AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Jimada Ulai, 1436 Bugu na 1172 ISSN 1595-4474


Babban Labari

Bom na 14 ya tashi cikin watanni 4 a Potiskum

Daga Ibrahim El-tafseer


NUJ

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari ya bayyana kulle-kulle da zagon kasa iri daban-daban da toshe hanyoyin samun gudummuwar zabe daga jama’a, ta hanyar kamfanonin sadarwa na GSM, da kuma ingizawa a kai shi kotu, don a haramta masa tsayawa takarar, wanda ya rage saura kwanaki da gwamnatin PDP karkashin jagorancin Shugaban kasa Ebele Jonathan ke yi, da cewa, ba wani abu ya haifar da shi ba face lalacewar aikin Gwamnati kasarmu Nijeriya.

Janar Muhammadu Buhari ya bayyana haka lokacin da yake ganawa da manema Labarai, ciki har da ALMIZAN, a gidan Gwamnatin jihar Kano a kwanakin baya.

Janar din ya ce, “idan ba lalacewa ba, yaya za a yi a ce ma’aikatan gwamnati, ciki har da sojoji, ana amfani da su cikin harkokin siyasa, har suke fitowa suna bayyana wa duniya cewa ba su san inda takardun makarantata suke ba, don ba su hannunsu.”

Janar Muhammad Buhari ya kara da cewa, “wanda Allah ya nufa ya zama Ofisa, daga ran da ya samu Anini a gidan soja, zai mika daukacin takardunsa na makaranta baki dayansu ga ofishin babban Sakataren Hukumar sojoji na kasar nan, saboda haka na yi mamaki yanzu a ce wadannan takardun karatun nawa ba su wurin soja. To, amma mun san abin da ke aukuwa a kasar nan, don wannan rashin ganin takardun nawa yana nuna lalacewar aikin Gwamnati ne.”

An tambayi shi Janar din cewa, da wadanne takardu hukumar zabe ta kasa ta ba ka izinin takara? Ya ce, “sai ku je ku tambayi Hukumar zabe, ba mu da takardu, suka bar mu muka yi takara har karo uku, ga na hudu muna yi, ba da takardun makaranta ba?”

Janar Buhari ya kara da cewa, “kamata ya yi Gwamnatin kasarmu ta mayar da hankali wajen yaki da cin hanci da karbar rashawa, da kuma kawar da rashin aikin yi a tsakanin matasanmu da rashin tsaro da zubar da jinin dubun-dubatar al’ummar kasar nan, shi ne abin da ya kamata ta mayar da hankali wajen magance wadannan tarin matsalolin, ba zargin rashin takarduna ba daga gwamnati mai ci.”

An sake tambayar Buhari cewa, to mene ne lambarsa ta jarabawa da jam’iyyar PDP ke zargin ba shi da ita ? Sai ya sake kada baki ya ce, “lambata ta jarabawa ita ce 82000002, kuma na samu kyakyawan sakamako, kuma ba matsalar takardar makaranta ba ne.”

Tuni dai makarantar da Janar din ya yi karatun sakandare a jihar Katsina ta fitar da kwafin sakamakon kammala karatun Sakandire din, ta raba wa manema labarai.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron