Fasto Buru ya bayyana irin yadda yake ganin girman matsayin Sayyid Zakzaky da almajiransa...Ci gaba
A ranar Talatar nan da ta gabata ne aka sake amfani da wani gungun zauna-gari-banza don auka wa 'yan uwa Musulmi, almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky na garin Gumel a jihar Jigawa a yayin da suke tsakar gudanar da karatu a cikin wani masallaci da ke Unguwar Juji a garin, inda suka ji wa sama da ma 25 raunuka...Ci gaba
Bayan mummunan harin da aka kai a kan 'yan uwa a Markaz da ke garin Potiskum, a ranar 7 ga watan Rajab, wanda ya yi sanadiyyar shahadar 'yan uwa har uku, Mu'assasatu Shuhada ta ware kowace Asabar din farkon watan Rajab ta zama ranar tunawa da Shahidan yankin (Shahid Abbas Musawi) da kuma tattara hakkin Shuhada a kowace shekara...
Malaman musulmi, na daga Shia da Sunna, da sauran musulmin duniya na ci gaba da tofin Allah tsine da danyen aikin da Wahabiyyawa-Salafiyawa masu kafirta musulmi suka yi na tone kabarin daya daga cikin manyan sahabban Manzon Allah (s.a.w.a), wato Hijr bn Adi al-Kindi da ke yankin Adra na kasar Siriya da kuma tafiya da gawarsa mai tsarki zuwa wani wajen da ba a tantance ba...
Da Subahin ranar Litinin din nan da ta gabata ne, sojoji suka mamaye wasu unguwanni a garin Sujela da ke jihar Neja da nufin bincike a gidajen da ke unguwar, inda suka kame kuma suka yi awon gaba da wasu 'yan uwa uku...
Ayatullah Khamenei ya yi Allah wadai da tone kabarin Hijr
Jagoran juyin-juya-halin Musulunci, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, yayin da yake magana kan lamari mai bakanta rai da ya faru a kasar Siriya na keta hurumin kabarin babban Sahabin nan Hijr bn Adi, cewa ya yi: Wajibi ne al'ummar musulmi, musamman manyan cikin su da suka hada da Malamai da sauran 'yan siyasa su sauke nauyin da ke wuyansu na fada da wannan bakar aniya ta masu kafirta musulmi, sannan kuma su yi abin da za su iya wajen hana yaduwar wutar wannan fitinar...

Mun samar da wannan ne don ku masu karatunmu ku sami saukin duba AlMizan a duk inda kuke, a ko yaushe ta hanyar "Android". Maza ka garzaya "Play Store" a wayar taka ka nemi AlMizan ka sa a wayar taka.
Tun farkon kamawar wannan shekara ta 2013, Hukumar leken asirin kasa da aka fi sani da SSS ta shiga kame 'yan uwa musulmi mabiya Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky. Da farko dai da ma'aikatan jaridar ALMIZAN SSS din suka fara. A watan jiya kuma sai suka kama Malam Ibrahim Husain da Malam Haruna Abbas, wanda yake Kwamanda ne na Harisawa. Ya zuwa lokacin fitowar wannan sharhin, shi Ibrahim Husain kwanansa kusan arba'in, yana tsare, shi kuma Malam Haruna Abbas kwanansa 21, yana tsare, ba amo ba labari. Haka kuma wani dan uwa Sharif Tukur Muhammad daga Funtuwa...
Insha Allah yau 28 ne ga watan Jimada Assaniya, wanda yake nufin gobe Alhamis 29, jibi Juma'a 30. Kuma daga imarorin da akan samu na cikan wata, ya nuna jibi akwai husufin rana, wanda ba za a gani a nan ba, amma za a gani a Gabas. Saboda haka ya yi kama da ranar Asabar zai zama daya ga watan Rajab.
To, Rajab da Sha'aban da Ramadan watanni ne masu daraja da alfarma. Watanni ne na ibada. Kamar yadda ya zo cewa, Manzon Allah (SAWA) kafin kamawar Rajab ya yi magana (Yana da tsawo ba zan karanto ba), Rajab watan Allah ne. Sha'aban, in ji Manzon Allah shi kuma watansa ne. Ramadan kuma watan al'ummarsa.
A ci gaba da aiwatar da dikar ta-baci da Shugaban Kasa ya ayyana kwanaki da suka wuce a jihar Barno da Yobe da Adamawa, yanzu rundunar hadin gwiwa ta JTF ta kafa dokar hana fita kwata-kwata a wasu unguwanni da sassa da dama a cikin garin Maiduguri da kewaye.
Sassan da abin ya shafa sun hada da Gamboru, Mairi Kuwait, Bakin Kogi, Kasuwan Shanu, Ruwan Zafi, 202-kwata, Dikwa Lowcost Sinner, tsarin gidaje ta 504 da na 303, sai Chad Basin, da hanyar Baga
Sashen 'yan uwa dalibai na Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake kira "Academic Forum" sun fitar da jadawalin shirye-shiryen makon tunawa da marigayi Imam Khomaini (QS)na bana da ake shiryawa duk shekara.
Daga Gidan Annabta
Tare da Abubakar Abdullahi Almizan
+234 803 701 4341
Watannin Rajab, Sha'aban da kuma Ramadan, watanni ne masu gayar falaloli da kuma Asrar. Domin a dukkan watanni 12 na Musulunci, babu watannin da suke da ayyuka na ibadodi kamar su. Shi ya sa bayin Allah (T) suke farin ciki da shaukin zuwansu. Haka nan kuma suke bakin ciki, da ma kuka idan sun zo karshe. Wato saboda yankewar da za su samu na falaloli da darajoji da zaukiyyat da halawat da kuma ma'anawiyyat na ibadodin da ake samu a cikin watannin, wanda babu irin haka a sauran watannin.