Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           An hana Achaba a birnin Kano

Jama'a da dama na guna-guni

A ranar Talatar da ta gabata, Gwamnatin jihar Kano ta ba da sanarwar kafa dokar hana yin goyo a kan kowane irin Babur a cikin Kananan Hukumomin babban birnin jihar, wacce za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 24-1-2013.

Haka kuma dokar ta bukaci kowane mai Babur da ya je ya yi rijista da Karamar Hukumarsa.

"Bayan tattaunawa da Hukumomin jami'an tsaro da kuma kyakkyawan nazarin shawarwarinsu, mun lura cewa ya zama tilas mu dakatar da jama'a daga hawan baburan tare da fasinjoji daga ranar Alhamis 24 ga Junairu, 2013," Ganduje ya bayyana.

"Ana bukatar masu babura da su yi wa baburansu rijista domin tabbatar da tsaron lafiyarsu da ta jama'a. Muna kira ga masu baburan da su koma Kananan Hukumominsu su yi masu rijista, don amfanin kansu da kuma jama'a."

Sai dai kuma awa guda da bayyana wannan dokar ne aka je aka harbe mutane biyar har lahira a unguwar Dakata da ke cikin Karamar Hukumar Nassarawa ta jihar Kano. Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta tabbatarwa da manema labarai aukuwar dukkanin hare-haren.

Hana wannan sana'a ta achaba ya sa jama'a na ta guna-guni kan dokar. Da dama suna ganin hakan zai haifar da karuwar marasa aikin yi a cikin birnin na Dabo, ko ba komai dubun-dubatar samari ne matasa ke cin abinci ta hanyar wannan sana'a ta achaba.

Shugaban kungiyar 'yan achaban, ACOMORAN a takaice, Alhaji Muhammad Hasan Sani ya bayyana hana sana'ar a matsayin wani abin bakin ciki a gare su, "saboda zai jefa mutane sama da miliyan daya da rabi cikin jerin rashin abin yi," a jihar.

Ya shaida wa manema labarai cewa ba a tuntube su ba kafin a kafa wannan sabuwar doka, don haka yana rokon a janye wannan doka don dadada wa membobin kungiyarsa da dimbin jama'a talakawa da suke amfana da wannan sana'a tasu.

Tuni dama aka hana acaba a garuruwan Maiduguri, Damaturu, Jos, Lagos, Uyo, da Lagos. Sai kuma wasu sassan birnin Gombe.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan