AlmizanAlmizan logo
Juma'a 24 ga Rajab 1435 Bugu na 1130 ISSN 1595-4474


Rahotannimu

 Saudiyya
Sanata Dansadau ya nemi a biya diyya ga jama’ar Zamfara
Sanata Sa’idu Dansadau ya bukaci gwamnatin Tarayya da ta biya diyyar mutanen da suka rasa rayukan ’yan uwansu a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani yanki na jihar Zamfara...
 Yan Acaba
’Yan bindiga sun kashe 36 a Dutsen Ngoshe-sama
Sun yi awon gaba da mata 11

A ranar Asabar 26/4/2014, ’yan bindiga suka kai hari kauyen Ngoshe-sama da ke garin Gwoza. Lawan Umaru Gufogo shi ne Lawinin kauyen, ya shaida wa Al-mizan cewa: Wanan hari wanda shi ne na biyu a cikin watanni uku, sun kashe mutane 36 da jikkata da dama. Kuma ’yan bindigar sun yi awon gaba da mata 11...

 NPF
An cafke sojar bogi mai damfarar jama’a

Wata mata mai matsaikacin shekaru, wadda take ikirarin ita soja ce tana damfarar jama’a ta fada komar sojoji reshen Akure babban birnin jihar Ondo...


Jawabai da Karatun Shaikh Ibrahim Zakzaky (H): Zakzaky (H)


Bidiyo (H)

Hoton Bidiyo:

Muzahara ranar maulidin Sayyada Zahra (SA) a Zariya


Albishirinku

Almizan
Android
Duk mai na'ura ko waya da ke da "Android" yanzu zai iya karanta AlMizan ta na'uran ko wayar tasa.

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.


Free counters!


Labaran Harka Islamiyyah


Tunatarwa:

Zakzaky (H)

Tare da Sayyid Zakzaky

In ka ji abin da ba ka sani ba kan Imam Ali (AS), kar ka ce ba haka ba ne

Mai karatu ga ci gaban jawabin Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na maulidin Imam Ali (a.s) da yammacin ranar Litinin din 13 ga watan Rajab, 1435 (12/5/2014). Ammar Muhammad Rajab ne ya rubuto maku. A sha karatu lafiya.

Allah Tabaraka wa ta’ala ya halicce ni da Ali daga haske guda kafin ya halicci halitta da shekaru dubu dari biyar. Kafin a halicci halitta da shekaru dubu dari biyar (500,000). Mun kasance muna ‘tasbihi’ da ‘takdisi’ ga Allah (T). Yayin da Allah (T) ya halicci Adamu sai ya jefa mu a tsatsonsa. Kuma ni na tabbata a bangarensa (bangaren Adam kenan) na dama, Ali kuma a bangaren hagu.

Sannan aka cire mu daga tsatsonsa ya zuwa tsatsotsi tsarkaka da kuma cikkuna tsarkaka. Don ‘Rahim’, ‘Rahim’ yana nufin (mahaifa) inda jariri ke zaune a cikin uwa. Muna ce masa ciki da Hausa. Shi kenan. Wato ainihin ‘sulb’ kuma tsatson na namiji da mahaifar mace. Wato tunda daga Adam har ya zuwa Abdul Mutallib. Daga Adam sai aka cira tsatson aka sa a Hawwa. Daga Hawwa aka koma ya zuwa Shiis, daga Shiis zuwa matar Shiis, daga matar Shiis zuwa… Wannan haka nan. Har ya zuwa Ibrahim zuwa Hajir daga nan kuma zuwa Isma’il zuwa matar Isma’il zuwa Nabit. Ga su nan, ga su nan, ga su nan har ya zuwa… tiryan-tiryan. Kowanne tsarkakka namiji da tsarkakka mace. Shi ne wato tsatsotsi ‘aslabud dahirat’ da ‘arhamud dayyibat’. Da ‘dayb’ da ‘dahir’ duk za mu ce, tsarkakka (tsarkaka za mu ce)...
Ra'ayin Almizan

Wakilanmu
Almizan
Sharri Kayan Kwalba!

Babban labarin mujallar Tell News Magazine na ran 17 ga Yun, 2013 No. 24 da aka yi wa kanu: Sabuwar matsalar tsaro: Rawar Gabas ta tsakiya” (New Security Threat: The Middle East Connection), abin damuwa ne. Wani wai shi ANAYOCHUKWU AGBO ne ya rattaba wannan ‘tatsuniyar” da ...muke magana a kai. A takaicen takaitawa, bangaren makalar tasa da aka yi kokarin nuna cewa Harkar Musulunci a Nijeriya da kuma Shugabanta abin girmamawa, ’yan tashin hankali ne masu mummunar manufa, ya nuna yadda marubucin yake dan baranda, wanda bai san abin da yake magana a kai ba...


Daga Gidan Annabta

Tare da Abubakar Abdullahi Almizan

Salati
Ayyukan ban kwana da watan Rajab

SALLAR DAREN ASHIRIN DA HUDU NA RAJAB

Salla raka’a 40, kowace raka’a Fatiha 1, Amanarrasulu 1, Kulhuwallahu 1. Allah zai rubuta wa wanda ya yi wannan Sallar ladar kyawawan ayyuka 1000, Ya kuma goge masa laifuka 1000, Ya daukaka darajarsa sau 1000.

SALLAR DARE NA ASHIRIN DA BIYAR

Salla raka’a 20, kowace raka’a Fatiha 1, Amanar-rasulu…1, Kulhuwallahu 1. Wanda ya yi wannan Sallar, Allah zai tsare shi daga kowace irin musifa. Kuma Allah zai azurta shi da kubuta daga sharrukan duniya da lahira...


Tambihi:

Muhammad Sulaiman

Tare da Malam Muhammad Sulaiman Kaduna

Darasin Hadisi na III
Insha Allah a wannan darasin Hadisi na uku, za a kammala wannan gabatarwa da kuma shimfida dangane da fannin ilimi na Hadisi da aka soma tun a darasi na daya. Kuma bayani zai gudana a wannan darasi kan wadannan ababe kamar haka: 1- Karancin Hadisan Ahlul Baiti a littafan Hadisai na Ahlus Sunna. 2- Taharifin Hadisan Ahlul Baiti a littafan Ahlus Sunna. 3- Jarabawowin da masu ruwaito Hadisan Ahlul Baiti suka fuskanta daga masu tafi da iko...Katun

Dama Amurka ta ce Nijeriya za ta wargaje a 2015
Katun
Sun shigo da kayan aiki don tabbatar da hakan


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUS SHUHADA na bana

  • IMG_4289
  • IMG_4288
  • IMG_4287
  • IMG_4286
  • IMG_4285
  • IMG_4280
  • IMG_4284
  • IMG_4283 01
  • IMG_4283
  • IMG_4281
  • IMG_4277 01
  • IMG_4298
  • IMG_4297
  • IMG_4296
  • IMG_4295
  • IMG_4294
  • IMG_4293
  • IMG_4292
  • IMG_4291
  • IMG_4290


Almizan na cewa a dakace mu...