AlmizanAlmizan logo
Jum'a 11 ga Muharram, 1440 Bugu na 1360 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Muzaharar Ashura, Jami’an tsaro sun raunata ’yan’uwa 2 a Zariya, sun kama daruruwa a Abuja, An yi a Kaduna, Sakkwato, Kano, Katsina, Gombe, Bauchi da Daura lafiya

Daga Abdullahi Usman


Daga Aliyu Saleh, Ammar Muhammad Rajab, Saifullahi M. Kabir, Muhammad Nasir, Abdul’aziz Kwaranya, Musa L. Musa, Saifullahi Shehu Dandume, Sadik Umar, Shehu Illela da Lawal Kafin Madaki

A jiya Alhamis ne ’yan’uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da Muzaharar Ashura a garuruwa daban-daban a fadin kasar nan, sai dai jami’an tsaro sun auka wa ta a Zariya, sun kama daruruwa a Abuja, yayin da aka gama lafiya a wasu garuruwan.

Wakilinmu ya shaida mana cewa tun da misalin karfe 7:00ns goshin Muzaharar ya motsa daga masallacin Juma’a na Sabon Garin Zariya zuwa bakin Dogo Hayin Ojo.

’Yan’uwan da suka hada maza da mata suna tafe cikin lumana suna rera wakokin juyayin kisan Imam Husaini, tare da kuma jaddada wa gwamnatin Tarayyar Nijeriya cewa ta saki Shaikh Ibraheem Zakzaky da take tsare da shi ba bisa ka’ida ba, duk da kotu ta ba da umurnin a sake shi.

Bayan Muzaharar ta ratsa ta titin Muchiya, aka nufi titin ‘Kings’, har aka isa inda za a rufe wato bakin Dogo, Hayin Ojo Sabon Gari, ba tare da wata matsala ba.

Cikin jawabinsa na rufewa Shaikh Abdulhamid Bello ya karfafi ’yan’uwa a kan jajircewa a wannan tafarki na Iyalan Gidan Manzon Allah (S). Sannan ya bayyana cewa; waki’ar Karbala da ta Zariya suna da kamanceceniya. Ya sake jaddada kiran a sakin Shaikh Zakzaky da gaggawa.

“Wannan ya kara fahimtar da mu hakikan yadda waccan waki’ar ta Karbala ta kasance. Saboda in ka dubi wadanda suka yi aika-aikar nan za ka tarar dabi’u da halayensu iri daya ne da Yazidawan wancan zamanin na rashin tausayi da imani, kamar yadda za su yanka mutum su taka da dawakai, sai ga shi nan a wannan zamanin an samu sojojin kasa, wadanda ake biyan su da harajin al’ummar kasa, sune za su zo kuma su kashe dan kasa su kona da rai, su kashe jarirai da mata. Wannan ya faru a Zariya.

“Babu abin da za mu ce, sai dai mu ce wannan abin da ya faru da mu waki’ar Ashura ce ta maimaita kanta, amma abin da muke so mu tabbatar wa azzaluman wannan zamanin, kamar yadda Yazidu abin da ya yi yi wa Iyalan Annabi, bai ba shi nasara da ya tabbata a kan mulki ba, su ma na yau su tabbatar da cewa Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky shi ne zai yi nasara, da’awarsa ce za su yi nasara.”

Shaikh Abdulhamid Bello ya yi kira ga ’yan’uwa su tabbata su kara daurewa, su sani fada tsakanin gaskiya da karya, gaskiya ce ke samun nasara. “A tunaninsu bayan wancan abin da suka yi, sun shafe masu cewa su ’yan Shi’a ne. Sara da sassaka ba ya hana gamji toho. Ga mu nan mun fito yau! Kuma muna nan daram! Babu gudu, babu ja da baya.”

Bayan kammala jawabinsa ne, har an fara watsewa, kwatsam sai ga gamayyar jami’an tsaro cikin mota 15, wadanda suka hada da ’yan sanda da sojoji. Sun isowa suka fara antaya tiyagas da harbi da harsasai masu rai.

Ya zuwa hada wannan rahoton an raunata ’yan’uwa biyu; Ibrahim Abubakar da Ibrahim Galadima, wadanda dukkaninsu matasa ne. Suna ci gaba da karbar magani a Asibiti.

Wasu majiyoyin sun bayyana mana cewa bayan kammala Muzaharar, jami’an tsaro sun kama ’yan’uwa da yawa da ba a tantace adadinsu ba. Sun bi ’yan’uwa na garin Gabari da ke kusa da Zariya suna dukan su. Sannan sun je Fudiyya ta garin Anchau da ke hanyar Jos sun shiga sun debo kayayyaki sun kona.

KATSINA

Su ma ’yan’uwa na yankin Katsina sun gudanar da gagarumar Muzaharar juyayin kisan jikan Manzon Allah, Imam Husaini (as) da rundunar Yazidu ta yi ma kisan gilla, tare da iyalansa da ma Sahabbansa a Karbala a shakara ta 61 bayan Hijira.

An soma muzaharar ne da misalin karfe 8:15 na safe, wadda ta hada dukkan ’yan’uwa maza da mata manyansu da kanana, inda suke isar da sakon wannan zalunci da aka yi ta hanyar wakokin da ake rerawa da aka yi wa Iyalan Annabi (s).

Al’ummar garin Katsina, musamman a titunan da aka bi ta kansu, sun nuna fahimtar sakon da ake isar masu, musamman a lokacin da masu Tamsiliyya ke nuna irin cin mutuncin da aka yi wa jikokin Manzon Allah bayan kashe Imam Husaini (AS).

Mawakan Harkar Musulunci sun ba da gagarumar gudummuwa ta hanyar shajja’a masu Muzaharar, inda suke rera wakokin juyayi daban-daban, abin da ya hana gajiya, ga kuma isar da sako ga al'umma.

An dai fato wannan muzahara ne tun daga filin wasan kwallon kafa na cikin gari, inda aka kewayo wasu tituna aka rufe ta a filin Tanki da ke unguwar Rafindadi da ke cikin garin Katsina. Shaikh Yakubu Yahya ne ya jiwabin rufewa.

DAURA

Su ma ’yan’uwa na garin Daura da kewaye sun gudanar da Muzaharar Ashura jiya Alhamis, inda dandazonsu suka fito suna rera taken mubaya'a ga Imam Husain (as) da yin tir ga Yazidu (L).

Muzaharar ta tattaro zugar mahalarta ayari-ayari na ’yan tamsiliyya, masu misalta yadda aka yi wa zuriyar Manzon Allah (S) a Karbala, Harisawa cikin sahu-sahu, ga yaran makarantun Fudiyya da ’yan’uwa maza da mata cikin kayan da suke alamta juyayi, wato bakake.

An fara ta ne daga babban masallacin Juma'a na garin Daura, kuma aka zagaya tsakiyar garin. An bi ta unguwannin da suka hada da Kofar Kudu, aka wuce ta unguwar Kusugu da Madabu, aka ratsa ta sassan unguwar kofar Arewa, sannan aka zagayo wajen kammala jawabin rufewa a babban filin kofar fadar Sarkin Daura.

A jawabinsa Wakilin ’yan’wa na garin, Malam Mustafa Muhammad, ya yi wa al’ummar da suka kewaye filin jawabi kan waki’ar Ashura, game da abin ya faru na ta’addancin da Yazidawa a Karbala.

GOMBE

Muzaharar da aka yi a garin Gombe ta taso ne daga Jekadafari Primary School, inda ta bi ta kusan dukkan manyan titunan garin. Ta bi ta babban shataletalen cikin gari, sannan aka bi ta hanyar Sabon Layi, ta shiga cikin kasuwa, har zuwa masallacin Idi, inda aka rufe ta a wajen.

Masu Muzaharar dai suna tafe ne suna rera take na juyayi da kisan Imam Hussaini da kuma take na kira da a gwamnati a kan ta gaggauta sakin jagoransu Shaikh Zakzaky.

Muzaharar ta samu halartar dubban ’yan’uwa maza da mata, da dama sun shaida cewa ba su taba ganin Muzaharar da ta cika kamar wannan Muzaharar ba.

Malam Abubakar Pantami ne ya rufe Muzaharar da jawabi, inda ya tunatar da mahalarta taron musibar da ta faru a ranar Ashura na kashe Jikan Manzon Allah (S). Ya kuma yi kira ga gwamnati a kan ta gaggauta sakin Shaikh Zakzaky, inda ya bayyana abin da ya faru a Zariya da cewa Zariya, tamkar Karbala ne.

KANO

Su ma ’yan’uwa na garin Kano sun bi sahun al’ummar duniya don gudanar da jerin gwano na lumana wanda suka saba gabatarwa don tunawa da ranar da aka kashe Jikan Manzon Allah (S), Imam Husain (AS) da Iyalansa a falalin Karbala.

Muzaharar, wadda aka fara ta daga masallacin Sarki na cikin garin Kano, ta samu halartar dubban ’yan’uwa maza da mata da ke tafe cikin tsari dauke da hotuna da tutocin da suke alamta ta’addancin da aka yi wa Iyalan Manzon Allah (S) a daidai irin wannan rana da kuma wadanda ke dauke da ta’addancin da rundunar sojojin Nijeriya ta yi a harin da suka kai a Zariya.

A lokaci guda kuma masu Muzaharar suna kira ga gwamnatin Buhari da ta gaggauta bin umurnin kotu na sakin Shaikh Ibraheem Zakzaky.

A cikin jawabinsa na rufe Muzaharar, Malam Sani Malfa, wanda shi ne ya jagoranci Muzaharar, ya yi karin bayani a kan irin kisan gillar da aka yi wa Iyalan Annabi a wannan rana, da yadda aka tsare su a falalin daji babu ko ruwan sha ballanta abinci da yadda aka dinga yanka su daya bayan daya.

SAKKWATO

A Sakkwato Birnin Shehu ma dubban almajiran Shaikh Zakzaky maza da mata ne suka fito kan titi a jiha Alhamis don gudanar da Muzaharar nuna juyayin kisan gillar da aka yi wa Imam Husaini (AS) a Karbala.

Haka ma bangaren jami’an tsaro sun fito da dukkan karfinsu, domin duk inda ka waiga gaba da baya har da tsakiya za ka gan su cikin shirin yaki dauke da muggan makamai.

Haka su ma bangaren mutanen gari da Wakilinmu ya yawata a cikin su domin jin abin da suke fada, ya ji wasu suna jinjina ga ’yan’uwa irin yadda suka ga yawan jami’an tsaro, amma bai hana su fitowa ba.

A cikin jawabinsa na rufewa, Malam Sirajo Abubakar Nufawa ya bayyana irin ta’addancin da sojojin Yazidu Dan Mu’awiyya suka yi ga Imamu Husaini da Sahabbansa. Ya bayyana irin rashin tausayi da kekasasshiyar zuciyar da suka yi a lokacin da Imamu Husaini ya nemi su ba Abdullahi Radih, yaro dan wata shida ruwa, amma suka harbe shi a makogwaro.

Haka kuma ya karkare da cewa, tsayuwar Imamu Husaini a Karbala samfur ne ga al’umma cewa ba a saranda ga azzalumai. Haka kuma ya kara da cewa; “Mu ma ’yan’uwa yanzu ya kamata mu san cewa taimakon Sayyid Ibraheem Zakzaky wajibi ne a kanmu. Don haka mu hadu a Abuja don sauke nauyin da ke kanmu na wannan bawan Allah.”

Muzaharar, wadda aka soma ta daga unguwar Mabera, aka bi ta Madan Karo, ta bi ta masallacin Sidi Attahiru, an rufe ta ne a kusa da Gidan Shahid Kasimu Umar Sakkwato.

KADUNA

Tun sanyin safiyar Alhamis din ne jama’a suka yi ta tururuwa wajen da aka shirya za a hadu domin tashin Muzaharar da aka yi a garin Kaduna.

Goshin Muzaharar ya tashi ne karfe 6:30 daidai daga mahada Hayin Danmani, aka bi babban titin aka nufi Bakin Ruwa, har zuwa kan Kagoro.

Malam Aliyu Tirmizi ne ya yi jawabin rufe Muzaharar, inda ya yi gamasasshen bayani a kan dalilin fitowar tasu, ya kuma yi tsokaci game da halin da Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky da maidakinsa Malama Zeenah suke ciki.

BAUCHI

An faro Muzaharar ta Ashura ne jiya a Bauchi daga Masallacin Ajiya, inda ta haura titin kofar Ran, ta biya titin Bakin Kura, zuwa Turin Wunti. Sannan ta zago ta Turin Kobo, ta haura kofar fadar Sarkin Bauchi, ta fado harabar kasuwar Central, aka koma harabar masallacin Ajiyan Bauchi aka kitse ta.

Muzaharar ta yi cikar da ba a taba ganin irin ta ba, ’yan’uwa sun fita cikin bakaken kaya dauke da tutocin masu dauke da rubutun LABBAIKA YA HUSAIN!

’Yan kallo ma sun cika titina suna kallon Muzaharar tamkar muzaharar Maulud. A lokacin muzaharar an raba takardu mai dauke da dalilin fitowar. Malam Ahmad Yusuf Yashi ne ya yi jawabin rufewa.

ABUJA

Dubun-dubatar ’yan’uwa ne suka halarci Muzaharar Ashura da aka yi jiya a Abuja, duk da yunkurin jami’an tsaro na dakile ta, inda ta yi cika fiye da yadda ake tsammani.

An fara Muzaharar ne da misalin karfe 11:00 na safe daga wajen gidan Mai na F.O, aka mike zuwa Hajj Camp, aka bi Sakateriyar kasa, aka zagayo ofishin Hukumar Shari’a ta kasa, sannan aka gangaro ta Unity Fountain, aka kuma yin kwana aka koma ofishin Public Complaint kusa da inda aka ta da Muzaharar.

An dauki kusan awa biyu da rabi ana zaga garin da Muzaharar, tare da barazanar gamayyar jami’an tsaro, masu yunkurin hanawa a duk gabar da aka nufa. Sun rika tare hanya ga masu Muzaharar, amma bisa taimakon Allah sai a tunkare su a bude hanyar.

Tun da safe jami’an tsaro suka rika tare hanyar, inda suka kama daruruwan ’yan’uwa maza da mata a motocinsu a hanyarsu ta zuwa wajen Muzaharar. Ya zuwa hada wannan rahoton dai, ba a sako su ba.