AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Take hakkin Shaikh Zakzaky da matarsa Shi ne mafin muni a tarihin kasar nan Cewar Femi Falana (SAN)

Daga Ammar Muhammad Rajab


gwamna

An bayyana cewa take hakkin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa shi ne mafi munin take hakkin Bil’adama a tarihin kasar nan tun bayan mulkin-mallaka na Turawa.

Babban Lauyan Nijeriya, kuma mai rajin kare hakkin Bil’adama, Femi Falana, SAN ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da jaridar LEADERSHIP a makon jiya.

Femi Falana ya ci gaba da bayyana cewa; gwamnatin Buhari sam ba ta nuna wa duniya cewa Nijeriya tana gudanar da mulkin dimokradiyya ba, “domin,” a cewar Falana, “a karkashin tsarin dimokradiyya, da zarar kotu ta ba dama, ko ta ba da belin a saki mutum, kamar a kes din Kanar Sambo Dasuki da Nnamdi Kanu,” a cewarsa, “gwamnati ba ta da ikon ci gaba da rike su, ko ta yi biris da hukuncin da kotun ta zartar.”

Femi Falana ya kara da cewa; “A shari’ar Dasuki abin ya kara muni da yawa, ta yadda har kotuna uku ne suka ba da umurnin a sake shi bisa beli, gami da karawa ma har kotun ECOWAS ta yi Allah wadai, ita ma ta umurci gwamnatin Nijeriya ta biya Naira Miliyan 50 a kan kin bin umurnin kotu na kin sakin Dasuki da take hakkinsa da ’yancinsa a matsayinsa na mutum a karkashin dokokin kare hakkin dan Adam na African Charter.

Femi Falana ya ce; shi ko al’amarin Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa shi ne mafi munin take hakkin bil’adama da ’yancinsa a matsayinsa na mutum tun bayan mulkin-mallaka na Turawa.

Falana ya ce; wannan shi ne karo na farko da ake rike mutum da matarsa, ake tsare su fiye da shekara guda ba bisa ka’ida ba, duk da kuwa kotu ta ba da umurnin a sake su, a kuma biya su diyyar take musu hakki, da kuma samar masu da wurin da za su zauna tunda gwamnatin jihar Kaduna da Sojojin Nijeriya sun rushe masu muhallinsu ba bisa ka’ida ba.

Ya ci gaba da cewa; wannan shi ne makurar take hakkin dan Adam da ’yanci a karkashin mulkin dimokradiyya da ya taba faruwa a kasar nan.

A cewarsa; suna daukar wasu sabbin matakan domin ganin sun cimma manufar ganin an saki Shaikh Zakzaky da matarsa, “domin,” a cewarsa; “babu wanda ya fi karfin doka.”

Ya ce; ko a lokacin mulkin Soja a karkashin Janar Muhammadu Buhari, babu wanda aka kama ba tare da izinin doka ba, ko bisa ka’ida ta dokar Soja ba, ko kuma karkashin dokar jami’an tsaron kasa ta tsare mutum ta Decree 2 na shekarar 1984.

Ya kara da cewa; babu wanda aka aka kama ba tare da umurni daga hukumomi ba. Ya ce; amma a yau babu irin wannan dokar. Sai dai Femi Falana ya tabbatar da cewa; yanzu kes dinmu (na ci gaba da rike Shaikh Zakzaky da matarsa), bai kamata ya zama mafi munin take hakkin bil’adama ba a mulkin dimokradiyya sabanin yadda ya rika faruwa a mulkin Soja.

Ya ce; a don haka babu wani dalili ko wani iri ne na ci gaba da rike mutum, ko kama mutum ba tare da umurnin kotu ba. Mafi hadari shi ne ci gaba da rike mutum bayan kotu ta ba da umurnin a sake shi. Ya ce; amma har yanzu gwamnatin na ci gaba da rike wanda kotu ta ba da umurnin a sake shi.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron