Shafin farko           

Hantsi                     

Tattaunawa              

Wakilanmu             

A takaice                 

Rahotanni                

Mu leka mu gani     

Masu karatu            

Duniyarmu a yau    

Bulaliya                  

Dandalin Wasanni  

Shafin hotuna          

Shafin baya              

Taskar Almizan       

Sisters' Forum         

WasuShafuka           Maulidin Manzon Allah (S)

Alamin hadin kan Musulmi

Tun bayan shigowar watan Rabi'ul Awwal, watan da aka haifi Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammad (S), aka ga karin alamu na haduwar kan Musulmi da ma al'ummar kasar nan baki daya.

A kusan duk inda aka shirya tarurrukan Maulidin, jama'a daga bangarori daban-daban suna halarta, kuma daga jawaban da suke gabatarwa, suna kara karfafa gwiwa game da fatan da ake da shi na dinke duk wata baraka da ake samu a tsakanin al'ummar Musulmi.

A garuruwa daban-daban na kasar nan ana ci gaba da shiryawa da gabatar da tarurrukan Maulidin, kuma ana ganin karuwar mahalarta, daga bangarorin jama'a. A wannan karon jama'a na shiryawa dai-daiku da kuma a jam'i fiye da lokutan baya.

Binciken da Wakilinmu ya gudanar ya gano cewa 'yan uwa Musulmi al'amajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky sun kawata garuruwansu da alamin Maulidi, musamman a garin Kano, wanda ke kara nuna wa duniya an shigo watan da aka haifi Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S).

A Kano 'yan uwa Musulmi a karkashin jagorancin Malam Muhammad Turi sun shirya tarurrukan Maulidi fiye da wanda suke shiryawa a baya, sun kawata shi fiye da shekarun baya, sun ziyarci gidajen Sharifai da manyan Malamai, sun kai masu kyaututtuka. Kuma duk inda suka ziyarta, wadanda aka ziyarta din suna nuna farin cikinsu, tare da shan alwashin aiki tare don ciyar da addinin Musulunci gaba.

A garin Kaduna ma Wakilinmu ya shaida mana cewa a karon farko sun shirya taron Makon Hadin Kai, wanda ya hada har da Kiristoci, inda wani Fasto da aka gayyata ya gabatar da jawabi mai ratsa zuciya game da daraja da irin daukakar da Allah ya yi wa Manzo (S). Malaman da aka gayyata sun hada da Shaikh Salihu Maibarota, Shaikh Lukman Hayin Banki, Shaikh Musa Tanimu Palladan, Shaikh Fatahu Pandogari da kuma Fasto Yonanna Y.D. Buru.

A Zariya ma a jiya Alhamis aka fara gabatar da taron Makon Hadin Kai karo na 10 a Husainiyya Bakiyyatullah, inda ake gayyatar Malamai daga bangarori daban-daban da fahimtoci daban-daban, inda ake jawabai na kara kusantar juna.
Shafin Farko

Muna Facebook


Kuna iya ziyartarmu a dandalin zumunta

 


Ku bimu a Twitter

Kuna kuma iya samun mu a wannan zaure

  


Ku Tuntube mu

Muna maraba da wasikunku

 


Kash!

Ba ka sami daman kare duba tsofaffin jaridunmu ba'
Babu damuwa.
Kana iya duba nan