Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Yadda Sarkin Kano ya tsira daga harin 'yan bindiga

Daga Ali Kakaki ([email protected])

A ranar Asabar din da ta gabata ne wadansu mutane dauke da muggan bindigogi suka bude wa motar da Sarkin Kano, Alhaji (Dk.) Ado Bayero yake ciki wuta babu kakkautawa, tare da na 'yan tawagarsa.

Nan take kuma mutane uku, suka rasa rayukansu. Sune Direban motar Sarkin, Alhaji Amadu Dogari, Majidadin dan Rimin Kano, sannan kuma Sarkin motar, da kuma Dan Mori, Alhaji Ado Bala Kofar kudu. Sai kuma na uku, Alhaji Kabiru Barden Ruwa.

Sai kuma munanan raunuka da wasu manyan bayin Sarkin da 'ya'yansa suka samu sakamakon harbin su da maharan suka yi.

Amma shi Sarkin, cikin ikon Allah babu abin da ya same shi, duk da cewa maharan suna ganin sun kashe shi sakamakon irin ruwan harsasan da suka yi wa motarsa.

'Yan bindigar sun kai wa Sarkin na Kano da 'yan tagawarsa wannan harin ne a kan hanyarsu ta komawa gida daga wajen taron bikin saukar karatun Alkur'ani na makarantar Madrasatul Ma'ahad Shaikh Muhammad Kabir dan Taura da ke cikin harabar masallacin Juma'a na marigayi tsohon Shugaban kasa Janar Murtala Muhammad da ke unguwar Hausawan Gidan Zoo, cikin Karamar Hukumar Kumbotso a jihar ta Kano, ta gudanar, har kuma Sarkin ya ba da gudummawarsa ta Naira miliyan biyu ga makarantar.

Wadanda abin ya faru a kan idonsu sun bayyana ma ALMIZAN cewa jim kadan da rufe bikin da addu'a ne, tsakanin filin taron da ofishin 'yan sanda na filin Hockey, sai kawai wadansu mutane dauke da bindigogi tsirara suka nufi kan motar da Sarkin yake ciki kai tsaye, suna mata ruwan harsasai.

Nan take suka kashe Direban motar, Alhaji Amadu Dogari, inda shi kuma Dan Mori Alhaji Ado Bala Kofar kudu, da ya ga abin da yake faruwa ya je da gudu ya yi wa Sarkin garkuwa suka yi ta masa ruwan harsasai. Shi ma nan take ya fada kan jikin motar ya rasu.

Shi ko Alhaji Amadu Barden ruwa sun harbe shi ne lokacin da yake kokarin isa kan Sarkin ya yi masa garkuwa shi ma.

Amma cikin ikon Allah babban bawan Sarkin, Shamakin da ke cikin motar, shi da Sarkin, Allah ya tserar da rayukansu. Sai dai shi Alhaji Wada Usman Shamakin Kano, sun harbe shi a kafarsa.

Cikin tawagar Sarkin da wannan lamari ya shafa akwai babban dan Sarkin, Alhaji Sunusi Ado Bayero, Ciroman Kano, sannan kuma Hakimin Gwale, a inda suka harbe shi a kafarsa, da kuma Alhaji Nasiru Ado Bayero, Hakimin Nasarawa, inda shi ma suka harbe shi a kafarsa.

Sannan akwai mutum takwas daga cikin 'yan tawagar Sarkin da suke kwance suna jinya a Asibitocin Murtala da Malam Aminu Kano.

Sai dai kuma a cikin mutanen da suka rasa rayukansu akwai Shugaban riko na Karamar Hukumar Kumbotso, Alhaji Salisu Kura, wanda kuma shi ne mai masaukin baki a wajen taron, da kuma wani makusancinsa da suke mota daya shi ma ya rasu.

Malam Muhammad Kabiru Dan Taura, Limamin masallacin Murtala tare yake cikin mota da Shugaban na riko da ya riga mu gidan gaskiya, ya kuma bayyana ma ALMIZAN cewa lokacin da suke kan hanyarsu ta rakiya ga tawagar, sai suka ji ana ta harbe-harbe. Sai suka yanke shawarar su canza hanya. Lokacin da suka canza hanya ne, sai kawai wasu mutane a kan babur suka biyo motarsu, su ma aka yi ta harbin su.

Nan take aka kashe Alhaji Salisu Kura da wani makusancinsa, tare da raunata daya daga cikin su. Sai dai shi babu abin da ya same shi.

Wani magidanci da gidansa ke kusa da inda abin ya faru ya shaida wa manema labarai cewa jim kadan da faruwar abin ya ga lokacin da wani matashi yake karya bindigarsa sannan ya sanya ta cikin buhu, suka hau kan mashin suka gudu.

Da yammacin wannan rana ta Asabar ne aka yi wa daukacin mutane biyar din da suka rasu sutura, aka kuma kai su makwancinsu.

Sannan a ranar Lahadi, aka gudanar da addu'a ta musamman a masallacin Juma'a na Kofar fadar ta Kano. Jim kadan da kammala addu'ar ne kuma da misalin karfe 1:30 na rana, Sarkin na Kano tare da 'ya'yansa guda biyu da wasu 'yan rakiyarsu suka wuce kasar Birtaniya birnin London domin duba lafiyarsu.

Haka kuma a wannan ranar ne ta Lahadi Mataimakin Gwamnan jihar, Injiya Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa an kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi da kai wa tagawar Sarkin hari, kuma suna hannun jami'an tsaro suna gudanar da bincike a kansu.

Haka kuma Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa dukkanin su maharan an gano cewa ba 'yan jihar Kano da Nijeriya ba ne.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan