AlmizanAlmizan logo
Juma'a 8 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1132 ISSN 1595-4474


Rahotannimu

 Tabarbarewan tsaro
Batun gurfanar da Janar 10 Na Soja
*Bisa zargin taimaka wa Boko Haram
*Hedikwatar Tsaro ta karyata
Rundunar sojojin kasar nan da Ma’aikatar tsaro ta Tarayya sun karyata bayyanai da ke cewa wai an samu kame wasu sojoji da ke ma Boko Haram aiki kuma wai an gabatar da su gaban kotun soji a wasu barikoki da ke Arewacin kasar nan....
Kashe-kashe
Yadda aka kashe mutane 36 a Dutsen Ngoshe
-Aka yi sama da awon gaba da mata 11

A ranar Asabar 26/4/2014 ne, ’yan bindiga suka kai hari kauyen Ngoshe-Sama da ke garin Gwoza ta jihar Borno...

 Arabic
‘Gwamnati na kawo cikas ga ci gaban harshen Larabci a Nijeriya’

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na nuna bambanci ga darasin harshen Larabci, duk kuwa da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta dauki harshen a matsayin harshenta a hukumance, Kungiyar Malaman Adabin Larabci ta kasa (NATALL) ce ta fadi haka...

Sauran rahotanni
Mummunan hatsarin mota ya ci rayuka 16 a Illela
‘Hukuma Alhazai Ta Kaduna Ta Samu Gidaje Kusa Da Harami A Makka’


Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H): Zakzaky (H)


Bidiyo (H)

Hoton Bidiyo:

Jawabin Sayyid Zakzaky (H) ranar maulidin Sayyada Zahra (SA) a Zariya


Albishirinku

Almizan
Android
Duk mai na'ura ko waya da ke da "Android" yanzu zai iya karanta AlMizan ta na'uran ko wayar tasa.

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.


Free counters!Labaran Harka Islamiyyah

 Shahidai Mu’assasatus Shuhada ta ziyarci Mahaifar Shahidin farko
A ranar waccan Juma’ar da ta gabata ne, wakilan Mu’assasatus Shuhada’u ta Harkar Musulunci suka kai ziyara mahaifar Shahidin farko a Harkar Musulunci a Nijeriya, Shahid Muhammad Bello a garin su na Kolori da ke a Karamar Hukumar Gamawa ta jihar Bauci...

Tunatarwa:

Zakzaky (H)

Tare da Sayyid Zakzaky

Dole a saki su Haruna Abbas

Wannan wani bangare ne na jawabin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a taron Yaumus Shuhada na ranar Asabar 25 ga Rajab, 1435 a filin Polo kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta mana.

IN DA KOWA ZAI BA DA HAKKIN SHUHADA

Sakamakon ’yan uwa suna gyara kaburburan Shahidai har wasu ma sun fara koyo. To, amma inda mutum zai je sauran duniyar musulmi zai ga cewa, wannan abu ne zaunanne. Ana kyautata makwantan mutane, ana kuma tunawa da su ta nan. To, Shuhada’u ‘khasatan’ da ma dukkan sauran wadanda suka mutu. Amma ‘khasatan’ Shuhada suna da wannan hakkin.

Sannan kuma suna da hakki na kula da iyalansu, ainihin abin da suka bari baya - matansu da ’ya’yansu da iyayensu. Har wala yau, wannan yana dan dada sanyaya rai. Ya dan kwantar da hankalin mutum, ya rika tunawa da nasa. Da zafi mun sani. Da zafi! Da zafi, amma kuma zai dan sa shi ya yi tunanin cewa, ran dansa, bai tafi a kawai ba, insha Allah...
Ra'ayin Almizan

Wakilanmu
Almizan
Sharri Kayan Kwalba!

Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...


Daga Gidan Annabta

Tare da Abubakar Abdullahi Almizan

Salati
Ayyukan ban kwana da watan Rajab

SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB

Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR

Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...


Katun

Ina mafita daga halin da muke ciki?
Katun
Kofa daya ce rak mafita


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA BIKIN NISFU SHA'ABAN
  Imam KhomeiniAna sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi bukukuwan NISFU SHA'ABAN na bana wanda za a gudanar kamar haka:

  Rana:
  Juma'a 15 ga Sha'aban 1435

  Lokaci:
  Yamma zuwa dare

  Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

  Rana:
  Asabar 16 ga Sha'aban 1435
  Jawabin Yaumul Taklif da sallah da yara

  Lokaci:
  Safe zuwa rana

  Mai Jawabi: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah

  Rana:
  Asabar 16 ga Sha'aban 1435

  Lokaci:
  Yamma zuwa dare

  Gagarumin majalisin mawaka wanda Alh Mustapha Umar Baba Gadon Kaya jai jagoranta

  Wuri:
  Hussainiyyah Bakiyatullah

  Rana:
  Lahadi 17 ga Sha'aban 1435

  Lokaci:
  Safe

  Gasar fareti da Harisawa zasu gabatar
  Mai karbar fareti: Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
  Akwai walimar bukin Nisfu Sha'aban bayan sallolin Magriba da Isha'i.

  Wuri:
  Filin Polo gefen Hussainiyyah Bakiyatullah
  Allah ya ba da ikon halarta


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron


Ra'ayoyinku na baya-bayan nan zai bayyana nan gaba kadan...

Tambihi:

Muhammad Sulaiman

Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna

Nizamin Ibadodi (I)
Wannan maudu'i na tsarin ibadodi, maudu'i ne mai gayar muhimmanci, domin zai taimaka mana insha Allah wajen tsara ibadodin mu da kuma fahimtar littafai na ibadodi. Malaman Irfan sun yi bayani a kan cewa ayyuka na Ibadodi a nizaminsu sun kasu kashi biyar:

*Ayyuka Yaumiyya, wato wadanda ake son aikatawa kullum.

*Ayyuka Usbu'iyya, wato wadanda ake son aikatawa kowane mako.

*Ayyuka Shahariyya, wato wadanda ake son aikatawa kowane wata.

*Ayyuka Sanawiyya, wato wadanda ake son aikatawa kowace shekara.

*Ayyuka Umriyya, wato wadanda ake son aikatawa, ko da sau guda a rayuwar mutum...