Ash'as ta sanya masa). Kuma Shahadarsa ta kasance a cikin wuni na 28 ga watan Safar, a bisa zancen Malamai biyu manya.

Kuma a cikin shi wannan wunin ne an ruwaito a shekara ta 128, ya kasance haihuwar Imam Musa Bin Ja'afar Alkazeem (AS) a Abwa'a (shi wuri ne a tsakanin Makkah da Madinah). A nan wurin ne Mahaifiyar Manzon Allah (S), Sayyidah Amina (AS) ta rasu.

A wuni na 20 ne ranar Arba'in din Imam Husaini (AS), ranar da kan Imam Husaini (AS) ya hadu da gangar jikinsa a wata ruwayar. A bisa zancen manyan Malamai biyu, ita ce ranar da ake gangaro wa haramin Imam Husaini (AS) daga garuruwa suna zuwa gaisuwa daga Sham. Ita ce ranar da Jabir Bin Abdullahi Al-Ansari (mutumin Madinah) ya iso Karbala don ziyarar kabarin Imam Husaini (AS). Shi ne farkon wanda ya fara ziyartar sa (a cikin Sahabbai). Mustahabbi ne a ziyarce shi (wato ana so a ziyarce shi).

Kuma an ruwaito daga Imam Hasan Al-Askari (AS) ya ce: "Alamomin Mumini guda biyar ne: Salloli 51 a wuni, na farilla da nafila na wuni da ake yi; da ziyarar Arba'in din Imam Husaini (AS); da sanya zobe a hannun dama; da sanya kumatu bangare biyu dama da hagu yayin Sujudus Shukur); da bayyanawar 'Bismillahir Rahamanir Rahim' a wajen karatu a cikin Salla. Hakika Shaikh Al-Mufid ya ruwaito cikin Tahzib da Misbah kebantacciyar ziyara a wannan wunin daga Imam Sadik (AS). Za mu kawo ta a babin ziyara in Allah Ya yarda.

A wuni na 28 ne shekara na 11 ranar wafatin cikamakin Annabawa, (amincin Allah ya tabbata a gare shi). Hakika ta zo ne a ranar Litinin na daga cikin kwanakin satukan karshen watan Safar, da kuma daidaituwar ra'ayoyin Malamai mabambanta ra'ayi. A lokacin da ya yi wafatin ya kasance shekarunsa 63. An fara aiko masa da Wahayi ne yana Dan shekara Arba'in, sannan ya kira mutane zuwa ga kadaita Allah shekara 13 a Makkah, sannan ya yi Hijira zuwa Madinah. A lokacin da ya yi Hijira zuwa Madinah shekarunsa ya shude madaukaki shekara 53, kuma sai ya rasu ashekara ta 10 na Hijira. Amirul Muminin Imam Aliy (AS) ya fara da wanke shi ne da sanya masa turare, ya kuma sanya masa lifafa, sai ya yi Salla a gare shi. Sannan Sahabbai suka fara zuwa jama'a-jama'a suna Salla a gare shi daya bayan daya, ba tare da wani Limami da suke koyi da shi ba. Hakika kuma Amirul Muminin Imam Aliy (AS) ya binne shi, amincin Allah ya tabbata a gare shi, a cikin daki mai tsarki, a wurin da ya rasu.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan