AlmizanAlmizan logo
Jum'a 17 ga Rajab, 1438. Bugu na 1284 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Gangamin neman a saki Shaikh Zakzaky a Abuja: ’Yan Sanda sun kai hari

Daga Abdulmumin Giwa


A ranar Talatar nan da ta gabata ne, ’yan sanda suka kai farmaki da nufin tarwatsa gangamin gamayyar ’yan Nijeriya masu kishi da suka shirya domin kira ga gwamnatin Tarayya da ta bi umarnin kotu ta saki, Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da gaggawa.

*Majalisa za ta sake duba batun -Hon. Ado Doguwa

*Shaikh Zakzaky aka fi zalunta a kasar nan -Femi Falana (SAN)

Daga Abdulmumin Giwa

A ranar Talatar nan da ta gabata ne, ’yan sanda suka kai farmaki da nufin tarwatsa gangamin gamayyar ’yan Nijeriya masu kishi da suka shirya domin kira ga gwamnatin Tarayya da ta bi umarnin kotu ta saki, Jagoran Harka Islamiyya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da gaggawa.

’Yan sandan dai dauke da hayaki mai sa hawaye, manyan karnuka na tarwatsa taro, motocin ruwan zafi da bindigogi, sun mamaye farfajiyar Unity Fountrain da ke babban birnin Tarayya Abuja, inda aka shiya yin gangamin domin su hana taron baki daya.

Sai dai masu taron da suka hada da Kiristoci da Musulmi sun bijirewa wannan kokarin na hana taron, inda suka bayyana wa ’yan sandan cewa babu inda dokar kasa ta ce sai da izininsu ne dan kasa zai gudanar da taro bayan sun yi iya kokarisu domin fahimtar da su, amma abin ya ci tura.

Lokacin da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban gamayyan Mista Deji Adeyanju, ya bayyana ci gaba da tsare Shaikh Zakzaky a matsayin tauye hakkin dan’adam da bai kamata duk wani mutumin kirki kuma dan kasa na gari ya aminta da shi ba. Don haka ya yi kira ga jama’a da su tashi tsaye su tabbatar da cewa an bi umarnin kotun Tarayya an saki Jagoran Harka Islamiyya.

Shi ma a nasa jawabin, daya daga cikin wadanda suka shirya gangamin, Dakta John Danfulani, ya bayyana dirarwa Harka Islamiyya da aka yi a Zariya a matsayin zalunci, domin babu wata hujja da ta ba da damar a dirar wa mutane da kisa kamar kiyashi ana rusa masu wuraren ibada da gidajensu.

Ya bayyana cewa ba zai taba mantawa da irin karamci, gudummawa da taimakon da Shaikh Zakzaky ya yi masu ba lokacin da suke dalibai a Zariya ba, inda ya ba su kariya a lokutan da ake rikice-rikicen addini da na siyasa a baya.

Ya ba su kariya, ya ciyar da su, kuma ya ba su kudin mota suka koma gidajensu bayan rikice-rikicen ya lafa. Ya ce bai dace a ce mutum mai irin wannan mutuncin ne ake cin zarafinsa jama’a na kallo ba.

Haka kuma tsohon Shuganban Hukumar kare hakkin dan’adam ta kasa, National Human Rights Commission, Farfesa Chidi Odinkalu, ya yi tir da tsare Shaikh Zakzaky har na tsawon kwanaki 484 ba tare da an tuhume shi da wani laifi ba, inda a lokaci guda kuma kotu ta ba da umarnin a sake shi, kuma gwamnati ta yi burus.

Ya bayyana wannan a matsayin kaucewa tsarin dimokradiyya. Ya ce duk cikan ’yan gamayyar su ma ’yan Shi’a ne, kuma suna kir da a saki Shaikh Zakzaky da gaggawa.

Ana cikin wadannan jawaban ne ba tare da wani tsokana ko tunzuri ba, kawai sai ’yan sanda suka fara watsa ruwa da motar ruwan zafinsu, suka kuma yiwo cikin jama’a da wasu manyan karnuka na tarwatsa taro suna harba hayaki mai sa hawaye da kuma bindiga.

Wannan ta’asan na ’yan sanda ne ya tunzura jama’a suka hau sahu suka bi titi suna cewa ‘Free Zakzaky!’ Inda ’yan sanda suka biyo sahun masu Muzahara ta baya suna watsa musu ruwa da hayaki mai sa hawaye.

Daga bisani kuma ’yan gamayyar sun fitar da takardar sanarwa da Dakta John Danfulani da Deji Adeyanju suka sanya wa hannu, inda suka yi tir da aika-aikan da ’yan sanda suka yi na neman tarwatsa gangamin neman a saki Shaikh Zakzaky.

Sun bayyana gwamnatin Tarayya a matsayin wadda ba ta son wani yare da ya wuce amfani da karfi ba ko da inda ba a bukata da karfin ne kuwa, inda suka kira ta da cewa ba ta da abin yi ko da yaushe da ya wuce taka mutane da karfin tuwo ko da ko bisa hakkinsu ba ne.

’Yan gamayyar sun bayyana cewa ba za su fasa kiran gangamin ba har sai an bi dokar kotu an saki Shaikh Zakzaky, kuma nan gaba kadan za su sake kiran wani gagarumin gangamin.