AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Sojoji 38 sun maka Gwamnatin Buhari a Kotun ECOWAS

Ammar Muhammad Rajab


apc

Sojoji 38, da aka sallame su ba bisa ka’ida ba, sun kai karar gwamnatin Nijeriya ta Buhari Kotun kasa da kasa ta ECOWAS. Korafe-korafe dai sun biyo bayan yadda gwamnatin ta Nijeriya ta hana daukaka karar da sojojin da aka sallama din suka yi. Shekara daya da rabi da sallamar manyan Sojojin 38, a wani rikitaccen yanayi, sai manyan Sojojin suka dumfari Kotun kasa da kasa ta kasashen Afirka ta Yamma da kokensu.

Sojojin suna zargin gwamnatin Tarayya ce da danne masu hakkinsu na mutuntaka ta hanyar kin jin nasu bahasin kafin gwamnatin ta yanke masu hukunci.

A cikin karar, korarrun Sojojin, suna korafin cewa, Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali; Hafsan Hafsoshi, Gabriel Olonisakin; da kuma Kwamandan Askarawan kasa, Tukur Buratai ne suka zauna suka kitsa korar tasu, a madadin gwamnatin Tarayya. A watan Yuni ne na shekarar 2016, kwatsam aka wayi gari da sanarwar sallamar Sojojin daga kan ayyukansu ta hanyar yi masu ritayar tilas, a bisa zargin saba dokokin aiki a lokutan zaben shekarar 2015, da kuma wai hannunsu a badakalar sayo makamai.

A binciken PREMIUM TIMES, ta bayyana cewa, wasu daga cikin Sojojin an tilasta masu ajiye aikin ne ba tare da bin dokokin aikin na Soja ba. Da yawan Sojojin da aka sallama hatta takardun tuhuma ma ba a ba su ba, ba kuma wata hukumar da ta same su da wani laifi, amma dai duk da hakan an sallame su, a bisa wasu dalilan da manyan Hafsoshin ne kadai suke iya tantancewa.

Sojojin dai sun kai kukansu ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun kuma kai kukansu ga mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, amma duk da hakan ba abin da aka yi kan bi masu abin da suka kira da hakkinsu a tsawon wannan shekara daya da rabin da sallamar su. Daya daga cikin Sojojin da sallamar ta shafa, Ojebo Baba-Ochankpa, ya mutu yana mai neman a bi masa hakkinsa a watan Janairun shekarar ta 2017.

Sojojin dai da aka yi wa ritayar tilas din, suna bukatar Kotun ne da ta ayyana hukuncin da ake cewa an yi masu a matsayin haramtacce, da kuma saba wa hakkinsu na ’yancin dan’adam, kuma an yi shi ne ba tare da bin ka’idojin da suka kamata ba. Suna kuma bukatar Kotun da ta tilasta a biya kowannensu kudaden ramuwa na Naira Biliyan goma-goma.

A wata sabuwa kuma, Rundunar ta Sojin Nijeriya, har yanzun ba ta bi kudurin nan na Majalisar Dattawa ba, wanda ya nemi da ta hanzarta mayar da wani Hafsanta a bakin aikinsa.

Bayan sallamarsa da rundunar Sojin ta yi, Chidi Ukoha, wanda yake da mukamin Kanar, bai gamsu da dalilan da rundunar Sojin ta bayar na sallamar tasa ba, sai ya garzaya da kokensa Majalisar ta Dattawa, inda ya koka da cewa sam ba a ba shi hakkinsa na sauraron nasa bahasin

ba. Kan haka, Majalisar ta Dattawa a ranar Alhamis 23 ga watan Nuwamba, sai ta umurci rundunar Sojin da ta mayar da Mista Ukoha, bisa hujjar cewa ba a sallame shi ta hanyar da ta dace ba.

A lokacin da yake gabatar da rahoton, Shugaban kwamitin na Majalisar ta Dattawa,

Sam Anyanwu, ya nusar da cewa, an yi kuskuren sallamar Hafsan Sojan, duk da cewa yana da akalla shekaru 12 nan gaba a cikin aikin na Soji.

“Bayanin da Rundunar Sojin ta yi na cewa, an ladabtar da Hafsan na Sojin ne ta hanyar yi masa ritayar tilas, an kuma ba shi damarsa ta hanyar sauraron kokensa kafin a yi masa ritayar, rundunar ta Sojin ta kasa tabbatar da hakan, domin ba inda ta nuna cewa, an gargadi Hafsan a kan wani laifi, ko kuma an kira shi a gaban wata hukuma ta Soji. Sannan kuma hukumar ta Soji ta kasa ta tabbatar da shaidar da za ta iya nuna cewa, Hafsan yana da hannu a kan wata

badakalar makamai ta Sojin ko kuma wata cuwa-cuwar siyasa a lokacin zabe,” duk in ji rahoton na Majalisar Dattawa.

Haka kuma wani Hafsan na Soji wanda rundunar Sojin ta kasa ta sallama daga bakin aikinsa, Abdulfatai Muhammad, ya sami nasara a karar da ya shigar gaban Kotun bin kadin koken Ma’aikata.

Mista Muhammad, wanda yake da mukamin Laftana Kanar, ya garzaya kotun ta sauraron koken ma’aikatan ne inda yake kalubalantar sallamar da aka yi masa.

Yana daga cikin wadanda aka ce an sallama ba tare da mika masu wata tuhuma ko kiran su a gaban wata hukuma ta Soji domin su amsa wata tuhuma ba.

A kotun ta sauraron koken na ma’aikata, rundunar Sojin ta ce, sam bai kamata a ci gaba da sauraron karar ta Muhammad ba, domin a cewarta, Muhammad din bai ketare shingayen da dokar aikin Sojin ta tanada ba, sannan kuma ta daukaka maganar nasa zuwa ga Shugaban kasa.

Amma duk da haka, Mai Shari’a Haastrup, na kotun sauraron koken na ma’aikata, a ranar 13 ga watan Nuwamba shekarar 2017, ya yi watsi da wannan bukatar ta rundunar ta Soji, ya kuma yi umurni da a ci gaba da sauraron Shari’ar. An dai sanya wata ranar da ba a ambata ba a cikin watan Maris na wannan shekarar domin ci gaba da sauraron shari’ar.