AlmizanAlmizan logo
Jum'a 26 ga Jimada Ula, 1438 Bugu na 1277 ISSN 1595-4474


Babban Labari

>

Sojojin da suka kashe ’yan Shi’a 350 Har yau ba wanda aka hukunta - In ji Amnesty International

Daga Wakilinmu


>

Kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoto da ya bayyana 2016 a matsayin shekarar da aka samu karuwar kyamar juna tsakanin bil’adama, wanda ya wuce yadda aka gani tun shekarar 1930, lokacin mulkin tsohon Shugaban Jamus Adolf Hitler.

Rahoton ya bayyana Nijeriya a cikin kasashen da ake samun ire-iren wadannan matsaloli.

Jami’in hulda da jama’a na Amnesty International a Nijeriya, Isa Sanusi, ya tattauna da BBC sashen Hausa a ranar Larabar da ta gabata, ya kuma shaida mata abin da rahoton ya kunsa kamar haka: “To, abin da shi wannan rahoto ya kunsa shi ne irin halin da duniya ta samu kanta a ciki. Kuma rahoto ne da ya duba yanayin da ake ciki dangane da hakkin bil Adama a kasashe 159, yadda yanzu duniya ke fama da rikice-rikice daga Yemen zuwa Siriya, zuwa batun ’yan gudun hijira da suka shiga wani hali da yadda kasashe da yawa suka juya musu baya. Sannan kuma da batun Nijeriya, wadda bisa ga dukkan alamu abubuwa suke kara tabarbarewa, musamman dangane da hakkin bil’adama.”

Sai aka ce masa, kamar dai rahoton ya fito da batutuwa da suka shafi nuna kyama da kiyayya da juna.. Sai ya ce, “Wannan batu na kiyayya da juna da kyama da farfado da batun amfani da kishin kasa da kuma kokarin tabo abin da yake yi wa mutane dadi domin kawai mutum ya samu kuri’a, matsala ce da ke shafar manyan kasashen duniya, kamar yadda a rahoton muka yi maganar abin da yake faruwa a Amerika, inda Shugabansu na yanzu yake wasu kalamai wadanda suke karfafa wa wasu su nuna kiyayya ga wasu, su nuna cewa su ba ruwansu da wasu.

“A Nijeriya mu matsalolinmu daban ne da suka hada da batun yadda jami’an tsaro kawai sun zama kamar suna da lasisin su kashe mutane, su ci mutuncin mutane, su daure su. Wani ma a daure ka a karbi kudade daga hannun ’yan uwanka, kuma babu wani wanda zai bi maka kadu.

“Sannan kuma ga batun ’yan Shi’a din nan da aka kashe musu mutane 350, amma har yau ba wanda aka hukunta, illa ma kotu ta ce a saki Shugabansu da Mai dakinsa, amma har yanzu nan gwamnati sai kewaye-kewaye take yi, ta kasa bin dokokin ma da ita kanta take amfani da su. Kun ga wadannan batutuwa ne da suke da matsala.

“A yankin Neja-Delta, kamfanonin mai masu karfi da suke da kudi suna cin karensu ba babbaka, suna lalata muhallin talakawa, wadanda daga karshe ba za su iya noma ba, ba za su iya samun ruwan sha ba. Ga rayuwa a Nijeriya tana kara zama idan ba ka da karfi, sai abin da Allah ya yi.”

Sai aka ce masa, da yake ka kawo batun Shi’a, to wane ka’idoji kuke bi ku fidd da irin wannan rahoto naku, tunda su ma ’yan Shi’an akwai rahotonnin da ke cewa su suke kamar tunzura gwamnati, suna keta wasu dokokin gwamnati da bai kamata a ce sun keta ba har ya kai ga aka dauki wasu matakai a kansu.

Sai Jami’in hulda da jama’a na Amnesty a Nijeriya din ya ce, “mu dai a duk lokacin da muka dauki wani batu za mu duba shi, mukan dauki watanni. Misali rahoto a kan batu guda yakan dauke mu wata uku zuwa hudu, saboda mukan je wurin da abin ya faru, sannan mu ji ta bakin kowa. Sannan bincike ne muke yi mai zurfi. Idan ka ba mu hoto, sai mun sa shi a na’ura, an tabbatar da cewa hoton nan a nan wurin aka dauke shi, kuma a wannan lokacin ne. Saboda haka muna amfani da abubuwa na zamani wajen tabbatar da cewa abin muke aiki da shi gaskiya ne.

“Sannan kuma ko da su Hukumomi a Nijeriya, idan muka fid da rahoto, kafin jama’a su ga wannan rahoton, sai mun aika wa Hukumomi mu ce, to mun yi bincike ga abin da muka gano, ga abin da muka gano, ku me za ku ce a kan wannan abu? Wato shi ne abin da ake kira muna musu adalci, mu sanar da su ga shi fa mun gano kaza, mun gano kaza, ku ma ku fadi naku bahasin.”

Dangane da wannan rahoto na Amnesty International, BBC ta tuntubi rundunar sojan Nijeriya domin jin martaninta, amma ba su same su ba ya zuwa lokacin hada rahoton nan. Sai dai a wata sanarwa da Kakakin hedikwatar tsaron Nijeriya Birgediya-Janar Rabe Abubakar ya sa wa hannu, ya yi watsi da rahoton.