Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo

Juma'a 1 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1131 ISSN 1595-4474

Rahotannimu

 Tabarbarewan tsaro
Tabarbarewar Tsaro a kasar nan: Ba a ba jami’an tsaro abin da ya kamata a ba su - Sanata Abu Ibrahim
A cikin tattaunawar da ya yi da Manema labarai a Kaduna, Sanata Abu Ibrahim ya nuna takaicinsa game da tabarbarewar tsaro a kasar nan...
PTD
Rikicin kungiyar direbobin tanka reshen jihar Kaduna
Kwamared Nuhu Muhammad ya samu nasara a shari’ar sa da Gambo Tuge

An kawo karshen shari’ar da ake yi tsawon watanni a babbar kotun sauraren kararrakin masana’antu da ke Abuja, tsakanin Tsofaffin shugabannin kungiyar Direbobin tanka, PTD ta jihar Kaduna, Kwamared Nuhu Muhammad Marafan Nasarawa, Kaduna da Gambo Ibrahim Tuge...

 ABU Zaria
SSANU ta raba filaye 104 a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya

Kungiyar manyan ma’aikatan Jami’o’i ta Nijeriya reshen Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta raba filaye guda dari da hudu ga ’ya’yan Kungiyar...


Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H): Zakzaky (H)


Bidiyo (H)

Hoton Bidiyo:

Muzahara ranar maulidin Sayyada Zahra (SA) a Zariya


Albishirinku

Almizan
Android
Duk mai na'ura ko waya da ke da "Android" yanzu zai iya karanta AlMizan ta na'uran ko wayar tasa.

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.Labaran Harka Islamiyyah


Tunatarwa:

Zakzaky (H)

Tare da Sayyid Zakzaky

Ba wata tsiya wai ita Boko-Haram

Wannan wani bangare ne daga karshen jawabin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), da ya gabatar ga dandazon dubban ’yan uwa da suka halarci taron Yaumus Shuhada a ranar Asabar 25 ga watan Rajab, 1435 (24/5/2014) a filin Polo da ke kusa da Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ne ya rubuto muku. A sha karatu lafiya.

DANGANE DA MASU TSAREWA

To, shi kenan, sai kuma dangane da su masu (tsarewa), tunda na ma fara taba, da tunanin cewa; su ba su da wani aiki illa su yi harbi. Mukan yi muku nasiha, don kuna da hakkin mu yi muku. Su mahukunta, kamar yadda su mahukunta dauri suka yi, ainihin suke ganin da karfin tsiya za su kawar da bayin Allah, haka ma na yanzu suke tunani. Kuma tunaninsu iri daya ne. Ba su daukar darasi daga abin da yake faruwa daga karshe. Ina mulkin Banu Umayya? Ina na Banul Abbas? To, kun ga yanzu me ya rage?

Lokacin da shi wannan Harun din nan zai cika (makashin Imam Kazim), sai ga shi da bakinsa yana cewa; “ma’agna anni maliyya, halaka anni suldaniya.” Da wadannan kalmomin ya cika. Shi da bakinsa ya fada, ya yanke ma kansa hukumci. “Dukiyata ba ta tsinana min komai ba, sarautar tawa ta riga ta kai karshe"...
Ra'ayin Almizan

Wakilanmu
Almizan
Sharri Kayan Kwalba!

Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...


Daga Gidan Annabta

Tare da Abubakar Abdullahi Almizan

Salati
Ayyukan ban kwana da watan Rajab

SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB

Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR

Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...


Tambihi:

Muhammad Sulaiman

Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna

Darasin Hadisi na III
Insha Allah a wannan darasin Hadisi na uku, za a kammala wannan gabatarwa da kuma shimfida dangane da fannin ilimi na Hadisi da aka soma tun a darasi na daya. Kuma bayani zai gudana a wannan darasi kan wadannan ababe kamar haka: 1- Karancin Hadisan Ahlul Baiti a littafan Hadisai na Ahlus Sunna. 2- Taharifin Hadisan Ahlul Baiti a littafan Ahlus Sunna. 3- Jarabawowin da masu ruwaito Hadisan Ahlul Baiti suka fuskanta daga masu tafi da iko...

Katun

Babban Hafsan Hafsoshin sojojin Nijeriya ya ce sun san inda kamammun 'yan mata suke
Katun
Dama Malam ya ce mana suna barikin sojoji

Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah
GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta.

Labarai cikin hotuna

Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana


 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
 • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
 • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
Ra'ayoyinku na baya-bayan nan zai bayyana nan gaba kadan...