Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Duk a ni'ímomi, babu kamar samun Annabi Muhammadu (S)

- Shaikh Dahiru Usman Bauci

Bisa ga zagayowar watan maulidin Ma'aiki, wanda ake bukukuwa a cikin sa, da kuma karatuttutuka gami da samun tarihin Ma'aiki, ya sa Wakilinmu Khalid Idris Doya, ya nemi Shaikh Dahiru Usman Bauchi don jin me zai ce dangane da zagayowar watan Maulidin. Wannan hirar ta musamman ce. Ga kuma yadda ta kasance. A sha karatu lafiya.

ALMIZAN: Ganin watan Maulidi ya doso kai, za mu so mu ji wane sako kake da shi dangane da zagayowar watan Maulidin?

SHAIKH DAHIR USMAN BAUCI: A'uzubillahi minasshaidanir rajim. 'Maulud' da Larabci, yana nufin wajen haihuwa, ko lokacin haihuwa, zarufuz zaman, ko zarful makan ne. In an ce Maulidin Nabiy, Rabi'ul Awwal din nan kuwa, ba shakka a ciki aka haifi Manzon Allah, amma na Miladiyya, har su kansu yanzu ba su san yaushe aka haifi Annabi Isah ba. Su da kansu in an ce masu, me ye sa ku e yin Miladiyya ranar 25 ga watan Disamba? Za su ce haka dai aka samu domin a kawar da wani bikin da matsafan arna suke yi. Don haka suka ce a kawo wannan ya zama ya rufe wancan na tsafin, amma su karan kansu ba su ambaci lokacin da aka haifi Annabi Isa ba. Amma mu mun san ranar da aka haifi Annabi Muhammad (S), mun san yadda aka haife a Makka. To, da abin ya zama tarihi, sai ya zama ranar biki, wanda babu kamar sa a Musulunci, domin dukkan bikin da ake a Musulunci wani abu ne da Allah ya bayar, sai a yi biki a gode masa. Duk abin da Allah ya ba ka, ka nuna murna, ka gode masa. "La'inshakartum

la'azidannakum wala'inkafartum inna azabiy lashadid."

Allah ya ce, idan ya yi mana ni'ima muka gode, sai ya kara mana. To babbar ni'ima, babu kamar samun Annabi a wannan duniyar tamu. Saboda haka ne ake bikin Maulidin Annabi Muhammad (S), abin ya zama biki. Idan mutum ya ce me ya sa Sahabbai ba su yi Maulidi ba? Sai mu ce masa, ai su Sahabbai ga su ga Annabin, sai su yi menene, in sun yi murnar ranar da aka haife shi, to wannan ranakun da suka biyo baya ai duk suna kallonsa, kuma kallon Annabi kullum, shi karan kansa ibada ce.

An tambayi Annabi (S), mun ga kana yawan azumin Litinin da Alhamis? Sai ya ce, ranar Litinin dai ita ce aka haife ni, ranar Alhamis kuma ne ake daukan ibadun mako. Ina so ake dauka har da azumi a ciki. Saboda haka sai ya zama abu ne na murnar haihuwar Annabi. Allah ya sa mu yin salla ranar Asabar, Lahadi, Litini, Lalata, Laraba, Alhamis, Juma'a na bakwai sai mu mayar da ranar Idi, mu gode wa Allah da ya ba mu salla, da kuma daman yin sallar har na mako guda, to sai ranar Juma'a ta zama ranar Idi.

Haka kuma idan shekara ta zagayo sai a je inda aka saukar da salla, Makka, a je a yi taro a can don ya zama Idi na shekara-shekara. Idin babban salla ke nan, kowace kasa, duk duniya sai a gayyace ta, ta zo ta yi yanka wa sauran al'ummarta, wanda ba su samu zuwa ba, wannan shi ne ake kira Hajji. Bayan an sauko daga Arfa a washe gari sai a mayar da shi ranar Idi ranar murna, an shekara lafiya, an kuma samu ni'imomi lafiya, saboda haka ake gode wa Allah, a yanka dabbobi na murna na saukan Alhazai daga Arfa.

Saboda haka kuma Allah ya ce in na yi maku alheri, to ku gode min. Idan mutum ya yi wani babban gida mai kyau, zai kira jama'a su taya shi murna, wani ma har yana walima. Haka idan mutane sun samu mulki, tunda mulki ni'ima ce daga Allah. Su Annabawa da aka ba su mulki, idan an samu mulki akan ce za a yi wankan sarauta ko nadin ba da sanda, ranar sai ta zama ranar Idi ga wannan garin. Sai su gode bisa mulkin da suka samu. Shi mulki alheri ne ga mutum mai alheri, haka sharri ne a wajen mutumin sharri.

Dukiya ma alheri ce wajen mutumin kirki, sharri ce dukiya a wajen mutumin banza. Haka ma idan aka yi saukan Alkur'ani, a yi walima a gode wa Allah, domin Sayyidina Umar da ya haddace Suratul Bakara ya yanka dabbobi don murnar ya haddace ta, kafin ya ci gaba da haddace sauran. Duk gaba daya, idan mutum ya yi aure zai yanka dabba don murnar ya samu mace ko ya kara macen. Akan kira wannan biki walimar aure. Haka kuma idan matar ta haihu, ranar ita yau, sai a yi yankan murnar an samu Da wanda ba a samu a gona ko kasuwa ba.

To, duk wadannan abubuwa da suka shafi addini, ya shafi Alkur'ani, to ya fi duk ni'imominin da muka ambata. Da Alkur'anin da zuwan addinin, duk zuwan Annabi duniya ne ya kawo su, duk wasu abubuwan da ake murnar zuwansu a addini Annabi ne ya zo da su. Saboda haka ya kamata a nuna zuwan Annabin ya fi kowane abu. Mu nan Bauci dama muna kiran bikin Maulidi, sallar kaji, a wajajen Kano a na ce mata Takutaha. Babu inda ake biki sosai kamar Borno, suna kiran Maulidi Gurikira, wato babban Idi, suna hawan Daushe duk shekara. Haka irin su Daura, Gumel, haka suke yi wa Maulidi. Amma mu kawai mukan yi biki ne a yanka kaji mu ci.

To Shehu Ibrahim Kaulaha ya ce shi a ganinsa duk Ididodin duniya ba wanda ya kai haihuwar Manzon Allah (S). Duk Idin da aka ambata a baya, kama da haihuwar Annabi, Idin haihuwar Manzon Allah ya hau dukkanin Idodi. Misalin tauraron da yake can saman taurari, to Idin Manzo ya fi haka. To, sai mutanenmu suka fara zuwa Kulaha suna ganin yadda Shehu yake girmama Maulidi. Shekarun da suka samu zuwa sai su bar wakilansu su yi maulidin a gida, su kuma su yi a can.

Za mu ci gaba insha Allah.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan