AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Duk ’yan Darika suna tare da maganar Shehu Dahiru Bauchi na cewa ‘Shi’a ’yan uwanmu ne!’

In ji Imam Awwal As-Sudani


“Wallahi a cikin Darika, ba wanda bai tare da maganar da Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya yi, na cewa ’yan Shi’a ’yan uwanmu ne! Kai Almajiri ba ka da ta cewa da lamarin Shehunnai.

Wakilci suke yi na sunayen Allah, kai muridi mai bi ne. Shehu Dahiru Shehunmu ne, abin girmamawarmu ne, abin so da bin mu ne, Marja’inmu ne a cikin Darikar Shehu da addinin Musulunci.

“Ina fada ne, duk wanda ya ji ya isar. Idan har Shehu ya ce muna tare da ’yan Shi’a, to muna tare da su! Musulmi ne ’yan uwanmu ne, in suna zagin Sahabban Manzon Allah, to mun rabu da su a wajen zagin Sahabban Manzon Allah, amma babu wani dalili da ya ce su ba Musulmi ba ne. Kuma wanda yake cewa, su ba Musulmi ba ne, dama kafin ya ce su ba Musulmi ba ne, ku ma ya ce ku ba Musulmi ba ne. Yau ne ya yarda ya hada kai da ku? Mu Darikarmu ba ta bukatar hadin baki wallahi!”

Wadannan kalaman sun fito ne daga Halifan Dk. Ibrahim Makari, Imam Awwal As-Sudani, a yayin da yake jawabi a wajen Mauludin da aka gudanar ranar Juma’ar da ta gabata a gidan Sharif Kabiru da ke unguwar Rigasa, Makarfi road a cikin garin Kaduna.

Halifan, ya nuna matukar takaicinsa ga muryar da ake yadawa a kafofin sadarwa, irin su Facebook da WhatsApp, cewa wani Malamin Kungiya ya yi suka ga maganar Shaikh Dahiru Bauchi na cewa ’yan Shi’a ’yan uwansu ne. Inda ya ce ba komai ba ne wannan sukan nasa face tatsuniya wacce dama ita suka saba yi, ba karatu ba, wanda sam ba su fahimtar karatun. “To waye ya ce ’yan Shi’a ba ’yan uwanmu ba ne? A ina aka fadi, wace aya ko hadisi ne suka fadi cewa ’yan Shi’a ba ’yan uwanmu ba ne? Babu!” In ji shi.

Ya bayyana cewa, kamata ya yi Ahlussunah su fara yakar Nasibawan cikin su masu zagin Sayyadina Ali (RA), wanda ya fi Sayyadina Abubakar da Umar da duk sauran Sahabbai daraja, saboda shi ‘Nafsur Rasul’ ne, sannan idan Nawasib din suka daina zagin, sai a tunkari wasu a waje, a ganar da su illar zagin sauran Sahabban idan ya tabbata suna zagin.

Shaikh As-sudani ya kuma yi kira ga ma’abota darikar Tijjaniyya da cewa: Kar ku yarda wasu wawaye da ba su iya karatu ba, ko sun yi karatu ba sa fahimtar karatun, su rude ku.”

Ya kara da cewa: “Ko da a ce ba mu da kowa a matsayin Marja’inmu yanzu sai Shaikh Dahiru Usman Bauchi, wallahi ya isar mana a addini. Don haka ba ma saba wa fatawarsa, ba ma saba wa abin da ya karantar da mu, domin ce masa da ake Lisanul Faidati da ake yi ba shi ya sakawa kansa ba, Shehu ne da manyan Almajiran Shehu suka saka masa. Don haka don wani shashasha ya zo yana sukan maganar Shehu da tasuniya ana turawa a ‘group’, ba zai yi mana tasiri ba!”