AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Ganduje ya gamsu da manufofin Kungiyar Izala -Alhaji Ali Baba

Daga Alhusain Dakace


gwamna

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana goyon bayansa dari bisa dari ga manufofi da akidun Kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah reshen Kaduna karkashin jagorancin Shaikh Abdullahi Bala Lau.

Gwamnan Kano, ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin addini, Alhaji Ali Baba A Gama Lafiya Fagge a lokacin da yake isar da sakon Gwamnan a taron wa’azin kasa da Kungiyar Izala ta gudanar a filin wasan kwallon kafa da ke Kofar Mata, Kano kwanakin baya. Gwamnan ya kara da yabawa irin jajircewar da Kungiyar Izala take yi wajen yada koyarwar addinin Musulunci a fadin kasar nan.

Shi ma a nasa bangaren, Shugaban Kungiyar, Shaikh Abdullahi Bala Lau, ya yaba da irin gudummuwar da gwamnatin Kano da jami’an tsaro da sauran masu hannu da shuni da suka hada da A. A. Rano. Alhaji Tahir Hungu, Alhaji Salihu Sagir Takai, Alhaji Sani Rogo da sauran jama’a suka bayar wajen samun nasarar wa’azin. Haka kuma ya yaba wa gwamnatin Tarayya, wacce ta turo babban jami’inta, Alhaji Kawu Sumaila wajen taron, tare da bayyana irin gudummawar da suka bayar wajen ganin taron ya samu nasarar da ya samu a jihar.

Sai dai jama’a na mamakin ganin yadda aka bar Kungiyar Izala bangaren Shaikh Bala Lau ta gudanar da taron wa’azin, duk da kuwa jami’an tsaro sun bayyana cewa sun haramta duk wani taro, ko gangami na addini a duk fadin jihar.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron